Sashe 74
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nan ba wani get together kuma da zamu . Koma za a barmu ban iya fita ko ina balle ban ma gigin fadin cewa zamu wani wajen don ko su maryam nasan ba za,a barsu suje ba . Mun dawo har mun kai kusan awa biyu su Aimana da Samira basu dawo ba don har Ammah ta fara fadan hakan don gaskiya sun dade kan basu dawo ba ina daki naji hayaniyar shigowansu. Lokacin har Abbu ya dawo ya koma fita sai gasu sun shigo fada Ammah ta hausu dashi tun shigowan nasu hakan yasa suka rage tamkiyan da suka shigo dashi din. Ina Aeesha Samira ta fada bayan ta bar Ammah din falo tsaye tana fada ta nufo dakin mu tace ke yau badon matar nan da kika sani ba da an barmu a wajen ai. Itace ta ganmu tace wani ya kawomu gida ta kuma bada gift ma kowa mu harda matar yaya habib da kuke tare na gane su khairat take zance a lokacin. Wasu manyan jakkunane ta zube a gabana tana fadin mun ba farida nasu ita da maryam wanan kuma mu guda guda tace mu baki sauran tasaka hannu ta dauki nata ta mikawa Aimana daya naji tace aje min nan sai naga ta kalleta. Tace muma muna da yawa gidan mu ai nace yaya akayine ta juya har takai kofa sai kuma ta tsaya tana fadin ke mummy akai fada a bayan ku. Fada kuma na fada ina kwabe hijjab din dana kare sallah tace bari mummy yau wani ya burgeni gaban kowa ya mari kawar saratun nan mai rawan kai yar gidan makwabatasu din nan da suke tare ko yaushe itama saratun da ta samu rabonta ai. Bari dai nazo ta fada ta fita da sauri naji Aimana dake rage kayan jikinta taja tsuki na kallota ina fadin anyi wani abune halan ? Tace ba komai Samira din nan tana son ta kawo min rainin wayau bata san halina ba tukun wallahi nace a,a don Allah kuyi hakkuri kinsan halinsu haka suke abu su kiyi hakkuri please. In bashi ba zan ci kayan nan ne kosai ta nunawa mutane ni barece a cikin ku kawai don nace ta ban in duba ko duk iri dayana abinda aka saka ciki kawai ta hauni da fada gaban kowa wai ba zata iya ba ita yadda aka bata zata kawo maki kamar zanci fa. Nace yanzu baga kayan tare da keba wai me aka saka a cikine ina kokarin budewa in gani abinda ke cikin jakkunan wanda samira tace sune nawa din. Na fara ciro dan karamin flask din silver wanda zaka iya turawa a jaka zuwa wani waje hakan yasa na gyara zama ina fadin ashe ba karamin kudi aka kashe ba dai ? Jin hakan yasa ta juyo tana kallo abinda na fitar din tace mu kuma wanda aka bamu ba wanan bane irin jug din nan plastic one ke ciki da kofunan sa. Mika mata nayi nace to karbi wanan ki kara dashi ko ba musu ta karba din ta kada a nata jakkan don nasan dai shi takewa. Allah yasa nawa din biyune sai ban damu ba koma dai meye aimu tazowa kara don haka ba zan yarda ta koma da bacin rai ba. Tun daga lokacin kuma ta sake tana fada min ai saurayinta ya kirata yau ban kusa da mun gaisa dashi amma yace ta gaidani. Nace oo dama ina kusa yau mu gaisa mutanen turai tayi dariya tace wallahi baki ma sani ba sai kinji hausarsa wallahi zaki san ya zaunu a can. Shine mama take wani kwalo kwalo wai ita dai a tsaya ayi bincike da kyau yanzun wa ke tsayawa wanan Aeesha dama yazo ya wuce mutum. A,a Aimana mama tana da gaskiya wallahi mutumin nan fa kema kin fada da bakinki baku taba haduwa ba ai dole tace ku tsaya ayi bincike da kyau. Ohh kema kin goyi bayan mama ke nan wallahi da badon ke bace da sai ince bakin ciki kema kike min yadda baba yace wa mama ranan. Aimana kada kiga laifin mama fa shi sha,anin aure dan bincikene komai yana son kwanciyan hakali kai Aeesha ke nan ke tunanen ki irin na mutanen dane wallahi. Bature yace opportunity comes once inya tafi shike nan ina zanga samu inga rashi Aeesha ita mama bata san komai ba daga Allah ya rufa min asiri zan cira in rabu da wahalan kasan nan. Idan naje suwa zasuji dadin hakan basu ba ke dai barni naje kawai ko ina akwai Allah shi zai tsareni tana fadin wai wuri yayi nisa nisan me don Allah. Galala nayi ina kallonta daga inda nake zaune din don ta hanni fada mata gaskiya a lokacin sai kuma naga ta dan kwashe da dariya tana fadin. Wai bakiji shiko mutumin ki ba da nace mai muna wajen buki sai cewa yayi yaji kamar ace bukin mune ai akeyi yanzu . Murmushin na tayata yi tunda ta fara ambato min bakin ciki cikin lamarinta nace aiya kwantar kwana nawane tunda baba ya bashi mukan musha buki. Tayi dariya tana fadin aini duk wanan shirmen da naga anty fati ta bari ana mata ban dauka wayayyu zan gaiyato tunda kinga kila da mutanensa zaizo daga france din ina zan yarda su raina muna. Nace wuuuu, ashe bari muja baya bukin manyane tace keba irin ku nake zance bani aiku yan gidane kune gaba gaba dolema ke Aeesha yanzu inda duk za a liffasa babban yarinya ai kina ciki. Amma dai gaskiya banji dadin rabuwanki da Man bash ba ga kuma yan uwansa na sonki don wallahi bakiga yadda sukayi ba da muka fada masu kin wuce gida dazun ba . Nima hjy tace min kannen Amadu biyu mata suna aure a kaduna zan gansu lokacin buki wai zasuzo nace dolema suzo ai suna kannen ango. Tace dolesu ma muna waya da babban karamar daice bamu taba gaisawa ba amma dayan mun gaisa wajen sau biyu da ita Allah sarki abin dacene ai. Kila rabuwana da man bash shine alheri kuma ni ban damu ba tunda ba soyayya mukeyi dashi ba dama mutuncine kawai tsakanina dashi daya koma muna kamar yan uwantaka. Amma ko kowa ya yarda da hakan ni kinsan ban yarda shifa ya fara bude maki ido haka lokaci guda Aeesha ni wallahi har yau ban yarda waiba soyayya kukayi dashi ba. Nace to shike nan tunda baki yarda ba amma ai duk zamaki gidan nan lokacin yana nan baki taba ganin ya sallama gidan nan ba wurina. And so what tunda dan manyane aiba sai yazo hira ba ko ni baga Amadu ba a waya muke kwashe soyayyan mu dashi zakice mun dade da sanin juna. Gashi da bakin kishi ni Allah ya taimakeni ma ba kasan nan zamu zauna ba aida munyi ta kwasa tunda yace baison ina yawan fita. Ko bukin nan da yaya ya barni nazo da yace wai ba zanzo ba sai dai ya turo min da kudi na bada gudun mawata saida baba yayi mai magana ya barni. Ikon Allah nake kallo daga inda nake kwance saman tieds kafin wayata ya dauki ringing na duba farida ce ina dagawa naji tana fadin yaya banji kida na tashi ba kuma ? Ki dan me na tambaya tace wurin get to gether din mana nace rufa min asiri don Allah kada inga bacin ran Abbu yau badai mun samu ya barmu munje wanan ba ai mun gode mun ba ido abincinsa munsha kallo. Ni aida kunji an balbalani da safe ina wajen dori nida yaya munir yaji ina fadin zamu yayi cikina da fada nace maganin ki ke nan yar son buki . Ni dama ko an barni ba inda zani wallahi maza haka da shegen kallon tsiya duk wace ta gitta sai an saka mata ido an kalleta ni ina zan iya wanan ? Wani kira ya shigo min nace ta kashe zan dauki kira mukayi sallama na dauka da sallamata don wani lokaci course mate sukan kirani don kowa ya matsu da zaman gidan a yanzu. Wani murya naji kamar nasan me muryan a wani waje muka gaisa dashi sai nayi shiru don ban gane me magana ba a lokacin. My queen ya kuka koma gida dazun lafiya wake magana sai naji yayi murmushi kafin yace kada muyi haka dake please kina nufin bakiyi serving number ta ba ? Nace sorry ban fa gane ko waye a layin ba kayi hakkuri may be wrong numberce ka kira yace Y S matazun ne da kuka hadu a wajen buki kika ba number. Sorry don Allah na manta da hakan wallahi saina kara fadin ina wuni ya amsa min yana fadin mu kara gaisuwan sani ke nan anyway dazun saida muka rabune naga ban san sunan hjyr tawa ba don zumudi ya hanani tambayan hakan ? Murmushi nayi ina fadin so soon haka gaba dai inda rabon sani zaka sani haba haba please kada muyi haka dake koda take no need a yanzu gaba zan sani ai tunda naga sunan ma rowanshi ake min kuma ? Ba rows kawai dai time din Sabin sunan baiyi bane ai zan fadama INA wanan yaron naka mai bakin naci shiya hadani da Allah dazun aina tsaya. Ooh wai umar yana waje suna hutawa ya kun fito wajen taron ne nace haba dai taro ai sai ku manya wanan wajen bana irin mu bane. Gaskiya ko mu manyan ai yanzu haka ina masaukina ban fito ba nagaji da yawa da mota mukazo garin nan saboda zirga zirga kada nazo na takurawa angon kuma da neman a nan . Angon abokinane right from our secondary schools muna tare dashi by them kuma muka rabu don na fita karatu saidana dawo muka sake haduwa dashi kuma. Hira sosai mukayi kafin mu kashe wayan dana gundura dashi don naga kamar shi bai gajiya da surutu Aimana na dan kalla tana charting a wayanta. Tana jin naja tsuki ta Dan dago tana kallona kafin tace wa kuma aka samu nace kai wanine yake son takura main wallahi banga alaman zamu shirya ba don ni ban son gadara. Kai Aeesha ko baki sonsa kici kudin banza kawai bashi ya kawo Kansa ba an kirashi ne jin hakan