← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 101

Sashe 12

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin takaici ta sauke ta kara kame rigan a jikinta kamar hakan zaisa ta jin saukin abinda ke kunar zjciyar ta tunane ta fada na dan lokaci akan hakan. Lokacin nashigo da sallamata idonane ya sauka akan rigan dake rike a hannunta rugume kamar mai tunane a lokacin. Cikin karfin hali idona akanta nake fadin Ammah na dawo tace ingaidake ta gode kaita dago ta sauke min kallo da idanunta da suka kada sukai ja a lokaci guda ba yadda na barta ba da zan fita. Na juya zan shiga daki naji muryanta tana fadin Aeesha yaki zo nan hakan yasa na juyo na dawo inda take rigan dake hannunta ta jefo min kafin na karaso gareta tana fadin. Kinsan daraja da muhinmancin wanan rigan a wajen mu kuwa da kika watsar dashi a nan wajen kanki daya kuwa idan baki sani ba yau ki sani wanan riga da kike gani darajarta tana da yawa a garemu. Saidana dan kara kallon rigan da take kokarin miko min na mika hannu na karba a hannunta makin na nufi dakina dashi saina nufi dakinta dashi a lokacin. Bina Ammah din tayi da kallo cikin mamaki tana fadin ina zaki dashi cikin sanyin jiki na juyo ina fadin dakin ki zan mayat don ni ban komai da kayanta. Galala tayi tana kallona a cikin mamaki kafin tace itawa ke nan banyi magana ba kawai nasa kai na fada dakin na aje rigan na fito. Har lokacin sai faman kallon mamaki take min don yadda na daure fuskana akan zance ba kuma iya fuska ba gaba daya raina a bace yake don zancen rigan nan data dauko min din a lokacin. Hijjab na dora saman kofa ban shiga daki ba na nufi wirin girkin mu mamaki ya hanata wani kyakyawan motsi a lokacin don na barta da fargaba da tsoro dayasa take zargin duk yadda akayi na dan san wani abu a yanzu kan yar uwarta ke nan. Wata zuciya ta keabeta da fadin ina zataji halin dan yaune kawai da bakin wayau irin nasu nufi nakeyi da bansa kayan da wani yai amfani dashi kila don tasan halina da tsandan tsiya. Aikina nakeyi cikin lumana yayin da har na kai ga hasa wuta ita kuma tana zaune kamar an shukata cikin tunane sai muryanane ya dawo da ita da nake fadin. Ammah akwai sauran gari ko nake tambayarta don tun lokacin nan da sukai tafiya ya kasance gari bai katse muna a gidan har sai mun tsaya jiran Abbu ya dawo daga kasuwa don muna dan ragewa a yanzu din sai hakan yake muna amfani wani lokacin kafin ya kawo din munyi amfani da dan wanda ke nan kuma ya ishemu a gida. Saida ta dan dauki lokaci kamar ba zatayi magana ba kafin naji ta sauke ajiyan zuciya da dan karfi tana fadin wanan shimkafan da maman Aimana ta aiko dashi nake son a dan sulala da wake mu dan canza abincin yau tunda Allah ya kawomunashi. Dakin na nufa don nasan inda kayan suke wake na dauko don in gyara can daga gefe daya na koma na fara gyaran waken nima dai zuwa lokacin a cunkushe zuciyana yake. Don tun sanda nasan da zancen mahaifiyana nake faman dakon bakin cikin daya yafi na baya a zuciyana sanin koni waye a yanzu yafi tayar min da hankalina. Don zuciyana tana min wasi wasin akoda yaushe akan koni yar halakce kamar yadda nana din ta fadawa yan uwanta saidai ni zuciyana yafi karkata da cewa ni din ba yar sunna bace gaskiya. Duk da hankalina a lokacin ba zai iya hango min gaskiyar zancen da Abbu ya fada min sai nafi hasashen Abbu din ya saya min zancen nasane don in yarda dasu din. Wai baki sauri Aeesha ki daga kanki ki dubi gabas tab yake da dari daya hadu yana shirin game gari kin zauna kina tunane haka . Hakan yasa na mayar da hankalina ga abinda nakeyi a lokacin bani kadai ba har ita Ammah ina kule da jikinta a mace yake har lokacin nasan kuma sanadin rigar nan dana fito dashi daga wajena nayasar a wajene yasata shiga wanan tunanen haka. A raina nace lalai Ammah da nana din nan da Abbu yace itace mahaifiyata akwai wani abu mai karfi a tsakaninsu don yadda Ammah din take shiga cikin damuwa haka. Zuciyanace ta bata amsa da fadin gaki kuwa baidai wuce matsalanki Aeesha don rikon dan da baka san asalinsa ba yanada wahala. A take naji idanuwana sun ciko da ruwa a lokaci guda tausayin kanmune ya mamaye zuciyana a wajen don nasan nikan a yanzu mara gatace duk da kokarin gatan da Abbu da Ammah ke nuna min sai wanan lokacin nake jin hakan bai wadatar dani ba a gaskiya. Ba malam bahaushe ba ko wani kabila nason ace yau ga asalinsa nikan a yanzu nagama sanin banda wani asali ko gata a duniyan nan kuma. Tunda ba wanda yau zan nuna ace dan uwan mahaifinane mace kona miji ina wanan tunanen ni dakaina naba kaina amsa da fadin No wander yan uwan Abbu suke min abu issa issa idan nashiga cikin su. Daga yara kuma har manya haka zasuyi ta hattarana kamar ba yan uwana ba har yakai idan munje wani taro nasu na daina nisa da Ammah duk inda take anan zaka sameni . Sai ya kasance yanzuma dana girma bani sha,awan bin Ammah zuwa sha,aninsu saidai taje ita kadai ta dawo na dauki shekaru a yanzu ban zuwa sha,anin su. Kauye kuma da take zuwa tun ina saka rai har na fahinci bata son zuwa danine kauye sai nafi daukan zancenta a lokacin da tace dani don mayu sunyi yawa a garin nasu yasa bata son zuwa dani wanan yasa na debe rai a lokacin. Amma yanzu da naji tarihina a wajen Abbu na gane kuma na fahinci abinda yasa Ammah din take min hakan don haka ya zamo wajibi in debe raina a dukka bangarensu biyun ga baki daya. Ba kuma don komai saboda in tsirar da mutuncina gare don daga yara har manya duk sun san asalina nake gani akan me zan matsawa kaina yanzu shigarsu bayan nasan asalina a yanzu cikin al,umma. Asalin Abbu dan cikin kanone dama nomane ya mayar da iyayyensu kauyen su Ammah har suka zama yan gari amma kowa nasu yana a cikin kano har kuma wasu daga cikin yan uwansa mata sunyi aure a kauye don can mahaifinsu ya maida rayuwansa a lokacin. Ko a bakinsu zasu iya jin tarihina a lokacin sai a yanzu da wayau yazo min kuma nasan asalin nawa wanan tunanen yake zo min a raina don haka a yanzu gaba daya saina share wanan gabaki daya a raina. Ina fada maki hakane mai karatu don jin da nayi da Abbu ya dawo yana fadawa Ammah zancen bukin wani dan uwasa da zai ma dansa aure. Gashi kuma idan ana bukin a can Ammah take kwanaki kusan biyu ko ukku saboda tazaran dake akwai a tsakanin mu don Abbu bai yarda ya sai gida ako kusa da unguwarsu ba a lokacin. Can yaje nesa sosai dasu yasai wanan gidan da muke ciki don rikona da ya dawo wajensu yayo kaura a kauye zuwa nan kano don rayuwana ya inganta ba tsamgwama . Saidai duk da hakan ba a tsira ba don anyo gudun garane aka fada zago saboda kallo daya zakiyi min dani da iyayyen nawa babu wani kamanceceni da nayi dasu don haka ba sai an tsaya bata bakin fadin su din ba iyayyena bane na asali. Don haka tunda wanan zance yazo kunnena na yankewa kaina shawaran ba zanbi Ammah zuwa bukin nan duk yadda ta taya min zuwa saboda yadda a yanzu na tsani shiga cikin mutane saboda haka nake daukan kaina kamar wata muji a gaban mutane idan na shiga waje. Daga inda nake jin Ammah na yanka fadan rashin fada masu bukin da wuri da ba,ayi ba don gashi jibinr ita ko wani shirin kirki bata dashi a yanzu don haka an mata girshi a bukin. Dariya yaso kamani nake fadi a raina su Ammah ho wanan wajen ko kinje da shirinki na gaske wa zaisan ma kinzo mutanen da suka goge suka waye idonsu na a bude. Karshema su ke zama yan aiki don angansu na kauye a wajen duk da gaskiya kira da tsarin su Ammah ba abin kushewa a cikinsa don mutanene tsayayyu ga diri da ake bukata a wajen mace Allah ya hore masu. Irin wanan kamar itama nana din nan tana da wanan halittan nasu a yadda naga zubinta a cikin hoton don ba inda ta rago Ammah din wajen kama saima ince kamar ta fisu cikar halitta ko don ita ta wayene fiye dasu yasa hakan oho bandai san komai a game da rayuwanta ba har lokacin. Aiko ban kai ga karshen tunane ba naji bayan Abbu ya fita Ammah din tana kwala min kira hakan yasa na amsa kamar a tsorace na fito lokaci guda daga dakin. Ashema har Abbu ya fita ban farga ita kadai na samu a zaune a tsakar gida take fadin abinci fa nace yanzu zanci Ammah. Na juya zuwa inda abincin yake na dan debo kadan gefenta na dawo in zauna ina shirin zaman naji tana fadin kinji min mutanen Aeesha ? Don rainin wayau da an mayar damu tallaka wai sai yau din nan ake sanar da malam zancen bukin dan gidan Alh sale don kawai sun raina mutane inbashi ba iyayye uwa daya uba daya ace sai yau din nan malam zaiji wanan zancen don Allah ? Mafarin in ba ajeba suce an ki zuwa ni yanzu na rasa data ina zan fara ma tunda nasan zuwa dole tunda banji yace dani komai ba. Shirun da taji nayine tana magana yasa ta dago ta dan dubeni tana fadin bakiji mena fada bane wai ina magana kinyi shiru haka ? Idonta data sauke ga abincin nawa yasa kuma ta canza akalan zancen bukin da fadin wai meke damunkine yanzu Aeesha ? Ina kule dake fa a yan kwanakin nan da kamar akwai abindake damun zuciyarki ace wai wanan dan abincin kamarki zataci kamar za abawa jariri dan watanni haka ? Dan murmushi nayi ina fadin amma
Chapter 12 · 0% Book details