← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 101

Sashe 52

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Tun dare na kwanta da wuri don kaina dake ciwo Asmauce ta kwana dani dakin wanda naji dadin hakan don ta taimaka min sosai a cikin dare.
Hakan ya hanani shiga school washe gari koda Auwal yazo ta fita ta fada mai banda lafiya yanzu na samu barci nakeyi don da dare kai ya matsa min da ciwo ban samu barci ba.
Yace inna falka tayi min sannu ta fada mashi na school ya nufa ya nemi class rep ya fada mai banda lafiya ban samun shigowa akan shi yayanane yaje masa.
Koda na falka rana tayi don har goma saura a lokacin na dan jima kafin na daga zuwa bandaki bayan nafitone na saka tufafi a jikina .
Tsakar gida na fito na samu Ammah zaune saman kujeran mata yar tsuguno Ammah ina kwana na fada daga bayan ta hakan yasa ta juyo gareni tana fadin .
Aeesha kin tashi yaya kan naki ya lafa ko da sauki Ammah na fada ina zama gefenta ta zubawa yaron dake tsaye taliya ta sake juyowa gareni tana fadin.
Yanzu Abbu kin ya fita ya tsaya dakon ki tashi baki falka ba dole ya fita nasan ba zai jima ba zaki ga ya dawo gidan nan ai haka yaron nan da kuke tafiya makaranta tare yazo shima Asmau ta fada mai yau kina jin jiki ya tafi.
Auwal yazo ashe na fada ai kema kinsan baida fashi kamar wanda akewa albashi kan hakan maza suna ban mamaki yanzu haka gidansu ba asan yana wanan ba.
Murmushi nayi don na fahinci Ammah bata san komai ba Abbu ya boye mata asalin zancen ke nan ko zakici taliyan in zubo maki ta fada cikin juyowa tana kallona ?
Kai na girgiza banjin cin komai yanzu Ammah inda akwai koko da sai insha magani dashi saidai a karbo maki waje wajen sadiya mai koko ko na darine tunda kina so.
Asmau tasawa kira tazo ta mika mata Dari daya tana fadin karbowa Aeesha kunu don Allah waje tasha magani ta karbi kudin ta fita.
Banson ciwon kan nan naki Aeesha don baisan ya tsaya ba cikin lokaci kankani dama yanzu naga kin rage yinsa sosai don kin jima bakiyisa ba .
Mummy wayanki fa nata kara a daki samira ke fadin hakan yasa na mike zuwa dakin don dauko wayan three miscalled na samu a wayan dan zamana wajen Ammah din.
Class rep din mune farko sai Auwal na ukkun kuma kharat ne kanwar Sir salman yadda na rubuta mun kwana biyu bamu gaisa ba da ita nasan akansa shine ta kirani lokacin.
Ban kara fitowa ba na kwanta bayan nasha magani sai wani barci kuma yinin ranan dai haka nayisa ba lakka a jikina kwana biyu ban fita zuwa school haka kuma wayana yana kashe.
Sai Auwal nema yazo ya shigo har cikin gida muka gaisa dashi yayi min ya jiki satin haka ya kare min ban samu shiga school ba.
Kafin Monday naji sauki sosai nafito munyi lectures lafiya misalin biyu da wani abune naga sakonshi yana nemana office dinsu.
Nayi mamaki kwarai da naga hakan don yadda naga kafan nasa a rana na zata sai ya kwana biyu a zaune yana jinya ai abin mamaki amma sai gashi har ya fito.
Banje amsa kiran nasa ba don muna da lectures Monday ce ko wani malami yana nan yana baje muna fahintarsa don haka na zauna sauraren lectures din.
Sai wajajen four sai gashi ya kirani a waya nazo office din su in same shi zai fita.
Banyi sanyi a gwiwa ba na mike don amsa kiransa din wanda a lokacin nima ina son ganinsa saboda wani topic da yai min tsauri gashi kuma kwana biyu bamu hadu ba baya ga hakan ina kewarsa nima.
Duk da yanzu ina son ja baya da lamarinsa don ance kwaruru ba tsaran wake bane tunda anyi min kashedi a kansa gara in ba kaina lafiya zaifi.
Sallama nayi daga kofa yana duke yana rubuta a wani farin takarda haka ya amsa min duken da yake bai dago ba nima data tsayen nace good day Sir.
Ya dago tare da amsawa a lokaci guda yana dan kallona kafin ya duka ya mayar da hankali ga rubutu ba tare da yayi magana ko ya kara dagowa ba.
Kujera ya nuna min in zauna nace nagode nakai zaune bai bar rubuta abinda yake yi ba kafin ya dago ya kalleni yana aje biron hannunsa saman takardan.
Saida ya dan hada hannayesa waje daya ya lankwasa suka bada dan kara ya soma fadin.
Two days kin boye ba a ganin ki kuma baki daukan waya kin hada fushin da kikeyi da kowa da sauri na dago kai na dan kalleshi yace yes hakane mana.
Zancen su hjy kika dauka ko ya fada yana kallona kafin yace gashi ni kuma time din bari na nan yayi ina ganin soon zan tafi insha Allah .
Da sauri na dago kai na dan kalleshi duk da bangane me yake nufi ba a lokacin saidai nafi zaton tafiya zaiyi kila mai dan tsayi yasa yace hakan dani.
Kai ya gyada tare da dan juya idanunsa alaman eeh zan tafi ko baki yarda da hakan bane?
Da sauri na taresa da fadin sir kwanan nan kaima kasan banda lafiya ne ai Auwal yazo gidan mu yagan ni zuwansa biyu yana duba ni.
Na sani don nina turoshi ya duba min ke ya kuma fada min halinda kike ciki da sauri na kara kallonshi muka hada ido na sauke kaina kasa.
A kaina kikai wanan ciwon nasani don me ba zan damu da ciwon ki ba tunda kinki zuwa asibiti a duba ki kada likita ya gane meke damun ki ?
Ba haka bane na fada aiko da baka nan zuwa nan kusan kullum mu gaisa da malam salman.
An fada min rashin zaman nawa yana da alaka da zancen da nake fada maki yanzu na kammala aikin daya kawoni Jami,an nan zan koma America very soon.
Wani irin kallo na mamaki na sake dago kai da sauri ina masa kafin kuma naji kunyan hakan nayi kasa da kaina ina fadin sir dama bawai nan kake ba dindin da zama ?
Kai ya kada min alaman eeh yace aiki nazo yi dasu dams kuma na kammala niba lectura bane .
A kan wanan sunan da kika taba gani a table dina nake nan kuma na kammala na gama tara duk wani abinda muke bukata a yanzu so ni zan barku may be sati mai zuwa ko kuma upper one.
Abinda yasa na kiraki a yanzu don muyi sallama dake may be ba zan kara shigowa school din nan ba kuma saida wani dalili mai karfi don yau yan team din mu zasu sauka zamu kama abin harin mu
Sai dai abinda ke damuna gashi har zamu rabu bansan komai akanki ba Aeesha don me yuyuwane idan mun rabu ba zamu sake haduwa ba wata kila kafin na dawo kinyi aure ko kuma kina da matsaya a lokacin.
Kaina dago da zumar bashi amsa amma na kasa sai naji yace dani why crying saboda zan tafi ko me kike hawaye haka kuma ?
Meyasa ka saba min da kai yanzu kuma kace zaka tafi ka barni sir idan ka barni a ina zan samu farin cikin rayuwan daka saba min dashi yanzu.
Dama ka barni a yadda nake Aeeshata ta farko da zaifi min sauki dama baka shigo rayuwata a dan wanan takin ba da hakan yafi min dadi a yanzu.
Cool down ki saurareni kiji don nace zan tafi bashi ke nufin ai na tafi har abada ba Aeesha farko ki amsa min tambayana ki daure ki dan ban labarinki ko kadan ne don Allah kafin nasan abinyi yanzu akai.
Kukana na tsananta sama da farko kafin ya dago inda yake zaune zuwa wajena ya miko min kyale na gane me yake nufi na karba ina goge fuska a hankali kafin na dago kai na dan kalleshi nace cikin muryan kuka .
Sir me kake son ji a gareni yanzu cikin dakewa yace komai ki fada min ke wacece ina iyayyenki me kikeyi anan garin ke ?
Banda iyayye sir na bashi amsa a takaice sai naga yayi murmushi yana gyara zama saman table din daya jingina da farko yace.
Baki da iyayye Aeesha a sama kika fado kome dole dai haihuwanki akayi kuma nasan ba wanan dattijon ya haifeki ba don baki da kama dashi tako wani hanya.
Su waye bylogical parents naki nake son sani a yanzu kuma suna ina a yanzu shine nake son sank daga wajen ki ya fada ba wasa a fuskanshi lokacin.
Abbu ya fada min mahaifiyata tana saudiya a yanzu haka mahaifina kuma run bayan ta haifeni ya gudu ya koma kasansa na haihuwa ya barta dani.
I know ya fada na dan kallesa yace Abbu bai fada making komai bayan wanan ba nan na bashi labari kamar yadda Abbu ya fada min ranan.
Yace photon da kika gani har yanzu yana nan koya bata nace yana wajena na boye a yanzu haka su Abbu basu San photon yana gurina ba a yanzu.
Kuma kin tabbatar da mahaifiyar ki tana Raye na gyada masa kai nace tana raye tana turo da kudi ana muna sayayya da komai ko wanan gidan da muke zaune Abbu yace itace ta saya muna shi don mu zauna.
Komai ban boye masa ba na fada mai game dani lokacin ya koma ya zauna saman kujeransa sai faman dan juyawa yake yana saurarena.
Da kuka na karasa ina kaico da rayuwata da irin gori da zagin da nake fuskanta a yanzu gun mutane.
Bayana naji ya dan bubuga a hankali yana fadin kuka bashine abinyi ba gareki yanzu nasan you deserve it amma lokacin kuka ya wuce agareki yanzu.
Cool down GF kina jina yanzu ba lokacin kuka bane akan wanan lokacine da zaki gina kanki ki zamo wani abu a rayuwanki da zaikai har an manta da past dinki.
Hakan kuma ba zai samu gareki ba ayanzu sai kinba kanki taimako ke da kanki zaki samu biyan bukatanki.
Kaina dake duke nake kokarin dagowa don in fahinci me kalamansa yake nufi da saini da kaina na taimaki kaina as how ta yaya me hakan ke nufi.
Yana tsaye a inda yake har dago baiko motsa ba kusa dani muna gab da gab da juna dashi a zatona zancen banza zaji daga bakinsa yasa na dan kura masa ido cikin mamaki.
Shima kallon ido da ido yake min bai kawar da nasa idon yace yes sai kin taimaki kanki kafin burin ki ya cika zaki kau da kowa da komai a yanzu a rayuwanki including me da zancen su Abbu kiyi facing din studies dinki kawai a rayuwanki.
Idan kinyi hakan non taimakawa rayuwanki dana duk wanda yake kaunarki da alheri ajiyan zuciya na sauke lokaci guda.
Saboda nasan tundaga level one har yanzu da nake zancen shiga uku shine ya biya min kaf don ko naje biya zasu ce dani ai anbiya har an bada resist akan biyan.
Muryan shi da yake fadin kin min alkawarin hakan a yanzu yasa na dawo ga dan dogon tunanen dana shiga cikin dan lokaci na kalloshi ya kura min idonsa a kaina.
Samun kaina nayi da daga masa kai alaman eeh a lokaci guda yace good idan kiyi hakan kin taimakawa kanki.
Ya juya zai koma wajen zamansa yana fadin kasan nan na bukatan mata a wanan fannin na karatunki musanman matan arewan nan namu.
Karatun ki shi zai kaiki ga matakin da ido ko keya ba zai iya fuskantanki da wani challenges din rayuwa ba zaki gane me nake nufi dake a nan gaba.
Motar da Auwal ke kai ki school dashi nasa a canza maki iyakar Auwal dake satin nan kece zaki dinga driving da kanki baki da matsala akan karatun ki matukar zaki daure kiyi kamar yadda na bukace ki dayi a yanzu.
Abbu dinki kafin na bar kasan nan za,a fadada masa shagonsa ki dauki wanan abin a matsayin tukwici ga zaman mu dake yadda kona tafi ba zaki shiga wani damuwa ba akaina.
Yanzu kan kuka sosai nayi a lokacin wanda ba zance ga dalilin yinsa ba kuka na halarcinsa gareni ko na rabuwa dashi ?
Dams haka yayan mask kudi Duke ashe koshi wanan rayuwansa take daban dana saura ashe dama nike haukana kamar yadda bai taba nuna min soyayyaba ko da wasa haka abin yake har cikin zuciyarsa ?
Chapter 52 · 0% Book details