← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 101

Sashe 30

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gurfane nake gaban Abbu dan nisa kadan da India yai shimfidansa daidai shigowa gidan don haka ba kowane zai iya jin mu ba a lokacin. Ban boyewa Abbu komai ba saidai na danyi gyaran zancen yadda zai fahinceni har zuwa photona dana samu anzana da case din da akayi da wayan da aka kawo min da yamma na mika mashi. Nisawa naji yayi kafin ya ce to Nanata ai aikon gama ya gama saidai kiyi hankali gaba kuma din mutane yanzu ba abin yarda bane shiya kike ganin taimako yayi karanci a yanzu Allah ya kyauta ya tsare gaba. Ki dai kara kula da rayuwanki Nana donke amanace a wajen my yanzu don haka ki kara kulawa kinji ba komai mutum zai jefa kansa a yanzu da sunan taimako don sai abin ya rufta dakai a karshe kazo kana da ansani kuma don haka kibi a hankali da kowa nana. Shikuma wanan alherin daya aiko muna Allah saka da alheri garesa don ba kowa zai tuna kamai halarci ba haka alamu sun nuna shi din mutumin arzikine tunda yasan kiyi masa har ya iya tunanen me zai saka maki dashi ya fito muna ta nan to mun gode Allah ya tsare gaba tashi kije ki . Bayan nabar wajen naji yasawa Ammah kira dams suna zaune da yayan anty har anty ana hayaniyar cin abincin dare. Wanda hayaniyar ya batawa Aimana da task taji tataunawan mu da Abbu din amma bataji komai ba son hayaniyar tasu donsu basu iya abu cikin hankali ba. Nan na zauna wajen su na debi abinci na fara ci kafin yaron anty yace min anty ban nuna making takalman dana sayo ba ya mike naji uwar na fadin takalman da yai ma kadan ya matse da yawa yaushe zaka more mai ? Ina ruwan su anty ba anty ba anta samira ta fada daga gefen uwar sai ta biyun mai bi mata tace kedai samira na rasa mi tayi maki baki son zancen ta mama hwa tace itama zaman uwa take garemu. Nan ta hayayoko kanwar da fadin a,a wallah Allah ya tsari gatari da saran kashi wa a uwata can dai gasu gada uwata kan gata nan kowa ya Santa. Ke ke manta tace haushi taka bata inta ganta waka kallonta in Aeesha na waje kwab naji uwar ta buge bakin karamar yarinya lokaci guda. Haba anty ki barta mana ya da duka haka kuma don suna shirmensu tsiya a bani so yanzu fisabillahi ya dace su hwadi wanga magana a gabaki Aeesha ? Kukan data saka yasa Abbu da Ammah tambayan meke faruwa uwar tace ba komai nan ta biyun saratu tace in an mu ta bugeta don' tace samira tace haushin anty Aeesha takaji ranan wai ta hwaye kyau da tsiwa. To ai sai ta yankata kafira mai mugun aniya samiran nan ba samiran arziki bace ina fadi ina kari Ammah ke fadan haka . Taci gaba da fadin banda yar banza mai baki kamar bakin zunubi Aeesha ba kanwar uwarki bace like fadan haka gareta ina nan da safe kudinta ta dauka taba kanin ki inba nakaba wa zaima haka ? Ta nuna ita nakune ta sadaukar da kanta ga Dan uwarku dan abindake gareta ta dauka ta mika masa ai naga ga uwar naku nan gida ta kasa bashi kwandala ya cika. Abincin nake ci yayin da nake jinsa kamar madaci a bakina haka nake kokarin turawa don kada in kwana da yunwa don sam ban yarda da inci abinda Aimana ke dafawa daki ba don a sani dai gidansu baifi gidan mu arziki ba da zata kawo min rainin wayau. Yo rainin wayau mana haka kawai zata zo gidan mu cin arziki ta nemi ta rainawa mutane hankali don wullakanci wanan yasa tunda ta fara hakan make bar mata dakin ga baki daya. Yau ace nice nake gudun abincin gidan mu duo kokarin iyayyena akaina tunda na taso har kawo yau Abbu bai taba kasawa damu ba wurin ciyar damu abinci koda ba dadi kuwa zamu daici ba za a kwana da yunwa ba. Saidana daidaici ta gama na mike zuwa daki don har lokacin duo muna tsakar gida ana shan iska kodana shiga akwance na sameta saidai batayi barci ba. Shirin kwanciya na soma kafin naji muryanta tana fadin dadin abindai mutum yasan asalinsa hakan yasa na dan juyo na kalleta kafin nace wanda baisan asalinsa ba sai a hanasa rayuwa ko ? Aida sauki tunda ba icce ya kawo mutum duniya ba iyayye suka kawoshi kuma ba a yanke kauna a zuciyan mumuni. Waike malama daga jin magana kin zake haka kina ta zuba nace wai tayaki nakeyi naga kinayi me kadaine dama mutum daya ai bai magana shi kadai data haka kowa yaja bakinsa yai shiru. Na kula da Aimana a yan kwanakin nan da take ikirarin cewa tayi saurayi dan kasan wake uwarsa tayiwa mamanta magana zata hadasu sure sai wani jiji da kai da daukan kanta so higher ya taso mata. Tana ganin tafi kowa tana jin ita wani tsiyace a yanzu don dan kudin da take ganin ta fara rikewa a hannunta abu kadan zatace hjy tace hjy tayi kaza. Dama nasanta da kyashi da hassada mai karatu inbaki manta ba tunda na fara Jami,a ta matsa saida tazo itama tafara haka kuma da muka taso unguwarsu suka matsa suma zasu taso da hakan bai samu ba lokacin shine ta dawo gidan mu da zama. Sai gashi kuma tana son zama min wani kaddara a cikin rayuwata a yanzu don hakane datayi min nake bata amsa a take kamar yadda tayi min din. Washegari kafin in gama shiri har ta fice gidan ita bata tsaya mun fita yadda muka saba fita ba a tare saidana gama na sallami Ammah don't Abbu na waje lokacin. A nan na sameshi nake fadin Abbu zan tafi Sam na manta da zancen man bashir a raina munyi sallama yana kokarin miko min kudi mota ta tsaya kofar gidan mu. Dani dashi muka bi motar da kallo don ganin wanene acikin motar har ya bude motar ya fito matashine dan karfafa dashi haka ya nufo inda muke yanawa Abbu sallama tare da gaidashi. Kafin ya kalloni yace nine aka turo in dinga kaiki makaranta da safe in dawo dake da gamma jiya nazo don jiya ya kamata in fara aikina saina samu bakya nan a lokacin. Kallon juna mukayi nida Abbu kafin nayi kasa da kaina sai naji Abbu yace amma bawan Allah waya turoka haka yana tambayan matashin ? Dan murmushi ya sake a fuskanshi cikin ladabi yana fadin baba ni aikinane amma ita tasan da zancen ai don kamar hakan kariyane da gata a gareta wajen ogan mu. Waye ogan naku Abbu ya tambaya cikin kafesa da ido sai naji yace man bashir jika a wajen mai martaba sarkin gabas maici yanzu. Kai Abbu ya fara dan kadawa yana fadin na,am na,am shike nan ya turoka ka dinga yiwa yata wanan hidimar koda yaushe? Kwarai baba ko ina take son zuwa nine zan diga kaita in har ta sanar min insha Allahu zanzo in kaita don shine aikina a yanzu. Don haka baba don Allah karkuce a,a ga hakan don idan kunyi hakan tankar kun hanani hanyar samunane saboda aikin nan ba karamin dadin samunsa nayi ba kasan iyayye suna bukatan hutu a yanzu tunda mun kawo karfi. Kallon Abbu nasakeyi don inji ya koresa da fada amma sai naji Abbu din yace cikin mutuwar jiki jeki Nana ya saukeki ban fatan sanadin mu ka rasa abin farautawa iyayyenka rai yarona saidai amana don Allah duk da bansanka ba amma lafazinka ya kwanta min a rai daka fada min gaskiya akanka . To nima ga amanan yata nan a yanzu na danka a hannunka ka dinga sa ido a motsinta da komai ka kula min da ita bisa ga amana son Allah. Insha Allahu baba zan rike nakuma kula kamar yadda ka bani amana in Allah ya yarda addu,an kudai muke nema ko yaushe garemu. Hakane Allah yai maku albarka dakai da sauran diyan musulmin Allah ga baki daya ya amsa da amin ya kalloni yana fadin muje ko ? Sake kallon Abbu nayi naji yace jeki Nana ta Allah yana tare dake aduk Indi kike Allah ya tsare muna ke ya kare yakai lafiya a dawo lafiya kuma. Amin Abbu na fada tare da mike nabi bayan mutumin kafin na iso ya bude min bayan mota nashiga na zauna ina mai runtse idanuna a hankali don bakon yanayin da yazo min a bazata. Tunda muka kama hanya dashi ba wanda yai magana a cikin mu har muka kawo ejection din da muke hawa mota da zai karasa damu school Aimana na hango cikin dandazon dalibai dake jiran abin hawa har lokacin bata karasa school ba ashe . Har ciki ya shiga dani ya aje nayi mai nagode ba yawa hjy aikinane a fito lafiya ya fada hakan baisa na juyo ba na shiga ciki. Ashe a gaban wanan Hindu ce da kawayenta mota ya ajeni nan suke tambaya wai wacece ni saidai ba wanda zai basu amsa har shiga aji akan idonsu nashiga suna tsaye suna gulma akaina lokacin. Masu zugata na zugata masu cewa tunda taga haka tafi harkata kawai zaifi amma tana tsaye bakin ciki ya hana tama magana taimakona dana kara batar masu dakoni wacece sai irin rigunan nan da nake sakawa da bai bari taga tufafina na asali da tunanen ta ya bata sanin ni din ba kowa bace a lokacin. Yayin da Aimana ta shigo school wata kawarta data ga fitana a motar take fada mata yau ba tare muka shigo bane ai taga mota ya ajeni sai hakan ya bata mamaki da har na rigata shigowa makaranta a lokacin. Sam na manta da zancen sabon wayan da akace in kunna za ayi magana dani a lokacin sai Dana zauna zancen wayan ya fado min a rai a hankali na mika hannu na dauko wayan daga cikin jakata dake gefena. Cikin hikima na kunna tayi karan da har ya jawo hankalin wasu a kaina amma na fuske don duk zamana dasu basu taba ganin wayata ba dama balle su dauka wani abune. Sakone har ukku ya shigo min na farko
Chapter 30 · 0% Book details