Sashe 95
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
idan zan fita don kusan hanyan mu dayane dake saidai akwai nisa sosai amma dai ba matsala idan kikaga hanya daga yau zaki gane waje ai. Nagode na fada ni dai naga matar tashiga daki ta kirashi ko me tace oho sai can ya fito da dan jakkarshi na zuwa wajen aiki yana fadin ok muje ko ? Amira na jikina tana wasa na dagata zuwa kofansu ina fadin anty Basira ni zan tafi sai mun dawo ke nan ta fito tana fadin ok Aisha sai kin dawo . Gashi bakima tsaya kin karya ba nace ba komai ai ina dariyan yake a fuskana don na fahinci akwai dan matsala da zuwana ya fara haifarwa a tsakanin su yazu yanzu. Amira ta saka kuka wai zata bini nace tayi hakkuri na bude yar jakata na mika mata 1k ta karba tana murna ta juya zuwa wajen uwarta