← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 101

Sashe 22

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

son ki hada Abbu ya juyo yana fada min a cikin wani murya a kausashe wanda saita baci yake irinsa. Da sauri nace yi hakkuri Abbu ya juya baice dani komai ba sai ransa da bai sake ba har lokacin Ammah na zaune ta saka muna ido ba tare data tsunka ba. Sai zuwa can take fadin kafiya irin na yarinyar nan ni yana ban mamaki kafin ta karasa hannu kawai Abbu ya daga mata taja bakinta tayi shiru a zancen. Mikewa nayi da sauri ina tattara kayan don ganin ya dauki buta ya fara alwala a lokacin ina furta nagode Abbuna. Jeki kawai Allah yai maki albarka na amsa da amin Abbu na shige dakina da kayan naji yana fadin na bata kudi ta sayo maki takalma da jakka da zakiyi amfani dasu. Saidai matsalan ba a san girman kafanki ba tace kafan na juyo tare da dakatawa ina fada nagode Abbu Allah ya kara girma da nisan kwana Allah ya barmi ku Abbu nagode. Sai lokacin na daga murmushi a gefen fuskanshi ya juya yaci gaba da alwala da sauri na fada daki ina budan kayan ganin kayan ina mamakin yadda Abbu ya iya fidda kudi yai min wanan sayayyan haka? Dude naji kayi shiru mana tun dazun salman ya fada daga inda yake zaune yana kallon abokin tafiyan nasa dan nisawa yayi kafin yace mai kake son ince dakai yanzu . Wanan yarinyar mana data tarowa kanta much ni tsoro ma ta ban wallahi don na dauka gamo mukayi wallahi. Kasan yau jumma,a ance suma mutanen boye suna fitowa sallah ranan jumma,a saina dauka mun faka mota a gidansune ai. Kaji dan iska ai bakai kadai ba nima kafanta na kalla yasa kaga ban girgiza ba ai suka kwashe da dariya kafin wanda ya soma magana yace. Yar gidan waye hakan wai da badon naji hausa a bakin yarinyar nan ba wallahi zan rantse ita din ba bahaushiya bace duk da shigan hausawane a jikin ta. Nan ma shiru yayi ba tanka masa ba saiki ke faman zuba shi kadai ya jawo wanan ya sake ya kamo wanan ya kare da fadin kila yar gidan wani masha huri ne dai don bata da tsoro sam a zuciyarta. Ka fa dameni don Allah ya fada hakan yasa ya kwashe da dariya yana fadin ai dole idona yau ya gano min mamaki Allah har yanzu ina tantama akan yarinyar. Ya juyo yana fadin saboda me yana dan kallon dan uwan nasa yace da gani fa diyar wani kusace wanan tsuki yaja ya juya tare da maida hankali akan motar da yake tuki kafin can ya juyo yace to ba yar gidan kowa bace dai wanan da ganin tsarjn shiganta tafi kama da irin ustanzan nan dai. Ga wani zullum bun hijjab ga kuma face mark a fuska ba wanan a yanzune kafin ta zamo yar hannu ba Allah ya kyauta za adaiyi abu dai kan. Ba students ba ba kuma lecturals din ba sai lokacin ya kara juyowa yana fadin kake gani Allah ya kyauta ni mugunta da zan mata data ambata min nake tunane a yanzu. Kai baka da dama wallahi aiba ita ta fadi ba abinda tajine ta fada ita kan ina ta sanka haka fa har malaman wasu ke fada a kanka din. Shiru yayi suka karasa shiga katon get din gidan nasu da maigadi ya bude masa tunda yaji karan motarsa tafe tare da daga hannu yana jinjina masa shima yayi masa horn alaman amsawa a gareshi. Malam idi ke nan sarkin gaisuwa sai lokacin ya juyo yana fadin don Allah ya isa haka salman kai baka san lokacin da ran mutum yake bace ba ka damesa da surutun banza haka. Wai har zancen yarinyar nan ya tsayawa a rai kake nufi Bashir banga abin damuwa ba tunda kai ka zabi hakan ance ga aiki kace sai koyarwan nan to dole ko ka fuskanci haka ga dalibai dama. Bude mota yayi ya fito ya shareshi ba tare daya tsaya kara saurarenshi ba ya shige ciki kai tsaye ko kannensa dake falo bai tsaya duba ba da suke gaidashi. Sai salmanu din ne ya shigo da baya da tarkacensa a daidai lokacin ne kuma hjy ke saukowa daga sama tana binsa da kallo don rashin ganin danta a tare dashi. Gaza hakkuri tayi tana fadin ina Bashir din kuma ya nuna mata hanyar dakinsa taja numfashi tana zama tare da fadin kunyi halin naku ke nan ma yau ? A,a wallahi mami daga can dai yazo da bacin ransa tace kaiya ni dama na sani haka za akai ai amma yallabai ya tsaya biyewa yaron nan shirmen sa. Barin samesa salman din ya fada ta tabe baki bata iya amsa mashi ba a lokacin don ranta daya dan sosu da maganan ta dago tana cewa yan matan ke dauko min drinks dina don Allah. Ko daya bude dakin ya shiga bai same ba yana bayi yana watsa ruwa don shirin jumma,a daya gabato shima bai tsaya ba ya zube masa takardun nasa a wajen ya fita zuwa nasa shirin. Sun fito a cikin shiga irin ta hausawan asali da hakan ya kara fito masa da suransa dakyau ga wani shadda sun saka a jiki faril sol sai maiko yake da yauki a jikinsu. Har lokacin uwar tana zaune a falo fuska daure shima ganin hakan yasa ya dan gaida ita sama sama yasa kai ya fita bayan yayi mata sai sundawo. Basu dawo gidan ba a yadda suka saba sai sun tafi sun kaiwa kakaninsu dake raye gaisuwan jumma,a muddin suna gari akace jumma,a tayi sun saba da hakan. Sai dare suka dawo nan falo suka samesu lokacin Abbansu ya dawo daga tafiya shima suka zauna suna gaisawa dashi cikin fara,a yakewa dan nasa ba,a da fadin malami yau yaya kuma ? Mamin ku tace ka dawo hasale kana masu cicika ba gaira ba dalili jin hakan yasa ya kawar da kansa gefe daya kafin kuma ya juyo yana kallon salma din . Da sauri ya girgiza kai yana fadin mami na fada maki wani abu don Allah da muka shigo ta kallosa cikin takaici tana fadin koka fada fa aishi yajawa kansa koma meye. My friend bani labari yaya akayi kallon Bashir din yayi yana matse dariyansa kafin Bashir din ya dauki filo yana jefa masa ganin hakan yasa ya cabe filon yana fadin ka jefeni to saina fada kuwa. Yauwa fada muna mu tayashi fushin muma muji kowa ya taba min besty na baisan ba,a tabawa yallabai kakansa ba a zauna lafiya ? Abba gamo fa yayi da aljana yau muna batun dawowa gida shirin jumma,a muka ganta tsaye a wajen motarta jin hakan yasa kowa dagowa yana fadin Aljana kuma ? Yace a itace ta bashi tsoro Abba wallahi koni na firgice da farko nan mami din tace wai tsaya wasa ko gaskiya don Allah ? Yace mami saura kiris in kawo maki shi gida shame shame aiyau saidai nima a tsorace din nake a lokacin nan ya kwashe komai ya fada masu daya faru dasu. Sukace me zasuyi in ba dariya ba suma har uwar da da fuskanta ke a daure a lokacin take fadin kagani ko kaga abinda nake fadi ko. Ni wanan tsarin sam bai mun ba wallahi mami Allah da farko na tsorata lokacin data dago wasu manyan idanuwa nata tana kallona dasu. Sai dai dana tuna da labarin Alh da yace inda ake gane aljani a wurin kafa yasa nayi saurin kai idona akan kafanta na kalla naga shegiya kafarta sumul suke yasa ban razana ba. Yallabai kajima sunan da suka nada masa ashe a school din mahaifin yace toba lectural bane sunan komai ai zakiji a garesa yanzu balle yadda suke ganinsa haka duk bat da kamasa sai sun zargi wani abu a kansa ai.
Chapter 22 · 0% Book details