Sashe 31
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
daga mtn suna min tallan mono dinsu sai na biyu bangane number maishi ba an rubuta call me back when you are online. Na kara maimaita sakon kafin naje na yaya sulaiman da tafiya ya kamashi zuwa Kaduna tsawon kwana hudu ke nan baya gari. Ya rubuto yana tambayana lafiyan mu tare da nuna yadda yayi kewan rashin mu a lokacin wanda hakan yasa na dan saki gutun murmushi . Ba laifi gaskiya kinsan yadda saurayin farko ake ji dashi hakane ya kasance tsakanina da ya Suleiman din don tun muna daukan abin matsayin wa da kanwa har yanzu mukai muna nunawa juna matukar kauna a tsakanin saidai a waya hakan yafi kasancewa a fili har yanzu muna da nauyin juna don muna da sauran yarinta gaba dayan mu a lokacin soyayyan dai akeyi hakana. Shigowan malam Lawal yasa ni natsuwa kamar yadda ya saba muna lecture yauma hakan ne rabi da rabi hira a haka kuma yana gamawa zai iya cewa test zaiwa mutane. Don haka wanda ya gane halinsa zai maida hankali kada ya shamace mu yau ma dai hiran wata batutiya a inda yai karatu yai muna a harkan computer inda a cikin hiran nasa ya bada labarin yadda ta hada wani waya by mistake saidai bai kai karshe ba yace ya bamu assignment akan labarin nan kan kowa ya daure da zancen. Yana fita wayan nan sabuwa da shaf na manta dashi yana daukan kara sai can na tuna ai tawace na dauka da sauri Man bashir nagani rubuce. Dakyat nagane received na dauka ina kaiwa a kunnena saidai anyi shiru ba magana nima kuma banyi magana ba kamar yadda maishi bai min ba. Still wayan na a hannuna hakana kuma ba a kashe ba daga wancan bangaren ga hayaniyar ajin yana ji nima kuma ban kashe ba a bangare na. Ta gefena take tambayana ya question din yake na juya ina sanar mata sam na manta da zancen wani waya can saida muka gama rubuta question din na farga wayan na running har lokacin da sauri na kashe baifi second ba wani kiran ya kara shigo min still dai daga maishi. Wanan karon ina dauka na kara a kunnena ina sallama naji anyi kamar ajiyan zuciya tare da fadin kina da lokacin amsa wayan yanzu ke nan ? Nima tambaya nayi da fadin waye mai kira a yanzu ina aji wurin karatune fa don Allah kayi hakkuri don' ni matar aurece a daina kirana na kashe da sauri. Bashi ba har salman dake zaune yanaji saida ya sake dariya ba shirinsa shiko ido ya fitar waje yana fadin kai wanan ni zata rainawa hankali. Hi meet me in my office now d marriage woman dan abinda ya rubuta ke nan ina kokarin mayar da wayan sakon ya shigo na dukar dakai ina tunane sai can na mike na hada takarduna waje daya na tura a jakkata na saba na fita don amsa kiran nasa. A hankali nake tafe zakice ni din ko zo in kasheki cikin Hausa ban sani don yadda na fito balarabiyata sak don bakaken kayan dake jikina sun amshi kalana sun min kyau baki ganin komai sai dan round face dina dana bari sai kuma face masks dake hanjina nayi takunkumi dashi. Tsayawa nayi kwankwasawa kamar yadda ka,idan shiga waje yake muryan salman ne ke fadin in shigo nasa kai na shiga da sallamata idan zaki shiga shine mutum na farko da zaki gani yana facing din kofan. Ranan saye yake da shirt na maza longsilf mai dogon hannu da aninaiya har kasa saidai yayi stocking ya dan bude aninaiyar rigan daga sama. Kanshi a duke yana faman rubuce rubuce a farar takardan dake gaban shi muryana tar na fara gaida salman din kafin na mika masa nasa gaisuwan daga baya. Amma ko gezau kamar baisan da shigowana ba salman din yace min in zauna hakan yasa na dan daga kai na saci kallonsa caraf idon mu ya sarke Dana juna. Ya zakacewa matar mutane ta zauna bayan kaji tace ita matar aurece yanzu ko so kake mijinta yazo yai muna ihun kwarata a office kuma . Kasa nayi da kaina lokaci guda sai naji salman din yace ai bata sanda wanda take magana bane No ka barta tsaye shine punishment din ta nakin bin umurnin dana bata. Nifa na dauka irin masu hada number din nan ne suna kiran mutum dashi yasa na fadi hakan ko dagowa baiyi ba ya kallemu duk da salman yace yayi hakkuri mantawa nayi ya daga mai hannu tare da mai kallon warning a gareshi. Shiru yayi cikin bin umurninsa ya duka yana dariya kafin ya karkare shan shayin dake aje saman table din yana gamawa ya mike tsaye yana kallonsa yace zan tafi amma zan biya can wajen Samsun na karbo sakon. Nan ma kai kawai ya gyada masa kafin ya dan ja kujera yana fitowa yace OK miss Aeesha see you next sai kin fito idan kin gama punishment din . Daga haka ya fita yana dariya sunansa naji ya kira ya juyo ya nuna mai basket din dake gefensa yace dashi two cup ? Wani kallo yai masa again ya duka yana dariya ya fara zuba masa ruwan black tea din ya aje gabansa kana ya dauko wani ya tsiyaya kafin ya kalloni yana fadin. Akwai madara a zuba makine ko kema haka zakisha no sir nagode ba zansha ba yau Thursday ina azumin nafila jin hakan yasa ya dago kai ya dan dubeni. Sai kuma ya dauke kai yaci gaba da rubutunsa salman din ya gama ya fita ya barmu mu biyu dagani sai shi a office din nakai minti biyar kafin ya dago yana fadin have your sit zaki iya zama. Next time idan kika kara barin saina kiraki kina fada min rubish waike matar aurece don baki da kunya kin iya karya see your eyes don Allah makaryaciya kawai. Dan turo baki nayi ina fadin ni ba makaryaciya bace na fadane saboda mayaudara masu batawa mutum lokacinsa da yaudara. Ido waje yake kallona kafin naji yace ways Suleiman a wajenki da sauri na dago kai na kallesa kafin in kasa da idona son irin kallon da yake min har ya dakatar da rubutun da yakeyi don son jin amsata da zan bashi. Yayanane na fada ina kasa da kaina daga kallonshi yace yayan ki as how desame father kuke dashi na girgiza kai alaman a,a kafin nace dan yayan babanane shi. Murmushi naga yayi kafin yace no wander kuke kalamin soyayya a tsakanin ku yanzu nasan ko ya kuke dashi makaryaciya kawai. Niba makaryaciya bace na fada kasa kasa azatona ba zai jini ba lokacin sai naji yace me azumi baya karya ko kin manta da azumi a bakinki ? To ai gaskiya na fada ko yanzu ni ba karya nakeyi ba gaskiyar ke nan na fada shi din yayanane kuma yana kula da duk wani lamarina dana yan uwana. Ina question din da aka baku a class saida na dan kalloshi nace gashi na jawo jakkata a kafadana ina fito da question din na dan daga na tura mai kafin najawo baya. Naga yabi pepper da kallo kafin ya ja zuwa gaban shi na dan lokaci yana nazari ya jawo wani pepper ya fara zanawa yana min bayani yadda zan fahince shi.