← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 101

Sashe 94

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zan juya na dauka ba nan suka saukeki ba ai a nan muka sauka na bata amsa. Ko ina akwai na Allah wani dan tashan ne ya taimaka min ya kwaso min kayana zuwa bayan motanta muka shiga na fito da dubu biyu na mika mai yana tayi min godiya. Taja mota muka tafi tana fadin shikan yau babu kamarsa ai yafi driver ma samun riba na daiyi mata murmushi ina fadin mun sameku lafiya ? Wallahi lafiya kalau Aisha yaya hanya ya kano kuma kai ina su mummy da kowa gida nace suna gaidaku anty ya kuka dawo kwanaki kuma ? Kai bari bari duk a cikin hausanta da harshenta keda surki da yarensu take fitar da harafinta amma ina ganewa tsab don hausane amma fitan harafi ne ya banbanta. Kano kan wai badai kuma yanzu ba gaskiya wanan bukin ma don na fatine naje wallahi ban iyawa da banje ba . Irin ginan nan ne mai hawa hawa ta tsaya gabanshi muka fito na dauki babban jakkar tawa da karamin ita kuma ta dauko min dayan dayafi karanta. Tana gaba ina baya da kyat na iya hawa saman na biyun da suke da kayan hannu ta sanya ta danna bell ba bata lokaci naji ana kokarin bude kofan ta ciki. Wata nagani mai dan buje da kitson attach akai tayiwa yarinyar yare tare da dan gusawa ta jaye naji tace min you are wellcome tana mika hannu in bata kayan na mika mata dama a gajiye nake lokacin. Abunda mummy gidan Rabakaya maman yaya habib ta fada min da naje sallamanta dashi na fara arba don cewa tayi Aeesha zaki iya zama gidan yaron nan don na sanki da yawan addini. Shiko gidansa kamar gidan kafirai yake don yan uwan matan nasa dake zaune taba agidan ba sallah ba salati sai kafirci. Zan iya mummy na fada a kunyace tare da nuna mata ba komai a zuciyana don yadda tayi maganan cikin yanayin damuwa fam a zuciyarta . To ki hada da hakkuri kije kiyi abinda ya kaiki ku rabu lafiya kinji don basira bata da dadi wallahi duk da farfar din da tazo nan tanawa mutane na karya . Abinda ya hadasu da fati ke nan lokacin har muka samu sabani dasu saidai ke nasan kinfi fati hakkuri saukin abin ke nan . Sai gashi suna gusawa daga kofan nayi arba da wasu katan maza biyu dagasu sai wani dan gajeren wando dayan yarinyar kuma cikin ta ukkunsu itama da nata dan buje ajikinta iya cinya. Duk da ana ruwan sama hakan baisa sun daina abinda sukeyi ba watau karta don cards ne a hannunsu suke bugawa a lokacin da ake son bawa ya natsu. Wa,iyazu billahi na fada a zuciyana ina kawar da kai daga kallon tsiraicin da nake masu lokacin don dasu da tsirara duk daya nake ganinsu a idona. Yarensu tayi masu duk suka dago suna fadin you are wellcome sannu da hanya na amsa da hausa yauwa sannun ku itako sai cewa take Aisha Aisha yau gaki Abujan mu ko ? Saidai kiyi hakkuri da dan gidan namu fa ba girma nace haba dai ba komai anty ta nuna min kujera na zauna ina mamakin wanan bakin rayuwan dana fara sama a cikin zuciyana. A cikin yare ta dakawa wace muka sama ta bude muna kofa tsawa kamar fada naga ta mike zuwa kitchen dinsu sai gata da wani farin goran da aka durawa ruwan sha a gida yayi sanyi a ciki tare da cup ta aje a gabana. Tun kan budurwan ta dago nace a,a yau akwai sanyi ai nagode ki mayar ina Amira ban ganta ba na fada ina dan dube dube naji uwar tace dani tayi barcine yau zata sha mamaki idan ta tashi ta ganki gidan nan ai zamuga zumudi. Sai naji dayan na mijin na irin yarensu da ita ta bashi amsa a gyatsire tace emba. Wai ashe ya tambaya nima sister din baban Amira ce tace dashi eeh hira take jana dashi niko hankalina duk a tashe yake lokacin da mamakin wanan rayuwan kamar na kafirci da nagani a gidan yaya habib . Ba Abinda ke raina sai kyankyami wanan gidan da zamu gaurayu a cikinsa muyi rayuwa har tsawon wata uku dasu haka wai ? Maryam ce ta kirani a waya suji kona sauka lafiya nace gani ma a gidan su anty Basira tare da ita zaune muna hira na mika mata wayan suka gaisa kafin ta miko min. Tun wanan lokacin dana fito da wayata naga irin kallon da sukai min yasa nasha jinin jikina da lamarinsu can na kalleta nace ina son inyi sallah anty . Cikin irin yadda suke magana kamar tsawa ta dakawa wata tsawa tana yare ashe tace taje ta gyara bayine lokacin koda na shiga yin alwala din haka nayisa cikin kyakyami na fito dakinsu tace in shigo inyi sallah. Saboda naga kayan yaya a dakin wajen gadonta yasa nagane dakin kwanansa nan nan nayi sallah har la,asar kafin na fito . Lokacin Amira ta tashi daga barci nafito daga kofa na tsaya na kira sunan ta tayi wani irin juyowa don jin muryana da tayi a bazata. Ta mike tabar abincin dake gabanta da sauri zuwa wajena haka kawai Allah yasa muna kaunan juna nida yarinyar hannunta naja zuwa wajen abincinta nace ta zauna taci saida kyat da taga na zauna kusa da ita ta yarda ta zauna itama ta soma cin abincin tana dan waigena. Saiga namijin ya kawo min wani farin dafa duka a cikin plate da gutsiren kifin teku ta tsakiyan nasan taji nauyin hakan ne yasa tace kici abincin mu da manage anty Aisha haba dai ai nagode. Idan na kalli wanan abincin sai naji bakina ya cika da miyau ya cika min baki hakana dai nake zaune ga kayana har lokacin aje a falo gefe daya kafin su gama cin abinci tana fadin bari mu gyara maki dakin da zaki zauna a ciki. Dakuna biyu kacal nagani a gidan kuma haka suke zaune da wa yan nan katan mazan da basu da tarbiya a ido don rashin kunya zaku zauna a haka cikin gida. Ni dai har na shiga dakin nawa inyi sallah magariba yaya bai dawo gida ba a lokacin wa iyazu billah na fada a raina dana shiga dakin don ko wani tsami da bashine irin na kaya sun hadu da sanyin dama ga kuma tsamin dauda din nan shine ya daki hancina a dakin. Ba yadda na iya haka nayi sallah cikin kyankyami kafin na mike na dauko rigan barcina wando da riga sai zanin dana daura sama na haye gadon da katifanshi duk yayi laushi kana jin katakon gadon na sukanka har gara tsohon katifana na gida da aka cire a dakina yaran anty safiya yanzu ke amfani dashi falon mu da suke kwana. Sannu a hankali nagama shirina tsab ina mamaki wanan rayuwan da nagani a gida yaya habib sam ban taba tsanmani ko zaton inzo inga hakan a tare dasu ba. Mai karatu kada kice na raina da irin arzikin su a,a wani rayuwace ta daban da bamu taso a cikinsa ba na tsunta a nan din da yake jikina da gaji a haka barci ya daukeni bayan duk na adana kayana nayiwa komai security saboda gidan dana gani a watse. Lokacin da ya dawo nayi barci don Basira tazo ta fada min ya dawo in kuma fito inci abinci ta samu nayi barci a lokacin donshi bata tasheni ba ta barni. Sai cikin dare yunwa ya tayar dani ba abinda zanci a lokacin na mike don inyo alwala shine naga wanan dayan yarinyar cikin yan matan dake gidan kwance a kasa tana barci a dakin itama. Nayo alwala na dawo na tayar da sallah lokacin ta dago tana gaidani na amsa mata ta koma barcinta ina idarwa na koma saman gadon ina danna counter dina sai wajajen asuba na fara jin buruntunsu. Wai wanka sukeyi kada su makara zuwa wajen sana,ansu ta fada min saida suka rarage na mike naje nayo alwala nazo nayi sallah asuba. Kafin nayi shirin wanka na fito na zauna ina shiryawa don nima ranan zanyi reporting inda zanyi aikin gwajin da aka turo muyi din. Tsab na shirya cikin irin kayan da suka sa muka dinka don zuwa ma,aikatan dashi bujena har kasa nayisa banyi guntu ba. Sama na kawo dan hijjab baki half sunna na dora akaina maimakon hula baki da sukace muyi amfani dashi idan zamu saka kayan. Na fita falo don in duba lokaci naji wanan yarinyar ta kirani da anty na juyo ta tausa murya tana fadin na adana komai nawa ko ? Nace ehh sai naga ta gyada kan ta alaman to shike nan har zan juya na sake jin tace dani in rufesu insa sheda koda an taba zan gane . Wa zai taba na tambayeta tace indaiyi yadda tace min din don tsaro ina kallo ta dauki wanan zanin dana cire na dan baza a kofa shi ta dauko ta yafa min saman kayan nawa nace mata nagode. Can aka kwala mata kira muryan Basira ce ta amsa a tsoroce ta fita ban sake jin duriyan su ba kuma wai ashe sun wuce kasuwa ke nan wajen neman kudi. Allah ya kawomu nace na yunkura tare da saba jakkata da wanda na saka na,urorina a ciki na goya sai gata tace yayana ya fito inzo mu gaisa dashi. Shikam tsab na gansa yana zaune yana shan shayi shida yarsa Amira nayi sallama ya dago yana fadin a Aisha harkin tashi ashe ko yaune zaku fara fita din ? Nace ina kwana yaya saida ya nuna min wajen zama a gefen shi ya amsa min yace ni baba ya kirani yana min bayanin da bangane ba ? A ina zakuyi aikin naku ya tambaya nafada mashi sunan wajen da sauri naga ya dago kai ya kalleni kafin yace amma kina da sa,a gaskiya. Ko wanine yayi maki hanyar zuwa nan din nace a,a daga school din mu daine suka turomu nan kai tsaye yace gaskiya daku dasu kunyi sa,a kwarai da gaske don ba waje bane da ranke ranke ke zuwa balle ku yan koyon aikin . Yanzu abinda za ayi ki karya sai in saukeki
Chapter 94 · 0% Book details