← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 101

Sashe 93

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da Auwal yace dani urgent ne sakon hakan baisa na bude a ranan ba saboda ina zargin wani tarkon irin yaudaran nasu suka hada min kuma. Takaicin hakan ya hana in bude inga meke cikin jakkar alokacin saboda gudun sabon yaudaransu gareni. Hakan yasa sai washegari da asuba bayan na idar da sallah lokacin ba wanda zai iya shigo min daki na jawo jakkar na bude. Idona ya fara tozali da na,auran bincike irin ta siri wanda ban taba mafalkin mallakanshi a duniyan nan ba saidai ingani a wajen wani kila balle a yanzun da nake daliba ? Yau sai gashi a matsayin nawa wai cigaba nayi da zaro abubuwa duk na,uran ukku wanda zai amfanenine wajen aikina da zanje koyo har Abuja da schoo din mu ta turamu yi. Sai kuma sabuwar waya dal da hannuna ya dauko karshe wayace ta gaba da wanda nake riko yanzu a hannuna can a cikin kwalin karamin na,uran na tsunci wani envelop a cikinsa da rubutun Man Bash a saman takardan ido na tsura rubutun nashi na dan lokaci ina tuno abubuwa da dama a zuciyana hakan yasa. Jikina na rawa mika hannu na nake kokarin bude takardan acikin tsoro tare da fargaban abinda zan iya samu rubuce a cikin takardan. Ina tura hannu don zaro takarda sai na zaro kudi suka zuba daga ciki irin kudin kasashen wajene sabbi a mike cikin takardan da nake zaton wasikace da farko . Duk da a lokacin bansan darajan wanan kudin ba ina dai ganin su sometimes a photuna ko a film don haka nasan abune mai daraja sosai. Ina kai ido sai ya sauka ga yar farar takardan dake a nade tsakiyan kudin na dauko na bude nan na fara ganin bayanin komai dake cikin wanan jakar ya tsara min yadda zanyi amfani dashi har kudin dana gani din saida yayi min bayani akansu. Kudine da zanyi amfani dashi wajen cin abinci zirga zirga da sauran abinda zai saya inyi daraja a gaban kowa koda wajen aiki ba,abamu alwances ba a ma,aikatan ya kasance ni ina da kudi a hannuna haka yai bayani a gajarce. Bayan na gama karantawa na koma na nikesu yadda na samesu baki a laikum ciki da mamaki fam a zuciyana. Don haka lokacin haka na koma gado na lafe kwance ina tunane a kan halin Man Bash din. Zuciyana fam cike da tunanen shi wanan Bash din wani irin mutum ne wai haka da bahagon rayuwa sunan wani littafin makawa. Monday da safe sako ya shigo min na accepting letter dina da cewa next week coming zamuyi reporting a ma,aikatan don fara training din mu a can din don haka bani da wani dogon lokaci yanzu. Dole na fara shiri saidai banson barin garin ba tare dana tabbatar da fara karatun yaran antyna ba da yanzu na kwallafawa karatunsu rai kuma ina cikin process din zancen tafiyan yazo min. Don haka ban bar gari ba saida na tabbatar da yaran anty sun fara karatu samira taje sokoto kwananta biyu ta dawo da takardun su kananun na jefasu primary din da Sama,ila ke zuwa ta gwaunati . Inda Samira ta samu gurbi a COE amma late addimition muka samu ita kuma Asmau zata yi jerabawan waec ta maimaita shekara mai zuwa inda zata dinga zuwa makaranta daukan darasi. Bayan na gama dasune na fara shirina na tafiya abuja a gagauce ba wasu kaya mai yawa na dauka ba dan akwatina na tsakiya shina zuba tufafin da zanyi amfani dasu. Sai kayan amfanina a cikin karamin kuma na loda sauran tarkacen unders dasu mai da sauran abinda zan iya bukata a can din. Tafiyace wadda ban taba yin irin saba haka zanyi inama nake zuwa nidana tashi a kifin rijiya bansan ko ina ba sai wanan garin kawai. Mun dade da Abbu da Ammah a daren da zan tafi din suna jamin kunne tare da dorani a hanya kan zama a bakon waje da zanje yi a yanzu. Kowansu yayi min iya nasihan daya dace inji daga gareshi don Abbu cewa yayi shi yayi niyar kaini da kansa har gidan yaya habib din amma yaya din yace basai yazo ba ai zan iya. Don hakane tafiyan ya fasu dashi din yanzu ni kadai zan tafi kamar yadda yaya din yace dashi da mun kusa sai in kira waya sai azo a daukeni duk inda nake. A karshe Abbu ya ciro kudi a aljihunsa ya miko min da sauri na girgiza masa kai ina fadi Abbu ba sai ka ban kudi ba duk abinda zamuyi sun bamu kudi a kansa da suka turo muna jiya a banki. Ai kaji saukin abin naku ba sai iyayye sun wahala ba dai nikan karatun nan naki yazo min da sauki Nanata duka duka ban kashe wasu kudi daga aljihuna ba akan karatun ki sai nake gani ke mai sa,ace nanata. A raina nace munyi sa,a dai Abbu Allah ya tsaya muna ya turo muna Man Bash a rayuwan mu mu duka komai yake zo muna a saukake a rayuwa. Zance rakiyana kamar na barin garine a lokacin saboda gaiyan yan rakiyan dana samu zuwa tasha maryam farida samira da Asmau yar gaban goshina rike da hand bag dina a cikin damuwa. Don hakane mutane da yawa a unguwar mu suka sanda zanyi tafiya a ranan har gareji mukaje tare dasu munyi sa,a saura mutum biyu motan ta cika. Ba a dauki lokaci ba sai gata cikon biyu ta iso motan ya cika don duk uban sammakon da mukayi motan farko ta riga data wuceni a ranan. Saita biyu muka samu a lokacin don haka ba,ama gama saka kayana ba cikon ta bakwai tazo zamu tashi ke nan mubada kudi. Na mika masu nawa tare da kirga wasu kudin na mikawa maryam ita da farida tace haba dai Aeesha kada kimin hakan nace ba zaki samin albarka ba ke nan ? Jin hakan ta karba sai kuma su asmau duk da na basu amma bai hana in kara masu ba nashiga mota bayan adduan da Abbu yace inyi tunkan in baro gida na tawakhaltu illa,lah lahaula wula kuwatu illabillah na shafa a fuskana sau uku. A baya muka zauna mu mata da wata musulma da wata kabila don ta shiganta na gane hakan suna tsaye mota ya tashi naji idona ya ciko da hawaye lokaci guda. Har na daina ganin su sannu a hankali muke fita garin ta bangaren da ban taba sani ba a cikin kano har zuwa lokacin da muka hau titi da kyau driver ya fara sharara gudu damu a motan. Inda wasu na waya wasu kuma suna hira irin ta kusa dani ke nan mai bakin surutun tsiya da son a sani. Irin mu dai sai faman raba ido nakeyi ina bin ko ina da kallo tare da karanta sunan yan kauyukan da muka shigewa a hanya wanda nake jin sunan su. Ta gefena dake zaune a tsakiya ta dan kalloni tana fadin you seens worried baki so barin yan uwa ba ko haka gida yake ba dadin rabuwa wallahi ? Murmushi na juya ina danyi kafin na lumshe idona tacigaba da waya da aka sake kiranta a lokacin ina jin damuwa don surutun da takeyi har cikin raina hakan yasa na dan ja tsuki ina gyara zama ta hanyar jingina kaina da gefen glass din mota. Tana aje wayan ta juyo take fadin akwai sauran zama har yanzu shiyasa nafi son inbi jirgi don yafi min sauki da shiga motan nan sauki . Sai naji dayan matan ke fada mata ai don yau babu jirgine kuma tana son shiga office da safe itama ta biyo mota. Ban tashi ba ina dai kwance ina jinsu nayi shiru saida muka kai kaduna driver ya tsaya wai za a duba mashi mota wanan yasa muka fito daga cikin motan . Ina kallon yadda suke sayayyan abubuwan ci saidau ni komai ban saya ba da sunan ci a wajen a hankali na tura hannuna a cikin jakana na dauko air pies dina na makala ina sauraren sheck albani zariya. Inda yake bayani akan sallah don kullum ban gajiya da saurarensa shine best malamina a lokacin wa,azin albani. Hakan yasa nake bin kowa da ido wajen har zuwa lokacin da aka gama duba mai motan cikin abinda baifi minti talatin ba muka kama hanya kuma. Saidai tun a nan yanayin garin ya sauya sanu a hankali hadari ya hade ko ina bakikirin ba,a dauki lokaci ba kuma ruwa ya sauko mai karfi haka muka iso Abuja ana lema ruwan sama. Wanan ya tayar min da hankalina gashi ban kira yaya ba kamar yadda yace na kirashi ko matarshi idan na kusa isowa Abujan amma don ganin ruwan saman da akeyi din yasa ban kirasu ba a lokacin. Ga ruwan sai an dan tsagaita sai kaji ya dawo kuma dole haka na daga waya na kira yaya habib kira biyu bai dauki wayan ba yasa na gwada kiran matarsa basira itama bata samu dagawa ba. Ya sallam na furta a fili yasa wanan bahaushiyan da muka shigo mota daya dan kallon inda nake tana fadin wanda zai daukekine baki samu ba ko nace wallahi. Nima gashi ina kiran gida amma sunki su daga call din may be suna can suna barci tunda ban gida. Shekaran jiya na bar nan Abuja naje buki kano shine na dawo yau wani unguwa zaki ke ta tambayeni nace garki which erea nace erea ten yadda naji a bakin basira din matar yaya habib . Sai naga ta dan tabe baki tana fadin ni gwarinpa zani ba waje daya zamu ba dana daukeki sai ga wayana yana ringing na daga da sauri yaya habib din ne a layi yake fadin. Aisha kun kusane nace ina tasha tundazun naga ana ruwane ban kira ba yace kinaji Basira zatazo ta daukeki don ni ina nan nashigo Nasarawa ban kusa da gida yanzu. Ok to yayi nagode naji ya kashe wayan shi tace kin samesu ko nace eh nagode da kulawan ki sai wajen kamar rabin awa anty Basira din ta iso tana dan waige waige hangota da nayi yasa na fito daga cikin motan har lokacin ana dan yayafi mai karfi . Kwankwasa mata glass nayi ta juyo tana fadin to har
Chapter 93 · 0% Book details