Sashe 9
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
fada akai sai faman fadin umm,umm ikon Allah dama shirinsu ke nan Abbu ke fadin. Kafin naji yace abinda nake so dake shine daga yau ki kawar da idonki acikin wanan zance don Allah ku bar masu suje suci in zasu iya in ba yau akwai gobe ai a wajen Allah. Kin ganni nan Ammah banson fitinan daya shafi gado ko kadan badai sun sayar da wajen ba to kuyi hakkuri kusa masu ido kuga ikon Allah ai inku matane suna ganin baku da yadda zakuyi akwai maza a cikin ku donshi dayyabu ba zai yarda ba haka kuma ba,a sab abinda gobe zai haifar ba ai ga bawa. Jikina ya kara sanyi da zancen su kamar ranan haka na kwana banyi barci ba duk iskan da akayi har aka gama ba ai ruwan sama ba idona biyu. Haka na shirya washegari na fita zuwa school kwana biyu sai rama ya shigeni na fara ramewa a tsaye don damuwa dana saka kaina. Saukin abin karama nake a lokacin amma ibada ya shigeni sosai a zuciyana haka nake fitowa a tsakar dare cikin sanda nakan fito nayi alwala in raba dare ina gaida Allah ina neman daukaka a wurin ubangiji. Yadda malaman islamiyan mu sukr koyar damu a kullum wanan sai banyi wasa da hakan a rayuwana ba na rike hakan sosai a zuciyana duk da bansan amfani hakan ba gareni. Aeesha nayi firgigit ina dagowa dagawa tare da kallon Ammah din ina fadin na,am Ammah itama kallon mamaki take min a . . Keko me kike tunane haka har kira ukku bakiji ba lafiyan ki kalau kuwa yar nan tunfa dawowana naga sauyi a gareki kardai wani abu ya faru dake a bayana kika kasa fada min Ammah din ta fada. Cikin damuwa da kulawa take min maganan tare da maida hankalinta gareni lokaci guda nace cikin sauri Ammah wallahi ba komai daya faru dani bayan ki . To meke damunki haka yar uutana yaki zo nan ki fada min ta fada tana nunamin kusa da inda take zaune a lokacin. Hakan yasa na karasa ina sakin hawaye nace Ammah a cikin muryan kuka sai kuma na kasa karasa maganan dana so fada saboda tuna gatgadin da Abbu yai min kafin ya ban tarihina din a ranan. Hankalinta ne ya tashi gashi kuma ina fadin ba komai saina fake da fadin mafalki kawai dai nakeyi akan wata mata. Mata kuma na gyada mata kai wace irin matace haka kuwa nashiga uku ni Ammah nidai inba manya bace ta sa min ke gaba haka ? Bari malam ya shigo ya bamu hayaki ayi insha Allahu inkin tirara ba zaki daina ganin ko wace muguwa ba cikin mafalkin da yardan ubangiji. Haka kawai ban damu da dan kowa ba balle wata muguwa tasa min ya a gaba don hassada da bakin ciki kurwanki kurrr wallahi. Sai ta jawoni tana shafan kaina tare da tambayana kanki dai bai ciwo ko na girgiza kai alamam a,a gareta. Nayi kukana ma,isha a saman jikinta kafin na tashi na fara aiyukana nagida don kada ta kara jefa kanta cikin firgici. Da Abbu ya dawone take fada mashi shidai murmushi yayi ya dauko hayakin ya bata ta tukaka min ina ji ina gani ba yadda na iya da Ammah don nina jawa kaina hakan a lokacin. Abbune ya zaunar dani yana min fada akan na natsu na cire tunanen komai a raina a yanzu in dai mayar da hankalina ga karatu in samu inci jerabawana yayi min alkawarin ina gamawa insha Allahu gaba zai kaini in karo karatu gaba da secondary da yar gidan malam iro ke zuwa. Wanan magana da mukayi da Abbu ya karfafa min gwiwa yasa har nasake na koma normal na watsar da zancen Nana a zuciyana ban mason in tuno da inada wata mahaifiya bayan Ammah.