Sashe 34
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
said a na fitar da kayan naga yawan uban kayan da muka kwaso shagon duk da kudin man Bashir akai wanan uban sayayyan haka dolene nasan yayi fada idan ya farga. Amma saime da gamma saiga Auwal naming sallama har ciki ya shigo don yana ganin ya zama dan gida yanzu shi da akwati baba niki niki a hannusa da wasu tarkace ya kawo min don't gulma har daki ya shiga min dasu ranan kamar an kada kan yan gidamu sun fita wai sunje talla da uwarsu. Tare muka fita kofan gida dashi bayan nayiwa kofana key nan yake fada min yana gida aka kirashi yazo gidansu kharat ya dauki wanan din shine yaje ya dauko. Ai hjy Aeesha in fada making harka da masu kudi akwai dadi wallahi don nima yau a cikin farin cikin jimma,an nan nake don na samu alheri ba kadan ba gaskiya. Tun banson sakewa dashi da farko har yakai yanzu na soma sakewa dashi don ko yanzu dana jingina da mota INA saurarenshi nace malam Auwal yace that's my name koki kirani da Awilo lo gomba. Hakan ya dan ban dariya kafin ince dashi tsoron abubuwan dake ta faruwa nake a zuciyana Auwal ina jin tsoron idan ba wani tarko aka hada min ba don ina yar talkawana nazo na fada ciki a karshe. Dan shiru yayi yana tunane kafin yace dani to gaskiyane amma kuma banjin hakan gaskiya ni dai abinda na dauka shine yana son ki fito kamar kowa tunda kina tare dashi ta yadda babu inda wani ko wata zai iya rains masa akanki. Kinsan fa yaran masu kudin nan dason jan aji nidai gaskiya abinda nafi tunane ke nan amma duk da haka hakan zan saka maki ido akan komai wanan alkawari na daukar maki na hakan. Kinsan mu a barga aka haifemu anan kuma na taso cikin gidan sarki don iyayyena anan suke rayuwa har yanzu mu daine diya maza idan mun tasa saimu koma gidan mu nagado mu zauna ciki amma har gobe ina shiga gidan duk lokacin da nake son hakan anan ma muka shaku dashi idan yazo har sabo ya shiga tsakanina dasu tun muna kanana. Na tare da fadin ashe dai duk ku din ne yan saka masa ido kan komai yace gaskiya ko wanan aikin cancantana aka duba aka dorani a kai kuma ina jin dadin hakan wallahi. Saboda kina da mutukar saukin kai da sanin darajan dan adam Aeesha hakan yasa nake maki fatan ku kasance a tare duk da naji yana fadan ke din kawarshine kawai na dan lokaci. Naso ya fada min wani abu fiye da hakan amma sai yace yamma yayi zaije ya faka mota kada ya makara ko a hakan na fahinci wasu hiran da yai min din game da shi man bashir din kamar yadda suke kiransa malam bashir amma sai suka sauya da man bash ko man bashir. Saida dare na zauna na jera komai yadda ya dace haka kuma na ware wanda nazabowa yaran gidan mu dama iyayyena na kuma fitar da tsofin kayana da nake amfani dasu wanda Abbu yake min zanbawa su samira su duk da ban sani ba ko zasu karba din. Kayan kwalam dina kuma na hada su waje daya bayan na ware wanda zan ba iyayyena suyi amfani dashi don kome na zama banda kamarsu a duniyan nan koda kuwa yau ga uwata da ubana suna sani don dasu na bude ido nayi sabo. Washe gari weekend ne don haka na tiki barcina don ban fito wani aikin girkin abinda zamuci ba dama Abbu ya hanani hakan nice dai naga ya kamata in fito inyi din. Don in banyi ba haka zai fita da yunwa bai karya ba don Anty dai ko yaranta ba fitowa zasuyi ba suyi tunda ance wai insuyi bai kyau koba dadi yasa tace daga ita har yaran basu kara taba abinci da sunan yi kaji sakarai. Nasan kawai dai don ganinane yasa hakan duk da yanzu ba kullum nake girki ba wani lokacin idan na dawo sai in zama saboda gajiya. Duk da nasan dan sauyin rayuwan dana fara samune yake son jawo min hakan a yanzu idan ban girka ba Abbu zai fitane ya kawo min abinda zanci nida sama,Ila dashi da yakan hado da Aimana sai taking karba. Saina fada mashi tana girka abincintane kada ya damu da rashin karban nata yaso yin fadan hakan kome ya tuna kuma yayi shiru aka tafi a hakan. Yanzun din ma muryansane ya falkar dani daga barcin inda yake fadan rashin fitowa a girka abin karyawa a gidan shine na mike na fito da wanan ledan kayan shayin ina fadin Abbu ina kwana daga bayansa. Nana kin taso ke nan an tashi lafiya na amsa da lafiya kalau Abbu jiya nayi barci koda ka dawo yake fadin munjimane bamu shigo ba jiya mun samu aiki sosai wallahi ya kaimu har dare. Ledan na aje a gabansa ina fadin kayan shayine Abbu jiya muka shiga kasuwa da kanwar mutumin nan shine tayo min sayayya masu yawa ta kumace in dauki duk abinda nake sai na dauko maku kayan shayi da wasu kaya suna daki. Baki Abbu ya bude cikin mamaki yana fadin kanwarsa ma Nana bako shi ba ta saya maki wanan kaya haka nace wallahi Abbu tare wanan drivern nasu ya dauko mu shine tace a tsaya zatayi sayaya a wani shago . Karyan dana shatawa Abbu ke nan ya hau ya yarda dani akan ba zan masa karya ba don ya sanni farin sani kuma ban iya karya ba saidai kash Abbu bai san da na fara shiga system ba nima a yanzu. Na sake dawowa dauke da kaya niki niki a hannuna kafin na soma bayani da tace in dauki duk abunda nakeso kada inji nauyi ko kunya Abbu shine na dauko maka wanan jallabiyar don naga kanaso wanda Nana ta aiko maka ya tsufa. Ammah kuma turmin zani gashi gana su anty safiya da yan matanta juyawa yayi ya kalli Ammah tace to nima dai jiya ina nan nagansu da kaya niki niki ita da yaron nan dake daukanta yanzu sun shigo ashe ba karamin kaya suka dauko ba. Anya Nanata wanan kayan sayayyan mace be kuwa bafa karamin kudi aka kashe wajan nan ba wallahi Abbu macece ta saya min idan baka yarda ba muje dakai gidansu ka tambayeta kaji. Baba mekakewa mamaki indan ance macece ai idan mace nada kudi tafima namiji kashewa kawa abu don ta burge mutane. Allah ya kyauta yau Nana ba don ke bace wallahi ba zan taba yarda cewa mace tabaki wanan alherin ba haka to nasanki Nana ta baki iya karya ba tun kina karamar ki wanan yasa na yarda. Ita kuma inda niyar alheri tayi maki Allah ya saka mata da alherinsa ya biya mata bukatunta na alheri. Muka amsa da amin kafin anty safiya ta matso tana fadin mukan waga mata Allah ya saka mata da alheri wallahi nace anty ba matan aure bacema fa dalibace itama kamarni kudin daine akwasu kawai. Kinji arziki ba anty din ta fada nace ni ai jiya naga duniya banza da wofi haka zata dauka sai matsamin da take ki dauki duk abinda kikeso fa Aeesha kada kiji nauyi ko kunya Dana zabo was yan nan dariya ta saka min shine ta zaba min wasu riguna masu kyau da takalma da jakka. Bayan wanan kuma nace wallahi Ammah saida muka sauketa min kamo hanya wanan driver yake fadin ai haka take da alheri ita. A,a ashe haline yanzu naji magana Abbu ya fada nan aka sayo bread ga murnan kaya ga kuma murnan shayi da bread da za,asha ranan Allah sarki tallaka. Sai bayan fitan Abbune na kira Asmau yar anty safiya nace su kwashi kayan dana ware masu na kara masu son ina son in kara gyara dakin mu din kafin Aimana ta dawo na shirya komai yadda nakeso. Hakan ne ya faru kuwa dakin ya fito tsab kamar yadda na keson sa matsala dayace katifan kwarai da bandashi a dakin har yanzu. Amma dakin ya fito min tsab dashi ba laifi ranan yan arzikin yan gidan mu yana kai yar anty safiyace Samira tayi min kitson kalaba manya masu kyau da suka fito min da fuskana shar a lokaci. Wanan yasa muka fara shiri da samira ba kamar yadda muke kamar Annabi da kafiri ba don wayata yana hannuta suna kallon carton saida caji ya kare suka dawo min dashi. Tsohon wayata na bata a ranan don su samu na kallo a ciki tunda gidan mu ba kayan kallo yaro kuma akwai son kallo ko can haka uwar tace tana fama dasu kan kallo. Washegari ma tare mukai abin karyawa da ita din saidai ni ban maci ba na kwanta don in huta kafin rana lokacin ne Ammah ke masu fada tace koke fa da kika shirya da yar uwarki bakiji dadin kanji ba don't Allah ? Amma haka kawai kin dauki bakin rai kin sakawa kanki ga year mutane dubeku yau gwanin ban sha,away daku na fada maku run farko Aeesha bata da matsala yanayintane na shiru shiru haka ita. Zaku iya kai dare da ita batayiwa kowa magana ba gidan nan sai task to ai na fada mata a daki nima mai son ka shike damuwa akan ka dama shi sama,ila ai kinga tuni ya watsar da shirmensu dama anty sama anty kasa kuma yana samun alherinta . Daren Sunday din muna zaune tsakar gida muna shan iska kwance nake saman shimfidan Ammah Samira tana gefena a zaune da yar wayan dana bata tana kallo. Sai su Asmau dake bayanta sun gwagwafe sums kallo sukeyi a lokacin mukaji sallaman Aimana kamar an jefota a lokacin gashi munsan ka,idan dawowanta sai safiyan Monday idan ta shiga school daga can muyo gida. Ranan zumudi yasa ta dawo tun lahadi a cikin dare inda ta fake da karyan ta dawo tayi assignment ne ta manta bataje dashi gida ba . Nan ko zuwa tayi da safe ta nuna min ita din ta wuce sanina kan komai don taje ta shiryowa hakan a yanzu saita ban mamaki da safe idan zamu fita. Nikan tunda muka gaisa na mayar da kaina saman tabarman naci gaba da charting da nakeyi