← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 101

Sashe 6

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

sa ran hakan saida tana can kasa mai tsarki don can ta koma. Duk da dai bada yardan mu tayi hakan ba don data kawo shawaran komawa can din daga baya bamu yarda mata da hakan ba sai ta shamace mu ta sulale ta koma ba tare da sanin bu don ba zata iya rayuwan nan ba don acan ta taso tayi rayuwanta da komai. Hankali ya so ya tashi bayan batanta saida na zaunar da ita Ammah nan na bata magana don tafiyanta ya nuna tabar muna amananki a hannun mu nida Ammah din don wayiyar gari mukayi muka nemeta muka rasa a lokacin. Sai ke kadai a dankin kwanan kwace da yar takardan da wasu tarkace cikin leda data bari a gefen ki na daukeki Ammah ta bude ledan kudine a cikinsa masu yawa sai sarkan gwal guda biyu a cikin wani leda daure. Ganin batarta zai iya jawo magana tun kan mutane su farga da hakan yasa nayi shawara da ita Ammah washegari nazo nan cikin kano na saya muna wanan gidan nan a wanan unguwar a cikin kudin. Nakoma can kauye ba wanda yasanda hakan saiji sukayi kawai munce munbar gari zuwa nan cikin kano da kowa nawa wanan yasa kikaga ko dayan mu zaije gida bamu yarda muje dake har yau din nan don gujewa abinda zuwan naki zai haifar a kauyen mu din. Gudu tayi ta barni ke nan a wajen ku itama na fada ina kallon fuskan Abbu din da alokacin shima ransa a bace yake da tuno da abubuwan da suka faru a baya. Cikin murmushin yake yace dani ba zance gudun tayi ba kuma zan iya cewa hakan don hankalinta nacan kan nema maki inda zataji labarin mahaifinki daya tafi ya barku da kuma makomar dukiyanku data baro a can a lokacin. Wanan nake zargin ya mayar da ita wacan kasan a lokacin don mun taba samun labarinta wurin wani mutumin garin mu inda har tabada sako garemu yace taji dadin ganinsa kuma shima din yace bai ganta a mugun kama ba lokacin. Kinga ke nan duk inda nana take tana cikin koshin lafiya haka kuma muna a ranta musanman ma ke din nan da a yanzu tasan kin girma kin kai munzalin hakan a girma. Ba abinda muke kullum sai adduan Allah ya karkato muna hankalinta zuwa gida ta dawo cikin yan uwa kamar kowa wanan shine fatan mu a yanzu. Ki godewa Allah nana da kika taso a cikin mutuncin daba duk ya zata samu hakan duk da muke ba mu muka haifeki ba Allah ya dora muna kaunarki a zukatan mu fiye da yayan da muka haifama a ciki mu a yanzu. Don ke din kin kasance ammace a wurin mu idan munyi maki rikon daba daidai ba ranan gobe kiyama Allah zai tambaye mu wanan a bainan jama,a. Na sani Abbu banda kamar ku a fadin duniyan nan koda kuwa yau uwata da ubana zasuce zasu dawo gareni basu kaiku girma da daukaka ba a idanuna. Masha Allah tunda har kin san wanan to ina son ki cire duk wata damuwa dake kasan zuciyarki game da iyayyenki a yanzu haka kuma ki daina kwankwanto koke wacece daga wanan ranan . Don kema ya ce kamar kowa da aka samu ta hanyar halak banson in kara ganin ki a cikin damuwa wanan kaddarankice da Allah ya zano maki tun farko. Abbu yayi min magana da zasu kwantar min da hankali da wanda zaisa kada inga laifin mahaifana da suka haifoni kuma suka kasa rikona a hannunsu don saba lamba. Da haka Abbu ya fita zuwa kasuwa bayan ya ban dari yace insai taliyan hausa in sulala da rana inci komawa nayi daki naci gaba da tunanen duniya don har yanzu zuciyana ya kasa gaskanta labarin da Abbu ya ban game dani din ashe mutane sunyi gaakiya da suke dangantani da larabawa tabbas ni din yar balaraben asaline ashe . Jinin sune a jikina kamaninsune na kwaso nake ruwa dasu jinin su shiyafi karfi a jikina bisa ga na mahaifiyata wanan tunanen na wuni yi ni kadai a gida da haka har barci ya daukeni ban sani don idona dake da rankon barcin jiya da banyi ba. Koda ta falka karfe ukun rana ya gwauta a gagauce ta debo tuwa a randa ta shiga bayi ta watsa ruwa tafito tayi alwala zuwa sallah bayan ta idar wanan hoton dake gefenta ta kara jawowa ta zubawa matar jikin photon ido na dan lokaci tana nazarinta. Tabbas ko a cikin hoton rayuwa ya nuna tana cikin jin dadi da walwala a lokaci saboda yanayin da suka dauki photon ya nuna gidane hadade ko a dacan baya don akwai abubuwan more rayuwa a gidan da photon ya nuna. A fili take fadin don me zaki gudu ki barni cikin bakin ciki da takaici bayan kune sanadin zuwana duniya a haka ina kika shiga kika watsar dani haka kamar marainiya ? Idonta ta mayar kan wanan balaraben tun daga rawaninsa daya dan daura ga kai har zuwa fuskansa dake nuna tsawon dogon hancinsa zuwa dan gashin bakinsa kafinta mayar da idonta kan farar jallabiyan jikinsa tana runtse idanuwanta. Cikin jin kuna da wani irin tsanarsa a zuciyanta ba zan yafe maka ba ta furta a fili kayi sanadin zuwana duniya ta hanyar yaudara kuma ka wofintar dani a cikin duniya duk da kasan da ina raye a doron kasa. Hakana dinga sakin maganganu ni kadai a gidan kamar sabuwar mahaukaciya in na gaji in fashe da kuka inyi kuka saina gaji kuma in cigaba da magana. Har nagaji nayi barci a wurin saida almajiri yazo yana bara na falka sauran tuwon dana zubawa Abbu ya rage shina raba biyu na kirasa nabashi ya shiga jero min addua. Nan kofa na zauna bayan na debo ruwa a randa nake zauna na tasa abincin a gabana na kasaci da kyar nayi loma biyu naji tuwon bai wucewa hakan yasa na mike zuwa alwala nayi sallah. Haka na wuni ko wanka banyi ba a ranan sai zuwa yamma na dan samu zuciyana ya sake har na samu na dinga yan aiyukan daya dauke min hankali. Sauran garin tuwon daya rage na tuka muna don zai isa saboda daga bakina saina Abbu har miya na hada koda Abbu ya dawo da wasu kayan cefane yasanu ina kwasan tuwo. Tun daga kofa yake fadin nana ikon Allah a ina kika samo kayan girki na juyo ina fadin Abbu sannu da dawowa ya amsa da yauwa har lokacin da mamaki a fuskanshi. Ya sake maimaita min tambayan dayayi min da farko na bashi amsa da fadin Abbu sauran na jiyane daya rage na tuka muna. Allah yayi maki albarka nana ya fada nakanji dadi idan Abbu da Ammah suna min wanan adduan don duk sukai min nakanga fa,idan wanan abin
Chapter 6 · 0% Book details