Sashe 62
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga inda nake zaune na juya ina bayani naji yarinya ta rike min hannu tana fadin i know you na dan juyo na shafa mata kai kadan naci gaba da magana a tsanake. Ta kara makale min jiki tana fadin wait ta sanni uwarce cikin murya irin na kabilu tace a ina ta sanni ? Wai a cikin tv gidansu har tanawa uwar kwatance da film din hakan yasa na dawo da hankalina gareta bani ba duk wanda ke falon ma yana kallonta a lokacin ana sauraren shirmenta da uwar ke fassara muna. Gashi sai kwantan fatan jikina takeyi ta gani ko zai fita can tace wait zan mayar da ita irin jikina nace ehh na shafo mata kai Ina karba yar wayata daga hannun yaya Fahad days gama tura recording din vedio a wayarshi. Umma ke fadin sannu yar gidan Ammah mun gode da wanan taimakon naki garemu ba komai umma naga in ban kawo an gani ba sai anyita zargin Wanda bashi ba. Hakanefa umma din ta sake fadin kafin anty fati itama ta mike zata biyo mu lokacin uwar take fadin Fati kada inji kinyi zancen nan da wani harsh gane ansan sarkan nan na hannusu su juya zancen nan. Ba zanyi ba ai umma ta fada nan yar nan tasa rikici wait zata bimu uwar ta rike ta nidai na samu na fice daga dakin tare muka fito da anty fati har kofan gida ta rakamu ta kama ciki. Amma mummy kina da kasada Asmau ta fada nace aikina ke nan dama kasada ai karatuna ya shafi hakan yanzu kinga kowa ya fita zargi ai Asmau don ko mu ba zamu fita cikin lissafin zargiba. Koda mukaje gida shiru mukayi mun samu Ammah ta dawo take fadin ance kuna gidan ban ganku ba kuma nace Mina dakin umma da Anty Fati . Karban aikin abincin nayi kafin lokacin fitan my zuwa wajen bukin ranan yayi nikan ina gamawa daki na shiga kwanciya nayi sai barci sai zuwan su faridane suka tayar dani na falka lokacin Aimana ta dawo ashe wai gida taje ta dauko abu acewarta. Cacakata sukayi wai nasan zamu fita kuma na kwanta ina barci haka farida na kalla cikin karfin hali da muryata dake nuna barci yaci idona har lokacin nace ba. Wai kece kawar amarya dai halan in naga wanan bukin duk kin shanye zakinsa farida to Aesha ko bani bace kawar amarya kanwar amarya nake ko saida anty fati fa ta kara turowa a fada muna kada mu makara karfe hudune. Nina na rasa dalilin da yasa ta kula damu haka cikin sha,aninta maryam ta fada tana zama gefen gado sai Aimana tace. Kema ai kin sani mana tunda taga yan mata haka shar kun waye da kauyawane wallahi ko kallonku ba zasuyi ba kawai kun zamo hasken bukintane ku. Nan na barsu suna zancen su wanka nashiga nayi na fito na zauna zaman shiri suma dai hira sukeyi a wajen Wani dogon rigan lace mai kyau na jawo na dora saman gado kafin na juya na fita kodana dawo na samu dan kwalinsa a hannun Aimana tana fadin. Amma dai wanan lacce ba garin nan aka sayesa ba na dan kallota nace nan kuwa a Dan kwarai muka saya. Ta sake juya lace din kafin ta aje dan kwalin maryam ke fadin wanan tellan naki Aeesha badai dinki ba kan shi yayi wanan halan nace shi ke min dinki ai yanzu. Wait ina kika zakulo tellan don Allah tellan manyane fa garin nan yadda naji kai tsaye nace da it's khairat ta hadani dashi. Khairat wacece hakana nace yar gidan shehi ce ita tana UG four yanzu school din mu wanan dake karanta Education bata faye shiga mutane ba sosai data matsa saida ta gano tace what wanan ai yayan manyane Aeesha. Sister din su Man cefa na fada tace wai ina man don Allah tun jiya nake son in tambayekishi ai nace man ya koma America da zama Aimana cikin wani yanayi na ban tausayi. Tace ke ki bari don Allah nace wallahi da yanzu bakiji ya kirani ba ko kiga Auwal gidan nan da sako cabdi jam ashe karya ta kare maki ke nan Aeesha ? Jin abinda ta fada yasa na dago da sauri na kalleta tayi saurin fadin eh mana ai gaskiya na fada ina zaki samu irinsa yanzu don Allah ? Mutum kamar baisan zafin kudi ba yadda ya dinga maki basin kudi kamar wanda ake bugasu a gidansu ba jin zafi ko takaici ? Lokaci daya ya sauya rayuwanki fa Aeesha ki dubeki ki dubi gidan Ku a yanzu don Allah INA zaki sake samun wanda baisan zafin kudin ba irinsa haka yanzu ? To ai ba cewa tayi dake sun rabuba cewa tayi ya koma America da zama yanzu ko maryam ta fada ta sake fadin me hakan me nufi ya tafi basu kai ga matsaya ba ya tafi ke nan. Amma Aimana kina zance kamar wata mai bakin ciko ko hassada kin sani ko zai dawo ko kuma Allah ya bata wani wanda yafishi ma Aeesha fa bamu bane macece da kowa zaiso ta a duk inda ta shiga maryam ta sake fadan hakan. Wai ke Aeesha shike nan kin fita zancen yayana ko cewa sulaimam lokacin na juyo na kalleta nace farida aini banki yaya Suleiman ba kema kinsan inda matsalan mu yake ai. Yau ko zaizo nace shima aiya san ban kisa ba matsalan mu dashi ummace tunda tace ni banda asali na fada kai tsaye ga yar nata don tasan na sani. In Allah yayi ai ba wanda ya isa ya hana hakan saidai gaskiya koshi a yanzu ya ganki yasan kinfi karfinshi shida ko taya baida keko harda motar kanki a yanzu ni wallahi naso insan man din nan amma kuma ya tafi. Man Dan ka,idace maryam ko a school ba kowa ke ganinsa ba Iran kin ganshi ya fito yin lectures dinsa ne yana gamawa ya koma ciki. Na shirya tsab na dauko gyale da takalma da jakka na kara fesa turare muka fito bayan na rufo kofa mukaiwa su Ammah said mun dawo. Hakana suke matsawa su hudu a bayan motar nida maryam muna gaba muka nufi event center inda za ayi wasan a haraban wajen . Wurin ya cika dam da mutane na samu wuri dan nisa kadan na faka motar a gefe daya daga inda muke muna hango cikin taron muna ganin abindake wakana a filin. Farida ta matsa sai mufita muje mu samu waje a cikin taron muma ina duban yadda zamu tsara wajen haka zuwa bangaren mu zauna. Dole dai haka muka shigo wajen cikin jama,a muka ratso kaina a kasa ga mc din ya canza kida slow music na tashi ya kuma mayar da hankalin mutane a kan mu yana irin shakiyancinsu na mc a lokacin. Wurin zama muka kama faridace ta samo wajen muka zauna gaskiya ba laifi don zamanin nan kwaliya yana gyara mace ko wacece iya kudinka iya shagalinka don kowa ya kure adakansa a wajen wajene na yan mata da samari amma duk da haka wasu matan aure sun tafi wajen da yawansu ma. Kaina na duke ina karanta sako a wayana naji an rugumeni ta baya dago kai nayi mukai arba da kharat din da muka gama hiranta dazun. Cikin mamaki da baiya jin dadin ganinta nake fadin antu Kharat ashe kunzo bukin kuma ? Tace ehh family din mijin antyn mune angon tare mukazo dasu ta nuna min ta inda suke zaune tace amaryan takuce ko ? Eh family din mu daya da ita yar wanan Abbuce ita unguwa daya kuma muke dasu kice kune da amaryan ashe ? Dan dariya nayi ina mikewa na gyara saitina kafin nace muje in gaisa da anty din ta riko min hannu tana fadin har da yaya Salman yana wajen nan ai. Gabana naji ya fadi ambato min sunan salman da tayi sai naji kamar naga Man Bashir ne a yau din duk da bankai ga ganin salman din bama a lokacin. Amma a fili cewa nayi da ita ashe zamu hadu ke nan dashi lalai dai kam amma kuna waya da yaya magaji kuwa ? Sunan data kirashi dashi din ya daure min kai don ban taba jin wani ya kirasa da sunan ba gabana sai ita a ran taci gaba da fadin ance numbers din da akansashi dash yanzu basu amfani. Lokacin na gane watake nufi gashi kuma mun karaso wajen table din da yayan nata suke zaune naji tace anty ummi ga Aeesha ku gaisa. Ta juyo don kallon mu matar tayi bala,in kama da sir salman sosai tana sauke fara,a a fuskanta tace au kece Aeesha din Man Bashir wai kin dai bar kura tsakanin Magaji da mai babban daki. Zo ga waje ki zauna ta fada tana nuna min waje daga gefenta da sauri nace no thanks anty tare da yan uwana muke nazo in gaida kene dama. OK nagode ta kara fada saina kalli kharat din nace anty kharat bari koma wajensu kada suga na barsu zaune tace tsaya ai muna photo tare da Anty for remembering kinsan ba nan take zaune ba tana Ghana da mijinta dan kasuwane shi. Au dama ba kasan nan suke ba ashe na fada muka sata tsakiya mukai photo ai kafin na bar wajen munyi photo da wajen mutane biyar saiga Farida tazo tana fadin. Aeesha don Allah zo mu tafi kada ayi badamu ba taja hannuna na dan waigo ina masu sai an jima wai ina zamu na tambaya tace gun angon nai za a karban kudi gasucan ta nuns min su daga nisa zuwa lokacin su maryam na tsaye daga baya kadan. Wai nifa kinsan ba irin abin nan na iya ba farida da kunje kawai zaifi idan kun dawo ku sameni tace don Allah muje dai ayi a gaban mu gasu maryam can suna jiran mu. Dole muka karasa daga dan baya kadan muka tsaya muna jin yadda suke ciniki kamar wani kayan sayarwa suka kasa gajiya nayi da dan tsayin naja tsuki tare da dan juyawa ina fadin nifa na gaji zan koma wajen Asmau idan kun gama ku sameni naji sunce yyauwa ga wa yanda muke jira sun karaso motar yazo