Sashe 86
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yasa mai babban daki kara shiga cikin damuwa ta saka tako ina a nemo mata wa yan nan iyalan nata amma shiru . Gashi kowa na fadin shi baiga fitansu a gida ba balle wanda ya daukesu din wanan wani abin kunyane ke shirin faruwa a gareta. Daren da zasu cika kwana ta ukkune kakansa ya kirashi yana fadin wasan ya isa haka magaji kasako iya iyalamsa suna cikin wani hali a yanzu. Kafin safiya sai labari aka samu na dawowan shi gida saidai yayi kyau ya kara murjewa gashi in an tabayesa waya daukeshi amsa dayane shima bai sani ba. Amma ya gana da maimartaba sunyi magana dashi na siri wanda baiyi da wani ba ko a cikon iyalansa. Dawowan iya ya tayar da hankalin dattijuwa hjy hauwa mai babban daki uwargidan sarki inda a yanzu ta debe rai ga zargin jikanta da wasu da takeyi. Wasa wasa satin su biyu a wanan gidan aka sakosu a cikin dare suka dawo gida babu ta yadda zasu zargi cewa bashir ne yayi masu wanan aikin . Don mutanen basu danganta kansu dashi ba illa iyaka sun masu barazana da tambayan ta dukiyan mijinta inda takai ne ? Da wanan kan kowa ya daure ana mamaren ko suwaye suka kamasu din sai akafi dangantasu da wasune dai da ba,asan ko suwaye ba kuma ? Sai shige da fice akeyi gidan hjy kura abinda ya dameta ya dameta a lokacin kan ko waye ogan masu aikin nan yasan sirinta ciki da wajenta irin tambayoyin da sukai mata din masu tsauri. Gashi kuma sunce zasu fallasata duniya tajita asan aikin data aikata ga tsohon mijin nata marigayi da tayi sanadin barinshi duniya. Ga yan uwan marigayin dama suna zarginta kan hakan gashi wani da yasan komai yana shirin mata kutse a cikin lamarinta. Abinda ya daure mata kai shine yadda akayi wani mahaluki yasan zancen su na karshe da mijin nata dake zargin tana son halakashi din. Ga Hindu da bata san komai ba tun acan ta fara tambayanta da mama dama kinsan Abban mu zai mutu ashe ? Mama kece kika kashe mahaifin mu dama don kawai ki mallaki abin hannunsa don kawai Abba zai kara aure me kike nema kika rasa mama a gun Abba da kika yanke masa wanan huluncin haka ? Saida kyat ta samu dabara ya fado mata na cewa hindu ki natsu mana ki dawo cikin hankalinki don Allah wanan zance da sukeyi ni bansan dashi ba ? Mama idan baki sani ba yaya zasu fito da zancen su bayan kafin daddy ya tafi kuna kan wanan fitinan dashi dama ? Tsawa ta dakawa hindu din tace ki barni inji da zancen dake damun zuciyana hindu ba wanan shirmen naki ba don Allah. Cikin dare bayan kowa ya watse daga wajensune ta ciga tantama a zuciyarta anya kuwa batayi kuskuren saurin yarda da zancenTajjudeni ba na ya gama da Usman a lokacin. In bashi ba shiba ba wani mahalukin da yasan da zancen nan sai iyan zangina da suka hada plan din tare dashi kuma ta sallameshi tun wanan lokacin. Ta ina wanan zancen ya fito mata haka bayan kusan shekara goma sha yanzu ke nan har tayi dumu dumu da dukiyan usman ta sayar dana sayarwa tayi facaka da kudinta ita da yaranta. Yanzu ga kuma wani zance daga baya yana son tasowa a kan hakan dolene ma tagano ta ina wanan lamarin ke shirin faruwane ta tosheshi ga ga sagir yadda ya mayar da kanshi yanzu balle ta nemi shawaran dan nata. Munyi exam lafiya mun kuma gama lafiya an bani zabi waje biyu kaduna ko Abuja dole a can zanyi IT din nawa gashi duka garuwan banda kowa a can da zance zan zauna a gidansa. In bashi ba kaduna dai yafi min kusa da gida gaskiya ko weekend ne zan dinga zuwa gida inayin abina inyi kwanakina in dawo bisa ga abuja to amma matsalan gidan wa zan zauna acan din yanzu ? Da wanan tunanen na dawo gida ranan saida nayi sallah na huta a dakina nafito na mikawa Ammah kindarmo data ban sako in sayo mata. Wuri na samu na zauna ina fadin yau ina anty safiya Ammah kece min ta kwashi yarta sunkai kaya wani gida da aka kirata. Shiru nayi kafin can ince amma bai dace ace tana fita wanan harkan dasu ba gaskiya idan can su basu dauki hakan komai ba nan zasu fassara hakan da wani abu. Ai kinsan halin yar naki Aeesha nayi mata nuni da hakan tace suba komai bane a can to wakace kuma yanzu yadda take ganin tauraron nan nata ya haska a yanzu . Asmau ma so nake ta karasa karatun ta ita kuma samira tunda ta gama in gaba zata taje gaban idan kuma tana da tsayayyen ta fito dashi tayi aure. Murmushi Ammah tayi min kafin tace ai diyankune amma kinsan auren su yanzu wani fitinane kuma tunda daga uban har danginshi kaf sunyi watsi dasu a yanzu ko labarinsa ma bance sun sani ba a yanzu gaskiya. To Ammah su zauna hakane tunda sun isa aure dukkansu a yanzu ko mu in badon karatu ba aida yanzu an fara saka muna ido . Ke kin fi yar naki tunane don ita neman kudi kawai tasa gaba dasu bata tunanen hakan garesu bata ko san ba haka za a tabbata ana kallonsu ba dole dai ko anki ko anso akai ga hakan watarana. Zanyi magana dasu idan sun dawo tace ai ita samira din dazun nan ta fita zuwa gidan Akwai farida ta aiko nemanta nasan fita zasuyi. Ammah farida tasan abinda ta taka a yanzu yawon nan ba zai fitar dasu ba wallahi ato ke ka fada a zauna lafiya kila nikan idan nai magana suce min yar sa ido. Muna wajen muna hiran duniya har suka dawo Asmauce ta fara shigowa tana ganina ta washe baki na daure mata fuskana . Ganin hakan yasa tace mummy nayi laifi halan kinyi mana na bata amsa tana sauke kayan nace ina kikaje Asmau ? Kallon Ammah tayi tace aina fadi idan kika dawo kikaji nabi mama fada zakiyi wallahi gashi kuwa yanzu ke yadace ace kina wanan harkan ba aure gareki ba don Allah yarinya karama dake ma,u ? Tayi shiru nace kafin na bar garin nan saina tabbatar da kin fara karatu insha Allahu tace don Allah mummy nace insha Allahu bari Abbu ya dawo muyi shawaran inda zaki shiga daga ke har samira din. Tafiya zakiyine mummy nace insha Allah saidai bansan inda zani ba nima kaduna ko Abuja suka turamu gani duk garuruwan bansan kowa a cikinsa ba. A,a wallah abuja kan baga anty Basira da mijinta ba fuska na tabe alaman kai kafin na furta kinsan halin mutane Asmau ba kowane yake yarda da hakan ba ai ? Kuma ni yaya habib namu baizo daya ba wallahi dashi dama ita matar nasa dai muna dan dasawa da ita yanzu. Ina ruwanki dashi tunda ba a kansa zaki zauna ba da matarsa zaku zauna meya shafeki dashi kiyi abinda ya kaiki ki gama ki dawo ki barsu iyaka ke nan ko ? Nidai da ana samun haya ko a turamu wani waje da irin muke zama zaifi min Ammah kinsan fa surutun mutanen gidan nan namu ? Surutu kan ai cikinsa suke suyi sugama dadin abindai har yau basu ga wani daga gidan nan yaje kofansu roko ba yanzu dai saiki bari baban naku ya dawo kiji ai. Daki na shiga don in gyara kafin magariba yayi Asmau tazo muna gyara tare da ita wayana yai kara na dauka wanan sojan ne da yanzu ya zamo min chewing gun yakirani . Yana tambayana yaya exam na amsa da alhamdullahi yake fadin yana son yazo yai min weekend nace sai kace wata mai zaman kanta ? Why zakice min hakan baby don kawai nace zanzo in maki weekend aiba a gidan ku nace zan sauka idan nazo haka yake da saurin jin zafi matsala na dashi ke nan rashin fahinta da saurin fushi. Amma yana da kula sosai ko yaushe yana kan kirani yaji halinda nake yana kuma turo min da alheri akai akai jin nayi shiru sai kuma ya koma ban hakkuri yana fadin ranki ya baci da amsa nako ? Umm,umm don me raina zai baci kuma naga dai daga magana ka mayar dashi bakar magana Ok keba baka kikai min ba ko ? Iam sorry na fada naji ya saki dan murmushi yana fadin zanzo kaduna wajen hjy in dubasu daga nan sai in gangaro kano in ganeki . Ai da ka fada min tun farko amma kace zakazo min weekend aisai naji zancen wani iri a raina dariya naji yanzu ya kwashe dashi yana fadin tare da sister dina zamu zo ta matsa zatazo ta ganki. Don zanzo da sune zan sauka a kaduna da kano naso sauka direct idan na ganki sai in wuce zuwa wajensu yanzu kuma ta canza min lissafina a yanzu. Kace ina da baki kenan wanan weekend din yace insha Allah saidai ba kwana zamuyi ba don sunday zan dawo lagos na karasa mashi da insha Allah. Mun dan jima muna hira kafin muyi sallama dashi ina aje wayan Asmau tana fadin shikan dai da gaske yakeyi har zaizo da kanwarshi. Asmau su dai zo din kika sani ko zata zo bincike ne a kaina ta koma kuma wani magana ya biyo baya . Koma dai meye ai tazo ta fada nace ban ma dauka da gaskiya yake zancen ba yana da wuya din suzo kila dai ya fadane kawai . Yadda na fahinta kamar fa S matazun yana da mata ma,u don kinga ko two weeks ago yazo gida ya dubasu idan baida mata yana zaman bin hanya haka ? In mai kulane sai yazo kuwa ko don mahaidiyarsa mummy kinsan wasu sun san darajan kula da incense sosai balle koma meye ai dole aji komai nasa dai idan komai ya kankama tsakanin ku . Abbu ya dawo da dare saida na bari ya gama komai na fito nayi mashi bayani abinda zamuyi din shiru yayi kafin yace ikon Allah yanzu ba ayi a kano sai can kaduna ko Abujan Nanata ? Wallahi Abbi muma haka muka roka