Sashe 85
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni Aishatu ashe tsugune bata kare min ba a ranan don ko ina daki nagama sallah isha,i ina shirin kwanciya naji Abbu ya shigo yana kiran sunana da dan karfi. Wanda wanan kiran ke nuna alaman wani abune mai muhinmanci ya taso a lokacin da sauri na fito ina fadin gani Abbu sannu da dawowa ya amsa da kyat tare da fadin . Fito muje gidan Musa Rabakaya kema Ammamatan dauko gyalenki muje tare lafiya dai malam Ammah ta tambaya ai tunda kikaji hakan da sauki mu dai isa din muji ko meye. Oh ni yasu ni Amma tun da aka tarka bukin nan yarinyar nan bata huta ba kamar ita kadace bare a wajen nan yau kuma me zamu ji kuma ? Abbu bai tsaya kulata ba yai gama nan Asmau tace mummy barin biyoki muje samira tace shi nake shirin fadi kika rigani . Ammah tace kun dai san halin malam yanzu zai koro ku duk da hakan basu zauna ba tare muka fito dasu muka hango Abbu can har yayi nisa yana waige ko mun fito din daga cikin gida. Kowa na gidan hankalinsa a tashe muka samesu gasu baba mai akwai gaba dayansu a gidan muka shigo da sallaman mu Ammah ce mai karfin halin yin sallaman alokacin. Yauwa kun karaso ba ku shigo ai gamu nan baba mai akwai ya fada muka nufi can nida Ammah da Abbu suka nuna masa wajen zama ya zauna. Kafin yakai zaune din ya kara furta lafiya dai ko zauna ai zakaji Muhammadu wani fitinane ya kunno kai muke son sanin gaskiyan zancen don a warwareshi a nan idan mun gaza hukuma tashigo cikinsa. Wa,iyazu billahi Abbu ya fada baba mai Akwai yace kwantar da hankalinka abi komai sannu da yarka Aisha zan fara ke Aisha na amsa da na,am baba. Kece keda waya da kukai hoto a cikinsa ranan kamun fatima wajen buki da har kika ba salis ya tura a wayansa nace ehh baba nawane. Mun dawo daga wajen bukin yace munyi hoto nace ehh yace mu bashi ya tura shine na bashi na fada kamar yadda suka tsara in fada a ranan dakin umma koda hakan ka taso. Wayayi hotunan ya sake tambayana nace Asmau anty safiyab gidan muce ta dauka don ni haniya yayi yawa nace ta karba ta daukar muna abinda akayi. Hjy Aginatu kinji kamar yadda ya fada ai a dakata ina wayan nata ita na mika wanda mukayi vedioting din event aciki ina fadin gashi. Kamo muna wanda kika turawa salis din nace suna da yawa amma ga wasu tiryan tiryan baban rabakaya ke bin komai yana fadin umm,umm ikon Allah har zuwa zare sarkan ya buga salati ya mikawasu baba mai akwai yana fadin Aginatu kin cuceni wallahi. Alh kabar cewa na cuceka tunda ban san abinda nayi ba ga dai Lami ficika ta zare sarka a wuyan yarinyar nan mun gani daidai lokacin Abbu ya karba yana kallo yana salati. Ai kawai baba duk wanan bayayi a mikata kawai ga hukuma gaskiya zai baiyana a can salis ya fada ba za ai haka ba tunda yanzunma gaskiya ta baiyana ai tunda ga zahiri mun gani da idon mu. Ke Lami yar ficika ina sarkan yar mutane kika kai don na taushi zancen nan ne kada ayisa lokacin taro donshine kuma ban koma ba na dakata yaya habib da sai yanzu na kula da duk suna nan ya fada. Sai lokacin na san har dasu lami din suna falon baba rabakaya din ashe case ya rigada yayi nisa a lokacin mune aka kira a karshe. Wai ashe tun yamma suka fara yin case din har zuwa wanan lokacin duk mu bamu sani ba ya kara maimaita tambayanshi gare kamar farko . Lokacin tayi magana tana fadin ku gafarceni don Allah nima sakani akayi yanzu haka kuma sarkan yana can mun basa Nasarawa a sayar dashi an taya dubu dari biyu ba,a bari ba muna son kari. Wajen wa ke nan tace su Saratuce suka san maishi don saratu naba takai munashi jiya ita da kawarta a sayar din suka dawo suka fada min hakan. Amma Lami kinci amanata saratu zanki ba saida sarka yar uwarta hju Aginatu ta fada sai lami din tace yau muka fara hakan dake da zakice naci amanar ki ? Kome muka dauko su ake ba sayarwa ko don yau kina ganin dubu ya cika kikeson zame kanki a ciki ? Allah ya isa tsakanina dake Aginatu yau din nan zaki bar min gidana keda yarki da sauri Abbu yace taje ina bayan wanan shekaru da kukayi a tare ga iyali an zuba ? Iyali indon wa yan nan dakata abi abin nan sanni Abbu ya kara katse dan uwasa din idan rai ya baci hankali yake nemosa ai . Katsaya a bincika idan tana da hannu cikin wanan abin sai muji dalilinta nayin hakan ke Nana tashi kijeki ina kun gama da ita duk wani yaro a nan ya bamu waje saikai habibu da yarinyar nan saratu muke son ku tsaya. Su yaya salis basu so haka ba a lokacin sunso ayi komai a gabansu sai gashi Abbu ya nuna masu halinsa ya kauda idon mu akan abinda zai faru a lokacin. Karshe dai yadda mukaji ba hannun hjy su saratu a cikin satan sarkan saratune da kawar maman nata da wata hjy kudidi akai wana deal din suka ba saratu a karshe ta sayar masu amma sunce hjyn tasan suna hakan a wajen buki . Hannun da muka gani hannun hjy kudidine bana hjy Aginatu ba wanan ya wanke ta amma yarta kam tana ciki tsundum a harkan . Allah ya saukewa mutane girman kanta da rashin kunya da cin mutuncin ko waye da hurawa mutane hancinta a cikin unguwa. Don duk yadda ake son a rufe zancen ba zai rufo ba tunda gaban mutanen da sukafi biyu uku harma ankai goma sha akai case din . Ranan idan nace nayi barcin kirki a idanuna karyane don sai auna zancen salman dana Asmau nakeyi a zuciyana ingane gaskiya da mafita ko wani daga cikinsu. Saboda kaina da salman ya barmi akulle kan zantukanshi gareni ido rufe da Asmaun ta kira da kurman kishine kawai yakeyi a kaina. Na aje a raina zan nuna masa ni yar halak ce zan nuna mai mata suna suka tara ba yadda yake nufin kwadayi ko son kai ya kaini ga cutuwa ba. Da banyi niyar shiga school ba amma daga baya naji ina son shiga kawai don haka na shirya nashiga late minits don na samu mun fara lectures a lokacin. Ba laifi an dan dawo fiye da jiyan da muka fara attending inda malamin bai fita ba saida ya tsuremu mukai test test ukku mukayi a ranan hakan ya hanamu fitowa da wuri. Ga yunwa da nake ji ban samu cin abincin kirki ba tun a jiya saboda bacin rai kindarmo na sayo mai kyau na zuka naji cikina ya dan tasa. Hakan ya ban daman dauko waya ina dubawa inda na samu miscalled ratata a wayan daga matar yaya habin sai wasu layuka da sukai ta kirana da ba suna. Na fara kiran matan yaya din aka ce min not reachable at the moment ashe suna hanya lokacin sai kuma wa yan nan sauran lamban dana kurawa ido na gano na sojan nan a ciki shima yayi min kira biyu lokacin ban daga ba ina class. Lumshe idona nayi ina mai sauke ajiyan zuciya lokaci guda kafin na bude idon nawa kuma ina kokarin mikewa inda nayi sallah azahar naso na tsaya nayi la,asar don lokaci ya kusa. Amma hankalina yana aji don haka na mike na nade abin sallah na koma class na samu classrep din mu yana nemana ina shigowa yake fadin yauwa zo ki muna solving din wanan don Allah muna ganin zai fito muna a exam. Kallon aikin nayi tun muna one hundrent level aikai muna shi kuma man bash ya koya min shi sosai ta waya a lokacin. A take nayi masu solving din yadda wayan ke tafiya zuwa wani na,ura ta daban yayin daukan information na gagawa. Tafi suka fara min suna fadin lalai wanan da namijine da anyi zakakon dan na,ura saimu hada dake tun a yanzu mu dinga zakulo manyan kasan nan . Aka fada maku ita mace bata da daraja ko kimar irin hakan ne bandai yi niya ba banyi kuma na fada na mike nabar wajen kujerana na koma na zauna ina nazari aiyukan da Man Bash ya koya min a lokacinsa damu. Don ba karamin karuwa nayi da sanin saba da yanzu nake ji a zuciya daga shi har salman duk na tsanesu a lokaci guda don ban fahinci amfanin da salman yake nufi yayi dani ba har zuwa yanzu din. Ban kara marmarin ko a hanya in hadu da wanan salman din ba ko tunawa da wani abu daya dangancesu karatuna na mayar da hankali akai. Saboda hakan kuma banje gidan yar uwarsu da nayi niyar zuwa ba illa iyaka a bakin anty safiya nake jin sun koma ghana ai ita da mijinta da yaransu. Khairat kuma duk da muna school daya ban damu nasan komai daga gareta ba a yanzu don haka nima ban nemeta ba koda sunan gaisawa yadda itama bata nemeni din ba. Yar tallakawa nake amma ina da zuciya da kuma gudun wullakanci kan abin mutum yau da man bash ne yayi min wanan gorin haka tsike nasa ba zai kwana a hannuna ba zan maida mashi da abinsa. Shima din yanzu yaci albarkacin shawaran Asmaune data bani inda ba don hakan ba zaiga aiki da cikawa gareni duk da ya kasance. Yanzu yan gidan mu sun saba da dadin daulan daya zube muna muna sha,anin mu dashi a gidan mu duk da sunan biyanane na aikin fakaice da nayi wanda ban sani ba kamar yadda shi salman ya fada. Acan kuma masarauta a lokacin hankali yakai kololowan tashi sosai don sun samu bashi din ya nuna baisan komai ba akan batan su hjy kura da yarta da iya din. Murmushi kawai maimartaba yayi ya kyalesa ga abu a zahiri yana son sai sun gama sanin waye bashir zaisa ya sakosu . Kwana uku a tsare ba wanda ya waiwayesu hakan