← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 101

Sashe 69

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani gida babba mai kyau duk da ginan dane amma gidan ya tsaru iya tsaruwa don da gani ba sai ka tambaya ba a zaman baya gidan na ciki jerin gidanjen da sukai tashe a garin. Don yanayin ginan ya nuna hakan har yanzu kuma ko yanzu din ba,a canza fasalin ginan ba gidan yana da dadin kallo don komai a tsare yake amma yasha gyara da kayan alatu na zamani ginan daine yan gayu a yanzu zasu daukeshi a old mordel saidai ko yanzu din dubban mutane suna kwadayin ace nasune wanan gidan. Sannu a hankali wani babban mota ya tsaya a kofan gidan kafin a bude mutanen cikin motar su fara fitowa a hankali. Anty Ummi ce da yan uwanta ta kawowa kakanin nata ziyara kada ta koma ghana bata samu zuwa wajensu ba shine dalilin fitowanta ta fara zuwa wajen kanwar mahaifiyarta mami suka gaisa daga nan tace zata wuto gidan kakar tasu shine yaran mami din sukace suma zasuzo suka hade su hudu da yaranta zuwa gaida kakanin nasu sai ince wanan ahalin sunyi dace da gadon tsawon rai don uwa raye uba raye harda kakani tako wani bangare irin hakan dace ne da baiwa daga Allah. Don ba kowa Allah keba wanan falalan haka ba wani ya taso ba uwan ba uba wani uwace kawai a raye wani ko ubane kadai a raye wani kuma rabuwan aure yashiga tsakani haka zai taso koda suna a raye ya koma kamar maraye haka dai abubuwan tsarin rayuwan sukan zo wa bawa wani lokaci. Tosu wa yan nan ahalin har wace ta haifi iyayyensu din mata bata jima da rasuwa ba don a lokacin baifi shekara ukku data rasu ba. Tana tsaye cikin kulawa saida kannen nata kaf suka gama sauka a motan kafin su nufi cikin gidan kai tsaye kharat ce tace ga sabbinani a zaure fa mu fara shiga. Hakan yasa suka shigo ta kofan zauren gidan mai kama da falon mutanen da zauren babbane ga kujeru ga fankan sama data kasa agefe daya. Ga tarin littafai na addini gefe daya duk da kujerun dake akwai a falon ga shimfida irinta alfarma mai nuna jin dadin rayuwa ga mutum inda tsohon ke kishingida ya huta ko yayi karatu saboda zama dake masa wuya a yanzu don tsufa. Sallama sukai masa cikin girmamawa kafin ya dago yana fadin su waye yana mai kura masu ido kafin yace au yau kuce in shirya ina da baki tafe ai. Suka kwashe da dariya kafin anty ummi din tace wai tsohon nan kana gani haka har yanzu yace ko zaki ban aron idonki in kara da nawa nina fiki gani a wajen nan suka kwashe da dariya . Kafin sukai kasa cikin ladabi suna gaidashi yayinda suka mike kuma suka dane kujerun aka fara jero ba,a a tsakaninsu. Mai karatu kada in kaiki nisa wa yan nan tsofin sune mahaifan iiyayyen su Man Bashir da Salma dasu khairat su Ummi. Na fada maki a baya ds uwarsu kharat da uwar Man bashir mami ya da kanwace suma asalinsu dai yan bauchine mahaifansu amma zama ya mayar dasu yan asalin kano don kowa nasu na kano amma ruwan fulanin nan yana yawo a jinin ahalinsu har yanzu. Ainihi karatu ya shigo da hardo garin kano saboda hazikancinshi da zati na iya yaki da sauran dabarun sarauta sai ya zama malamin cikin a masarauta a lokacin . Yayasa mata sune su mai babban daki da hjy Umma mahaifiyar su ummi da salman dama na taba fada cikin labari inda Man bash ya nuna salman ma jikantane ta nuna mashi ai tafishi sani amma jikanta na jininta take son ganawan siri dashi alokacin. Sun gama gaisawa dashi tasa khairat su kwaso mai tsarabansa wanda tasan abinda tsohon keso dama kayan shayine shi nasa tsaraban suka shigo mai dashi falon nasa aka zube masa. Yana faman saka masu albarka kafin su mike zuwa cikin gida su samu Yanti kakarsu mace itama suka zube mata nata nan su taliya kayan shayi man turkey maggi da sauran kayan amfanin gida haka tazo masu dashi don ummi din mijinta mai haline gaskiya. Nan suka baje ana zuba hira yaushe rabo kaya kaya suka dauko zancen man bash a cikin hiransu suna koro masu yadda akayi da mai babban daki dashi man bash din kafin ya tafi. Murmushi Yanti din tayi tana fadin shi dan adam a yanzu lamarinsa sai Allah sai ya manta mafarin komai ya rufe ido akan gaskiya. Ita harta manta da lokacin auren mu kakan ku gashi ubansu daya da mai martaba kun sani haka nida ita uwarmu daya uban mu daya. Amma yanzu tunda na fahinci mulki ya rufewa hjy hauwa ido ni kaina da nake kawa wajenta na rage shige mata. Don a gaban kowa saita nuna kai bakowa bane ta nemi ciwa mutum mutunci ko a auren shi Ahmad da mami ai saida rayuka sukaso baci a lokacin don haka ta budawa idonta toka taso nuna ba zai auri mami ba sai yar sarkin zariya. Shi kuma ya nuna mami din yake so dole maza sukasa baki ta yarda akai auren da yake rabon yaran nan ne bata isa ta kaucewa kaddara ba a lokacin. Don yau tayi hakan ban mamaki cikin lamarinta kadan ke nan daga aikinta indai hauwa kulu ce zata iya yin fiyema da hakan wallahi . Waiko shiyasa bata son mune Yanti wallahi ban kaunar zuwa gidan sarauta sai in wata nawa banje ba sai in mami ta matsa min nakan je kuma kaje da bacin rai zaka dawo gida. Daya daga cikin kannen man bash din ta fada sai murmushi tsohuwa yanti tayi kawai husna din tace Allah hjy nakan zo nan sau goma banje gidan hjy ba. Takan ce wai mu masu akidar nasarane bamu da kunya ko tace bamu samu tarbiya ba a rainon mu ni abin yakan bata min rai da ita wallahi. Hjy dai batayi tunane ba takan mata da da yanzu nice a matsayinta donni mai martaba ya nuna yana so sai mahaifin mu yace ban isa aure ba a lokacin ga hauwa nan dai su shiriya tunda ta dan tasa ita saboda ita haka ta tashi da dan kuman jiki ga mazaune da yasa ake kiranta da mai babban daki wanda mahaifanmu suka saka mata kuma sunan ya bita ashe zata zamo mai babban dakin wanda bai sani ba saiya zata don ta auri maimartabane taci sunan . Amma haka kowa yasanta dashi dama da shi kakanku ya taso kuma sai mahaifisu ya aura minshi wanda akaiwa hakan shi zai manta mafarinsa yace sai yan sarauta jininsa zai aura mu mun gaji sarautane da Allah ya bamu mazajen yan gidan sarauta. Koshi mahaifinku ai bata so aurenshi da mahaifiyar kuba so tayi ta aura mata wani basaraken gobir bayan ga mahaifinku da kowa yasanta dashi zan iya cewa wanan ya kara hadamu fada da ba shiri tsakanin mu har yanzu. Don lokacin mun nuna mata mu shehi muke son yarmu ta aura ba sarauta ba shine ta dawowa ubansu da uwarku wai yaje ya aura masa din. Hjy Yanti kice dai anyi kwamacala a wancan lokacin anyi kan khairat an Allah dai ya kyauta sam ba halinsu daya da mai martaba ba don shi yakan taka mata burki kan wasu abu da takeyi a rayuwa. Yanzu kan ai ta hadu da Bashir indai wanan mai taurin kaine anty ummi ta fada husna tace yace ko mutuwa tayi kada a kirashi tace miskili saikazo ka kasheni ai. Suka kwashe da dariya Yanti din tace wanan yaron wanan yaron dama take takensa nasan zai rina donshi ba mutum bane mai ra,ayin saurata gashi kuma bai rage kakansa ba tako ina ya kwasosa saidai hasken mu daya debo kawai na halitta. Idan ita yar rabosane kome suka iya zai auri abinsa amma kan sai ankai ruwa rana da mai babban daki nasani sai ya nuna namiji yake kafin ta yarde masa. Yanti bakiga yarinya bace wallahi yarinya mai kyau da ita balabiya asali da ganinta kema zaki san ba jinsin nan bane ita gata kuma tana da iliminta an mace karatun ne ya hadasu nata. Za a kai kan don hjy har sheri ta lakawa yayan mu ta kira daddy ranan tana fada mai wai yajawa yaya kunne yazo yana mata barazana da bindiga zai halbeta. Suka kwashe da dariya sosai husna tace wallahi ta tsorata kowa saida ta fadawa amma gwaggo kura ta kara turata kan yarta ta kara tunzura kan zancen. Kinji wata mara son mutane ni wallahi badon umma ba sai in shekara ina zuwa garin nan banje gidanta ba. Kura ai bata rage hjy da komai ba saima kari data samu wanan da namiji ta fito da anga sarauta a wajen ta da mutan garin nan sun shiga uku da ita wallahi. Sai Allah ya ragewa aya zaki da mijin nata ya mutu duk da mutane sun camfata ita da danta tundai yan uwan mijin cewa sune suka kashe mijin don suci dukiyarsa kinga aiko abin baiyi ba. Nasan ba zatai hakan ba hali daine idan yayi daidai sai akama zarginka dashi yanzu haka hjy Nasare na zuwa goma gidan nan Kura bata shigo ba. Ai ba halinsu daya ba dama anty ummi ta fada mummy Nasare da zakaje ta rikeka bata son ka wuce amma mummy kura kamar batason kazo idan ta ganka saima ta tsiro zuwa unguwa tana ita fita zatayi fa. Sai bayan azahar suka bar gidan tsofin don zasu koma gida su dan huta kafin shirin dinner da za a fitayi karfe hudu zuwa dare duk da dinner din har biyu za ayi da wanda yan uwa zasu taru da kuma wanda za ayi bayan magariba ango da kawayen amarya kawai yanzu na karfe hudun suke son halarta su. Gasu husna da sai sun koma gida sun dauko tufafin da zasu saka don basu sanda zancen bukin ba sai anan sukeji yass suka tafi gidan nasu baki daya. Saida ta gama photo da uban harsu maryam sun gusa suma yace ta kirani nazo na karbi wayana da yake faman juyawa a hannun nasa na dan lokacin . Hannuna da yarinyar tajan yasa dole na bita zuwa lokacin ya fito da kafafuwansa duk daga cikin mota
Chapter 69 · 0% Book details