Sashe 73
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Faridace tazo ta kiramu muje za a shigo da amarya hakan yasa muka barsu don zama a nan dama a tsarge nake duk na dago kai zan samu data daga cikinsu ta kura min idanu tana kallona sai hakan yasa na tsargu da kallon da suke min. Munje din an shigo da amarya harkace dai ta karya ta aron al,ada da akeyi a yanzu don ba,a san bahaushe da hakan ba.. Anyi buki anci ansha anyi raye raye su Asmau su samira Aimana balle farida kirjin buki sun cashe sunyi rawa sosai nida maryam ce bamuyi wani rawa ba tun bayan shigowa da amarya muka samu waje muka zauna. Anyi budan kai inda anty ummice a matsayin uwargida don itace matar farko a gidan kuma sarakuwa itace ta sayi bakin amaryam da kudi masu tsada saida kowa yayi ihu. Sannan wasu a cikin dangi sukai ta saye suma abin gwaunin ban sha,awa dai anyi photuna harma da wa yanda ban sani ba haka zasuzo suce ayi photo. Su khairat dasu husna muyi sosai dasu kafin na nemo matar yaya da dai muna tare tashi yin hoton yake dan rabamu sai ta dan sake dani muna hira jefi jefi tana tambaya wasu abin. Don haka na nemota don ganin har anyi isha,i a lokacin abinda akace karfe shida da rabi za a tashi nida ita sai asmau da maryam muka samu fitowa wajen mun bar sauran yan uwa a ciki. Ina tafe rike Amira da tayi barci wani soja yasha gabana yana fadin good day madam don Allah oga yace inyi magana dake yana nuna min motan ogan daya aikoshi wurina. Gaba dayan mu muka tsaya a wajen cikin duban direction din daya nuna din kafin nace you de crazy iam married woman murmushi yayi dan aiken kafin ya juya zuwa hausa yace saida muka tambaya don kada mu saba doka hjy a cikin dan murmushi. Gashi a can amma kaga sauri mukeyi a yanzu na fada ina masa wani kallo ayi hakkuri please ko minti biyune zuwanki zai tamaki rayuwana rashin zuwan ki kuma akasin hakan he son Allah please. Na fahinci me zamcenshi ke nufi kai tsaye yadda a take yai min magiya da fada min gaskiya a takaice na Dan juya kafin na sauke ajiyan zuciya nace . Shida ke son ganina aishi zaizo nan ga motana a can na fada ina kokarin wucewa naji yace sorry hjy babbanne fa son Allah ki daure. Hakan baisa na tsaya ba na nufi mota don yarinyar tayi min nauyi a hannu uwar ta zauna na mika mata ita su maryam suka bude baya suka shiga. Hjy gashi can a jikin wancan motan ya sake fada hakan yasa na juyo don ganinsa a tsamanina zanga tsoho tunda yace dani ogansa kuma zai iya laifi. Sai gashi naga matashi ne ashe yake nufi da ogansa din tare muka karasa wajensa yake wani kame masa irin yadda suke sarawa nagaba dasu din nan. Hjy barka da lokaci ya fada bayan wanan din ya tafi barka na fada a gundure sorry na bata maki lokaci ko ? Gani nayi kamar tafiya zakuyi yanzu din yasa nace ya tsayar min dake i am Yusuf Sha,ibu matazun amma zaki iya kirana da Y S matazun as you see ni ma,aikacine na soja da fatan banyi laifi ba don naga kamar kina sauri. Eeh ina tare da matar yayan mune zan kaita gida baby dinta tayi barci ohh sorry ashe kuna tare da mutane yanzu ya za ayi ke nan ? Name fa na dan dago ina tambayan shi yake fadin kada in bata maku lokaci ko zan iya samun lambanki don Allah ? Lambata kuma gaskiya ban ba maza layina don tsaro baki yarda dani ba ke nan ya fada cikin wani yanayi nace sorry ba zancen rashin yarda bane kawai dai haka nake. A taimaka wanan karon kada abar bawan Allah da tunane abu a duhu ko kuma mu biku a baya zuwa gidan nakune yanzu din da sauri na katseshi da fadin ina ? No na karanto mashi lamba abu ga jami,e ko bai yarda da number dana bashi din bane sai naji kawai an kira layin nawa zan dauko wayata yace no nine na gwada saina kira. Au baka yarda ba ke nan aida ba zan bayar ba bazan fada ba din tona gode ya fada kamar bashi wancan matashin ya gama kamewa ba yanzu . Muje na taka maki ya fada hakan yasa muka tako zuwa inda motan yake ya dan tsaya daga nisa kadan yana gaidasu suka amsa mai yana tsaye har muka wuce sai lokacin na kula da wa yanda ke binsa a baya ashe. Kai mummy kina da farin jinin jama,a Asmau ya fada daga bayan mota inda take zaune a raina nace na banza don zuwan banza sukeyi tunda banda asali. Amma a fili cewa nayi kada kiyi min sheri ke samari nawa kikayi a wajen nan banda wanan kinga wanine kuma ? Mummy kin manta da mai baki dubu dari uku a hannune na gasa yana nunaki fa a ciki dazun yar sheri na fada. Ai aka maza suke da saka ido da zaran sunga fine lady mace mai kyau basa iya zama sai sunyi mata magana don ma ke baki da rigimane ba kowa yasan kina wajen ba ai matar yaya habib ke fadan haka. Maryam tace Aeesha bata da rigima bata da sake jiki da mutane da watace aida Allah kadai yasan yawan samarinta a yanzu. Meye amfanin tara samari gareni maryam ka tsaya da wancan ko wanan meye ranan hakan na gidama sun nuna maka kai ga yadda kake balle na waje ni yanzu karatunane a gabana ba wanan shirme ba. Ai hakan yafi maki idan kina da ilimin ki zaki iya tunkarab kowa a lokacin matar yaya ta kara fadan hakan sukaci gaba da magana ina tukina ina sauraren su. Don Allah in ankai wani waje ina son in sayi pamppers don wanan amalalan saura kwara daya ya rage muna OK na fada. A bakin wani shago naja na tsaya tare da fadin Asamau don't Allah karbo mata pemppers a shagon can na mika mata kudi kai haba dai bari bata mana nace barshi kawai ta amso mana. Taji dadin hakan don't irin godiya da tayi min a lokacin tace anty maryam gaskiyar zancenki fa gashi tun bamu fita motaba nagani wallahi ni da farko dana fara ganinta nace tou bukin har da irin wa yan nan a ciki bari muja a gefe daya. Kuma dana shiga dakin mommy din nan zanyi sallah sai naji anty saratu nan tana ta fada dake kinsan ranan muka iso kuma aka fara da fada. Nace to barin kama kaina nasan ba hakkuri ke gareni ba yanzunen zan nuna maku halina shiyasa na kama kaina amma yau dana dan zauna daku naji dadi sosai da har namatsu mu koma Abuja wallahi. Ba abindata fada yasa nake murmushi ba sai hausan ta daya surka dana yarenta don duk wanda yasan hausan yan lokaja kona Abuja irin harshen da take hausa dashi ke nan. Duk da banda kano bansan ko ina ba a wanan kasan amma saj nake jin abin yana ban sha,awa haka yasa kosu Asmau da suka zo har wanan ranan nake dariya idan sunyi wani hausa zakiji kamar wani yarene sukeyi ba hausa ba. Har kofan gida muka sauketa mijinta yana waje zaune a lokacin yana kokarin kiran layinta don dare yayi sai gamu ya fasa na sauketa muka juya zuwa gida. Abinda na manta ban fada ba shine Abbu yaja min kunne akan motana duk wanda ya tambayeni amsa dayane shine mahaifiyatace ta aiko da kudi aka saya min fakat don yawan surutun mutane amma ko hakan bamu tsira ba ai. Dan wasu zagin mahaifiyar tawa sukeyi akan wai tana can suna badala a saudi tana turo da kudi nan muna jin dadi shine saratu taso fada min a gaban mutane muka fita baki ranan. Don kosu anty safiya har Ammah basu san daba Nana ta saya min mota ba don cewa Abbu yayi Nanace ta turo aka saya min nan tabayar aka kawo min don yarda da zancen da sukayi da Bash kada a samu matsala wajen mutanen yan sa ido. Ba don wanan shirin na Abbu da daga gidan mu zance zai fara yawo daga bakin anty safiya itace mutum na farko da zata fara baradani tana bata min suna. Don ba zata taba tunanen ba ko wace mace bace watsatsa da ba sai tabi maza zata samu rabo daga garesu ba . Don haka ko yanzu da nayi ribas na juya da motana galleleyi zuwa kofan gidan mai akwai na faka motar saida akai zance a wajen da cewa. Wai yaushe wanan yarinyar tayi motane ko saboda bukine ta aro tun shekaran jiya nake ganinta da motan nan tana hawa ? Na rabaka wa zai bata aron mota kwana da kwanaki haka uwar tace kasuwa ta buda a saudiya ta aiko aka saya mata mota don karatu. Kutuman uban nan ana iya shige garin nan kaji yanzu da zaman kanta ta sayawa yarta wanan motan gaskiya kai waima tsaya dama ita iyayyenta suna rayene ko ince uwarta tana da rai dama ? Don uba dai nasan babu zancensa wani katon balarabe za a samu can yaiwa uwarta ciki azo a haifota a wullota nan tana tangariri,riya haka. Kai haba ku bari mana don Allah yanzu me yarinyar nan tayi maku yarinya mai mutunci da girmama na gabanta koma itace tayi laifin ai kaddaratane hakan . Bai kamata ku aji haka daga bakin ku ba ana waje guda yarinyar nan yaya kasa yaya sama ga kowan ku ba wani abin watsewa kuma da takeyi. Yaya salis ne a gefensu zaune ya tsawata masu wanda ya fara magana yace ai ba zaginta mukeyi ba zancene ya kawo haka bros. Ku daina haka don Allah ba kyau ya sake fada tare da jan tsuki yana kawar da kansa gefe daya yayin da kuma suka bi yan bukin da ake saukewa mota mota da kallo suka shiga nasu rigan arzikin kuma. Get Asmau ta bude na shiga da motar cikin gida kai tsaye don ko ba niyar kara fita a wajena ranan don mun shige ke