← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 101

Sashe 89

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashina ke nan daga barci na gyara daki na fito in zubar da shara na samu yaran anty zaune kananun suna kallo suna marming din wakan harda rawa uwar na zaune gefe tana kulla taliyanta a leda. Tsawa na daka masu tare da fadin ke jamila yaya akayi baku je islamiya ba yau sai ta kalli uwar naji uwar tace dasu ai saida na fada maku tun dazun ku tashi kuje makaranta yau mummy Aeesha na gida kukaki. Indai baku zuwa islamiya saboda kallo zansa Abbu ya cire kayan kallon nan gaba daya me zaku gane a cikin kallon gara dasu wayan nan da kuke gani sun karbi kudinsu ko. Suna shagalar da mutane ku baku fatan ku samu naku rabon a wajen Allah kun tsaya kuna biyewa wanan shiriritan nasu haka ? Kema anty wallahi da laifinki kina ganin lokaci karatu yayi baki turasu ba don Allah ku bar yin wanan dabi,an hakana mana cutarwane ga yaran nan kikeyi wallahi. Ina tsaye saida naga fitansu gidan uwar harda basu hamsin hamsin waisu kashe a hanya nace oho dai a raina sai sun tafi dai na koma dakina ina mamakin halin ko in kula irin nata a raina. Kamshi na fesa a dakin na shiga wanka bayan na fito na gyara jikina na saka wani dogon riga cotton mai laushi zubin kamfala da gyalenshi dana dora akaina na dan gyara fuskana na kafin na fito falo neman abinda zan ciwa cikina . Don yunwar safiya akawai rikitarwa wani lokacin munyi sa,a akwai wutan Nepa suna falo suna kallo sai Asmau dake girkin rana. Don yanzu itace ta karbeni ga komai tayi sharan gida tayi girki da yan wasu aikace aikace dai samira kuma tayi wanke wanke wani lokaci da girkin dare gidan sai gidan namu ya koma tsab dashi. Asmau data debo min sauran tuwo shimkafa data gyara bata koma wajen girkinta ba ta zauna muna hiran film din da akeyi din . Don ni ba bin shirin nakeyi ba saboda banda lokacin tsayawa kallo yadda sukeyi suna min bayani akan shirin film din Sallama kaji tsakar gidan mu din Allah yasa Ammah na waje lokacin fitowanta ke nan daga daki ta amsawa mai sallaman . Suka gaisa da bakuwar take fadin Aisha take nema don Allah nan Ammah tace a rude wata Aisha wani lokacin idan an kirani da Aisha din takan manta da nice hakana don sun saba da kirana da Aeesha a bakinsu. Asmau ta mike ta leka wajen matar na tsaye har lokacin tare da wata yar yarinya data rike hannunta yarinyar zata kai kimanin shekara bakwai da haihuwa. Wasuke nema ne wai Asmau ta tambaya wai Aishan gidan nan, mummy Aeeshace mana Ammah ke meyasa kike da rudune wai don Allah ? Gata can falo zaune ta fadawa bakuwan hakan kafin kuma tasa min kira da mummy kinyi bakuwa fa hakan yasa mu dukkan lekowa mu ukun dake zaune a falo. Mikewa nayi nafito ina mata sannu da zuwa muka don ban shedata ba amma nace mu shigo falo . Saida muka shiga kafin nacewa yarinyar baby sannun ku da zuwa zo mana na mika mata hannu taki zuwa tana ja baya. Tana zama take fadin baki zuwa wajen takwaran ki maama sunan data kira yarinyar dashi ke nan lokacin, nake fadin ai takwaratace ma ashe zo mana ta kara shigewa jikin matar da suke tare . Muka gaisa taga dai alaman bamu gane taba daidai Asmau nashigo mata da kunnun ayya da zobo gora ukku da ruwan leda masu sayi a dan wani karamin tire data dora a sama. Ina jin dadin hakan da sukeyi gaskiya yan sokoto sun iya mutunta bako da karramashi gaskiya sun san daraja da kimar bako a idonsu sosai wallahi. Baki ganeni bako ta fada na danyi murmushi nace gaskiya tace tare muke da S matazun ni kanwarshi ce tare mukazo dashi ai Nace lah ikon Allah ashe gaskiya yake zaku zo tare na dauka wallahi zolayata yakeyi ai na fada cikin yar fara,ata a fuskana gareta. A,a ba wasa bane ni nace zan biyoshi nazo naga sabuwar antyna da muka samu don yaya na din yana ta magana ya samu wata a kano . Kara gaisawa mukayi nayi mata yaya hanya ya mutanen gida kuma kafin tace dani ai tare muke dasu suna waje shida kanin mu da abokinsa. Murmushi nayi ina fadin kai wanan yayan naki sai a barshi ai at list ka bugo waya daj ka sanarwa mutane tasowan ku dai ? Barin naje na tarosu a wajen kisha ruwa kafin na dawo don Allah kafin na dawo samira ki kulamin da ita na fada ina mikewa tsaye ta bini da satar kallo takalma na nasaka na gyara gyalen kaina na dan kara bajeshi na nufi hanyar fita wajen. Da Asmau na fara hadu tana fadin mummy na rigaki ganinsa ashema ba wani babba bane sosai ni yanzu ban san ya zanyi dasu ba wallahi Asmau saika kwaso mutane haka kazo min ba sanarwa don Allah. Sai naji tace name mummy nace abinci da inda zan kaisu su zauna mana tace su hudune fa da wanan macen . Indon Abincine baki da matsala don na kammala shikafa da miya nayi yau da kassan ragon da Abbu ya sayo jiya sai ganyen salad shina aiki yaro ya sayo min yanzu. Wurin zama kuma sai a gyara falo mana su shigo ciki su zauna anan je ki fadawa Ammah to ita bakuwar kuma ko dakina sai akaita can ta zauna. Hakama yayi ta fada na dafata ina murmushi na nufi hanyar fita gidan kai tsaye don kada suga an barsu waje tsaye nasan halinsa da saurin hasala. Ina fita kuwa tsaye na hangonsu sun jingina a jiki motarsu dukkansu su duka ukkun suna tsaye suna magana tare da facing din gidan namu na karasa fitowa cikin takona mai kama da yanga da izza irin nawa. Tun kan na kawo naga fara,an jin dadi a fuskansa gashi gaba daya sun zubo min idannuwansu a kaina kowansu na kare min kallo kwam don koshi ganina na farko ke nan da yayi da rana kiri kiri irin haka sosai. Don wancan ranan ganin dare tayi min ba zai karar da zahirin yadda yagani a yanzu ba. Idanuwana masu kamar an diga masu ruwan zinare da digo farin madara daga tsakiyansu na dubesu ina murmushi nake fadin sannunku da zuwa. Ya hanya cikin murmushi ya su hjyn mu da sauran yan uwa don haka nake jin yake kiran mahaifiyarsa da hjyn mu . Saboda na fahinci akwai matukar shakuwa a tsakanin su sosai hakama yan uwasa da nake yawan jinsu a bakinsa. Don bai magana daya biyu sai yace hjyn mu tace kaza ko sister na maimuna ko Nusaiba tace hakan yasa na nuna nima ina kaunan su lokacin. Ance idan kana son mutum ya kara sonka a ransa ka so abu mafi soyuwa dayafi kauna a duniya kaima ka kaunaci wanan abin sai tafiyan ku yazo daidai. Ya amsa min a cikin wata kasalaliyar murya data rufeshi a lokaci guda wanda bansan dalilin rikicewan nasa ba a lokacinnaji yana fadin. Hanya Alhamdullahi babyna su hjy duk lafiya sunce a gaisheki tace na fada maki sai sunzo suma murmushi nayi kawai don nasan ya fada ne kawai. Lokacin na juya wajen bokan tafiyan daya zo tare dasu suma ina gaidasu da hanya suka amsa cikin kulawa da jin dadin ganina a lokacin. Kafin in juyo in samu yana min wani irin kallo duk da mun taba haduwa yau kallon nasa na daban ne a gareni nima murmushin na sakar masa lokaci guda kafin na dukar da kaina kasa. Yace yau naga kinfi min wancan ranan kyau sosai babyna ashe karamar yarinyace ke sosai ranan kallon tsoro nayi maki ke nan shekarunki baikai yadda na dauka kin kai ba ke nan ? Da sauri na dago na dan kalleshi kafin na sanya hannayena ina gyara rufe fuskana da gyalen dake kaina ina murmushi nace nice yarinya kuma matazun ? Yes iam telling you ba zaki wuce sa,an last born ba gashi ya nuna min kanin nasa na kwashe da dan dariyan daya fito min da fararen hakorana na yarinta dake jere ras a bakina ina fadin sorry Gaku a waje tsaye mana amma shine kuma baka kara sanar dani zuwan kuba Allah na dauka wasa kake ba zakuzo ba a yau kadai fadane kawai . Yace wai har yaushe zaki daukeni da muhinmaci a zuciyar kine babyna naga kamar ni nafi damuwa dake wallahi kamar sam da wasa kika dauki zancena a gareki ? A hankali abokin nasa yaja kanin nasu suka koma dayan gefen cikin dan takawa suka bar muna wajen jin abokin nasa na batun sakin layi gaban kaninsa don saukin soyayya. Aisha tun ranan da nayi arba dake a wajen bukin Nadabo idanuwana da zuciyata sukayi matukar makancewa da kaunarki har sai yaushe zanji kin fara nuna min irin kaunar da nake ji naki a rayuwata daga bakin ki ? Murmushi na kara sakar masa ina gyara tsayuwata nace yanzun duk wanan baso bane kazo nafito yaya kake son nayi kuma matazun na karasa a tsigar shagwaba cikin langabe kaina kalar tausayi? No ba haka nake nufi ba sai ina gani kamar ke din wata allurace a cikin ruwa sai rabo da kaifin ido ga wanda Allah yabawa sa,a mutum zai iya mallakar ki Aisha a matsayin mata kamar yadda nake fata hakan gareni. Muryan Asmau ce ya katse mu tafito tana fadin sannunku da zuwa daddy sannu da zuwa yaya hanya da mutanen gida ku shigo daga ciki takarasa a karshe? Au daughter dina ce ashe mun sameku lafiya ya fada shima kafin ya ce ai nan ma ya isa nake gani ba sai mun shiga daga ciki ba tukun da saura wata ran zan shigo insha Allah. Haba dai ku tsaya a waje haka kowa na kallon ku Allah ku shigo daga ciki inji Ammah ta kara fadan hakan gareshi. Sai naga ya dan juya gun abokan tafiyan shi suma sunji metake fada a lokacin don haka dariya sukai mashi da sauri yace. Look daughter next time idan mun dawo zamu shiga akwai inda zamu yanzu amma ga wanan ki shigawa mummy dinki dashi ciki hjy ce ta
Chapter 89 · 0% Book details