← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 101

Sashe 16

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

nan amma kin bi kin damu kanki kin tsiro da wasu halaiya na daban a yanzu akan abinda bashi bane gareki. Yau dai nasan duk abinda wani zai fada maki a duniyan nan mukace dake ga gaskiya dole ki yarda da hakan a kanki don shine gaskiyan gareki. Don ba zamu fada maki abinda zai dawo ya cutawa rayuwanki ba daga baya muma ya cutar damu don muke tare dake ako wani lokaci. Kuka na dan farayi naji ta sake min tsaya tana fadin ba kuka na zaunar dake nan ki mun ba kiranki nayi inji waya fada maki wani labari a game damu ko ke ? Kaina girgiza mata a lokaci alaman ba komai a rayuwana saidai ina mai jin wani iri kasan zuciyana kamar in kashe kaina don bakin ciki. Nake ji a lokacin abinda yasani dagowa shine muryan Ammah din dake fadin duk da kin kasa tambayana labarin da kikewa bakin cikin kike wanan rama to ni nan nasan kin sani. Saidai ina kwankwanton a inda kikaji wanan labarin shine ya daure min kai a yanzu ba wani abuba so nike insan me aka fada maki game da mahaifiyar ki ? Da alaman tsoro a fuskana na dago ina kallonta sai kuma na dukar da kai ina tunane tsokin takaici naji taja tana fadin. Ga kayan can da taba wani bawan Allah tare da kudade masu yawa ya kawo maki har damu don haka sai ki tashi ki duba idan zaki iya don naga kin sakawa zuciyar ki abinda bashi ba a yanzu. Kaina girgiza nace ko tsinke bana so Ammah abawa wanda duk ya dace nagode ai bankai karshe ba naji saukan hannun Ammah a fuskana saida naje tangal tangal daga zaunen da nake don zafi. Fada ta fara tana fadin ni zaki kawowa diban albarka Aeesha sakaiyar da zaki min ke nan a yanzu ace na hinjiraki ban maki rikon gaskiya na tsakani da Allah ba. Idan Nana da mahaifinki sun maki laifi da farko idan kin kula yanzu ita Nana kokarin take ta burgeki ai taga ta wanke maki zuciyar ki. Ina laifinta ga hakan tunda duk wani abu donko take turoshi a garemu saboda rayuwanki ya inganta ai kada ki dauke mu bamu san abinda mukeyi ba mana. Ko duniya Nana ta mallaka a yanzu wanan bai tsone min ido ko in kalla balle raina ya biya da ace aikin banza takeyi a can mutumin nan saida ya rantse muna kamar yadda itama ta rantse masa da aure ta daura a can din bayan ta koma saudiyan. Don haka ki shiga taitaoyin ki dani kafin ranki ya baci kada ki dauko min wani surfa banza ki dagwala min lissafi dashi yanzu kuma. Sautin kukanane ya karu a lokacin akan nace ban karban kayan da Nana ta turo muna Ammah ke min wanan fadan da baida tushe haka har duka abinda bata taba min a rayuwana ba tunda na tashi. Gyaran muryan Abbu alaman zai shigo gidan a lokacin yana sanar muna hakan baisa na rage sautin kukan da nakeyi ba wiwi ina jan majina ta hanci don zuciya daya kawo min. Tundaga kofan gida yake fadin wai yayane meke faruwa hakane wai daga Ammah har ni ba wanda yai masa magana a lokacin. Sai ya cigaba da fadin tambaya fa nakeyi anyi shiru meya kawo haka kuma yanzu Ammamatan ya juya kanta ya kureta da ido yana son jin amsa . Haba malam kamar Aeesha zata zauna tana gardama dani yau don wani ya rutsata ya fada mata maganan daba shiba ta dauka tana kokarin rainawa mutane wayau. Juyawa yayi gareni saida ya kare min kallo a cikin tausayi yace haba Ammah kibi yarinyar nan sannu mana don Allah yau ko me tayi tayisane akan kurciya da dacin rai. Don ko an tabata dole tayi hakan ina hakkurin ki ya shiga da zaki biyewa yarinya kuna saida hali a cikin shiya muryan kukanta har waje na tsinkayoshi. Ai dole in biye mata malam da wani yarinyar nan ke son inji a yanzu da nata iya shegen da takeyi yanzu ko da wanda muke fama dashi kan rashin yar uwarmu. Duk yadda take ji mumafa muna jinsa a yanzu aiko inga dubaiya ban cancaci hakan a gareta ba a yanzu me muka rage yarinyat nan dashi don Allah malam a yanzu ? Umm,ummm Ammamatan ki duba lamarin nan ki auna shekaru ba daya bafa yau ace kaine hakan ya rutsa dakai ko babban kanka ke ya zakaji abin don Allah. Shi yaro a sannu ake fahintar dashi ya gane bada garaje ba irin hakan ya juyo gareni yana fadin ke nana rufe min bakin ki a yanzu idan kina son muyi magana a tsanake dake ko kuma in fasa hakan inyi fushi nima in baki baya in fita a zanceb in barki da Ammamata din kuyi tayi. Jin abinda Abbu din ya fada yasa na sassauta kukan nawa sannu a hankali yana ganin hakan ya juya ya fice daga gidan ban jima ba na mike na shige daki na barta a wajen cikin bina da kallo. Ya dan jima bai shigo ba sai can naji shigowansa yana rufe gida kafin kuma naji muryansa a kofana yana kwala ma sunana kira da ke nana fito ki karba nan . Jin hakan yasa na fito daga dakin ya bini da kallo kafin yace ungu jeki randa ki debi ruwa ki daureye fuska da baki kizo ki zauna kici. Na koshi na fada a sanyayye wani tsawa ya buga min da yasa na nufi sashen randan ruwab namu da sauri ina diban ruwan . Zama yayi saman shimfidan da yayi a tsakat gida kodana dawo gefensa ya nuna min yana fadin zauna nan a kusa dani . Ba mussu nakai zaune kamar yadda yace din ya miko min leda da tun kan in bude nasan meye a cikin ledan don kamshin dake fita a cikin takardan ga kuma nutrients milk mai sanyi har guda biyu. Bayan na karbane ya fara kwalawa Ammah kira itama ta fito ya mika mata ledan yana fadin karbi bude muna nan ya mika mata itama zama tayi cikin damuwa tana bude ledan daya miko mata din a lokacin. Dan juyowa yayi yana sauke min kallo tare da fadin bissimillah mana Nana nakine wanan gani nayi yau rayukanku sun baci bakuci abinci ba zaku kwana da yunwa daga karshe hakan ya zamo maku matsala. Maza ki bude ki somaci kikuma saurari abinda zan fada a yanzu ina son kowa ya bani kunnuwansa ya saurari abinda zan fada a yanzu wurin nan. Don zancene da zanyi a matsayina na uba kuma maigida a gidansa don haka kai tsaye umurni zanba ko wani ku a nan ko kuma doka a gidana don haka ina son kowan ku ya ban hankalinsa yanzu ya saurareni. Ke Nana dake zan fara don haka ina son ki saurara kiji abinda zan fada a yanzu a kanki don a yanzu kece wace kika saura da wanan zance kuma idan kinyi hakan ba laifi bane don kinyi a wajen kowa. Ko ita uwarki gata zaune bacin raine da damuwa ya saka tayi maki wanan boren a yanzu amma ba don taso hakan a gareki ba.
Chapter 16 · 0% Book details