Sashe 45
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shiga gidan akwai yake hannun farida sai da zan shigo gida ta mika minshi. Bude wayar nayi sai ga soko nagani na bankina na bude sakon daga MB kamar yadda nayi serving din sunansa nagani ya turo min da kudi daidai adadin yawan abinda na kashe a jiya din wajen electronic din da muka sayo. Mamakine ya kasheni da sauri na duba massage dinsa ya rubuto ba nauyiki bane yin hakan nauyin bawan Allah nan ne duk wani jindadin ku a yanzu wanan nauyinane ga kudinki nan na dawo maki dashi da sauran abinda na manta nayi maki na rayuwa. Shine na rubuta masa why MB zakayi min haka kada ka manta ni yar tallakace kada ka saba min da dadin da ba zan juri gushewansa ba fa ? Dadi kin kama jinsa ke nan a rayuwanki tunda kina tare da MB a yanzu sai kince yayi maki yawa zan daina. Kada kasa iyayyenka suyi kuka dani a yanzu fa kan hakan suce ina kwashewa dansu kudi ina kaiwa gidan mu mb yana ciyar damu da komai nasa. Ki sani MB ki ba rago bane daya dogara ga a bin iyayyensa nashi yake nema ta hanyar halakan irin ku dubu Mb zai iya kula dasu yarinya a yanzu. Niba kudi ko kyalkyal banza nake son gani ba mb nake son gani gaba da gaba naga halinda yake ciki a idanuwana . Karki damu da hakan gone Auwal zai kawoki nan har wajen mb sai ki shirya haduwa da mb din shine na mayar masa da amsa da yasashi dariya har salman din ya fahinci dani yake online a lokacin. Wanan ya kawo badakala a tsakaninsu har mami ta shigo ta samresu saidai bata fahinci kan musayar bakimsu ba lokacin harshi salman din ya fita Babu komai a zuciyana ranan sai farin ciki kusan duk wanda ke gidan mu ranan da abinda ke cikin zuciyarshi a lokacin musan man nida iyayyena da abin ya shafa kowa da abindake yawo a zuciyarsa. Ni dai a bangarena ina ganin nayi dace a lokacin don ba kowace mace bace zatayi sa,an dace irin wanda nayi na haduwa da MB a lokacin. Sai har na kasa hango matsalan dake akwai a tsakaninmu wanda zai iya haifar mana da matsalolin da ba a so masu muni daga baya saboda idona ya rufe a lokacin na fada tarkon soyayya lokaci guda nake ganin ba abinda zai iya kawo muna tsaiko a rayuwa. Yayin da Abbu da Ammah su kuma da zullumin hakan suka kwana don sunsan yana da wuya iyayyen Man Bashir su yarda da auren mu ba tare da sunsan waye takamaimai din mahaifina ba. Abu daine idan rabon mutum ya ratsa a jikinka sai kaci rabonka don haka wanan abubuwan da yake min a yanzu yana yin sune akan rabonane naci dani dasu daga gareshi kawai. Don sun dade a daren jiya suna tataunawa a tsakaninsu karshe dai sukai min adduan fatan alheri da samun sauki a rayuwa na mafita mai kyau. Washegari kan ban fadawa kowa komai ba na shirya tsab da zuman fita school amma a zahiri kwaliyan zuwa wajen MB nayi in dubashi idan mun fito break kafin mu koma Auwal zaizo ya kaini ingaidashi. Anty safiya kasa daurewa tayi saida tayi magana nace kinsan yau Monday ce anty ko bature yana girmama ranan ai. Yan aji dai sai satan kallona sukeyi ban kula kowa ba ina Allah Allah lokaci yayi in ware saima naga lokacin yai tsawo a ranan daya da wani Abu kuwa Auwal yazo ya daukeni shima sai sheri yake min bandaiyi magana ba na kyaleshi. Komai na jikina marching color ne shigar ya tafi daidai nasan gidan wancan zuwan da mukayi in group da sauran course mate dina don haka wanan karon ban tsaya mamakin mansion din ba saboda nayi a wacan karon da mukazo a cikin taro. Saidai motocin da muka ganine a haraban gidan yasa Auwal fadin akwai baki a gidan bari na kirashi muji saidai yayi kira bai dauka ba yasa yace mu shiga kawai ciki kai tsaye. Wani hanya muka bi ba wancan da muka shiga wacan karon ba wanan ta baya yake wajen lanbunsu muka bi. Sai gamu a katon falon dayake mallakinsa . Falon daya sha kayan alatun zamani iri iri farare kal dasu ga kayan motsa jikinsa nan a gefe daya zube . Yana bude kofan ya tura dariyansune ya shiga kunnuwan mu a lokacin yayin da su kuma suka juyo lokaci guda garemu. Kasa hade dariyan dake fuskansa a lokacin yayi yana mai zubo muna idanusa yana bin mu da kallon a cikin mamaki fuskansa daya baiyana karara a lokacin. Sannu a hankali duk suka juyo suna sauke kallonsu a kan mu suma don suga meya dauke masa hankali haka har ya sake kafan daya hana mami tabawa a lokacin. Inda nima kallon kafan nasa nakeyi cikin tashin hankali don ban dauka har ciwon yakai haka ba ashe ban damu da duban ko suwaye tare dashi ba a lokacin ga damuwa karara a fuskata dana nuna lokaci guda ina bin kafar tasa da kallo. Sai mahaifin nasane yace ku karaso daga ciki mana sannu ku da zuwa Aeesha ko dalibar man bashir ashe kin samu labarin abinda ya samesa ? Lokacin naga matan dake falon tare dash cikin shiga ta alfarma duk sun sake kalloni da yar kunya na karasa dan takowa saidai har lokacin banyi nisa da kofan shigowan ba don girshin da mukai masu. Au ko itace yar kwara din tasa data dauke masa hankali take kokarin hanasa yi muna biyyaya a,a lalai ? Lokacin na dago ido daga kallon kafan nasa dana shagala dayi tun shigowan mu na sauke kan wace ke magana din bakace yar karfafa da ita ga kuma alaman hutu ya nuna a jikinta. Amma hakan bai hana aga bakinta na asali daya baiyana ba a jikinta duk da gyaran da jikin ke samu na gata. Dan tattara natsuwana nayi na fara gaidasu ina fadin ina wunin ku ya mai jiki kuma cikin jin kunya tare da girmamawa ? Jiki Alhamdullahi ai da sauki gashima ana daga dashi ya taka yanzu yana shagwaba abu ga dan dangi dan asali. Au ko kece Aeesha da nake jin labarinki a wajensu lalai tubarkallah masha Allah, ashe kuna tafe kin samu labarin gwarzon naki ba lafiya ke nan umman salman dake gefen kafadan shi zaune take fada na dan fadada murmushi nace jiya nake jin abinda ya faru cikin sanyin murya. Karaso ciki mana ku zauna Auwal ka tsaya da ita daga kofa kuma tana nuna muna kujeran da ba kowa a sama dake gefe daya. Wai hjy hafsat dama haka kuke barin ko wani banza na shigowa gidan yadda sukaga dama ko wani lokaci babu kwabo ko security a kansa? Dayan matan da tunda muka shigo batayi magana ba sai bina da kallon banza tana watsarwa da takeyi run shigowan mu. Wanan dai da gani kin san barbaran yanyayawace ba tarbiya garesu ba hjy kubura irin yayan nan ne na tsaraban saudiya saiko dai idan ubantane ya auro yar gantalin Arab yazo da ita oho ? Dayan tace kinsan maza da son farar mace wanan inba fari ba meya gani a wajenta shi zamanta kwara din ne ya baka sha,awa kome ? Dadin abin dai dan asali sai yar asali ko mutum yaki kuwa don mu da asali muke ado ka rike wanan kalman tawa ka aje. Ta fada tana mikewa wanan dai matar dake magana a gadarance ta sake fadan hakan ta mike tsaye tana gyara gyalen jikinta. Har zan kai zaune saina fasa da sauri ina mikewa sai naji umman salman na fadin haba dai da girmanki kuma kike wanan abin gaban yarinya karama hjy kura. Nan daddysa ya dauka da fadin no bansan yaushe zakuyi girma da wanan halin naku na nunawa dan adam Shiba komai bane. Common, come here, naji ya fada ba kuma kunyan hakan a gabansu yasa na danyi kasa da kaina lokaci guda son kunya. Come closer, come and have you sit here ya sake fada wanan karon tare da dan dagowa yana nuns alaman dani take tare da nuna min wajen da mahaifiyarsa itama ta mike daga zaunen da take gabanshi saman Stoll. Gashi ya tsureni da idonsa akaina alaman dai dani yake a lokacin kan in taho inda ya nuns min in zauna. Kije Auwal ya rada min hakan yasa nabi umurninsa na taka zuwa garesa din na zauna a Inda ya nuna min ba tsoron komai a zuciyana lokacin. She is my girl friend and this my aunt's ya nuna min su da hannu sai hjy my lovely umma and my mami too you already know Dad before na dan gyada kai alaman eeh sai kuma ya juya wajen umma din yana fadin. Hjy wanan ce Aeesha daliban da tafi kowa hazaka a fanin mu kuma nake ji da it'a sosai a ,,,,,,, Kai dakata da wanan iya shegen naka na banza kaji ni da kyau ke ki jini da kyau in kina jin hausa in kuma sai turanci ko larabci ki samu wanda zai fassara maki hakan. Wanan da kike gani ke ba hadin kifi da kaska don yafi karfin ki wanan maimakon taga fushi a fuskana sai murmushi na sake cikin karfin hali a fuskata. A cikin harshen larabacin dana matsa kaina na koya don bacin rana irin wanan tun ina karama na koyi larabci kuma na iya. Umma since take magana tace na dauka duk abinda suke min a wasane don haka kada in damu dasu na gyada mata kai da na,am. Sai naji suka mike fice da ita da mami din nasa ganin abinda yan uwan mijinta ke shirin aikatawa a lokacin. Suna fita naji daddy din yayi wata tsawa tare da fadin hjy Amina bazan dauki cin zarafin kowa a gidana ba Damage nasani ai yaya da saninka make komai dake faruwa ta juya ta fita tana sababi tana aibantani haka yar uwar ta watsa min kallon tsana itama ta fice daga falon. Sai lokacin na kula da wanan hindatun da suke zaune ashe falon sums kamar basu cikin falon a lokacin . Naji mamaki kwarai yadda yayi mata tsawa ta fice da sauri tare da yar uwar ta lokaci guda