Sashe 37
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda muka tashi sallah ban koma na kwanta ba ina waje ina rage yan aiyukan gida kamar yadda na saba yi duk safe irin shara wanke wanke da hasawa Ammah wuta. Sai bayan nagamane na debi ruwa nayi wankana can ban dawo daki ba bayan nafito na kara gyara wutan na nufi dakina na samu Aimana da ta koma cool tana kokarin saka wasu tufafi a jikinta a lokacin. Jakata na jawo na dauko maina na fara shafawa katon rubane da aka hadashi da yayan itatuna na asali mai suna naturalseness . Yana cikin manda Kharat ta zabo min bai kara haske saidai jiki ya kara sumul fata na asali ya murje ya kara baiya ga mutum shine aikinsa ga kamshin diyan iccen da aka hadashi yana tashi sosai don a take ya hade dakin lokaci guda. Brezyer na saka sai dan short tiet da pant fuska na tsaya gyarawa lokacin Aimana dake nuna tana fushi dani na ba gyara ba dalili a yan kwanakin nan naji muryanta tana fadin Aeesha ni zan tafi. Ashe ta fadi hakan ne a gareni don in juyo inga shiganta a lokacin sai kuma aka samu akasi ban juyo din ba na dai ce da ita ki bari Auwal yazo ya sauke mu mana. Ta maimaita sunan Auwal nace eeh har lokacin ban juyo na kalleta ba a zatona zatayi gardama ta wuce sai gashi naga ta koma ta zauna tana wani tsabga kuma. A tsanake nake shirina tsab already kayan da zan saka dama suna fili na ajesu wani charculet less ne dinkin remade bubu da akabi da stone shina saka na dan lakato oud na murza ga gyale da dan kwali kafin in tsaya daura dan kwalin da baso nakeyi ba amma idan na daura zakice na koyi daurine dama a wani wajen koyon daurin. Takalma na jawo half cover da dan jakar hadasu har inda nake naji sautin ajiyan zuciyarta a kunnuwana hakan yasa na juyo lokaci guda ina kallonta. Wani iron kaduwa da razana nagani a fuskanta lokaci guda kamar ma ta manta a zaune take lokacin data ja baya kadan tana gyara zamanta. Karamin dan kunne na manna a kunnuwana lokaci wayata ta dauki kara nasan Auwalne ya iso ke nan nace da ita muje ko ? Ta mike kamar zonbi muka gyaro komai muka fito saidana tsaya wajen Ammah dake bakin murhu mukai magana kafin in mata sai mun dawo muka tafi. Zaune muka sameshi wurin Abbu suna hira shida Abbu dake zaune yana jan tasbaha a hannubsa na zagaya zuwa wajen Abbu na tsuguna ina gaidashi da kwana tare da fadin zan tafi Abbu. Nanata har an fito to akula da kai da mutunci kinji Allah ya tsare muna ku yana magana yana kokarin ciro dan kudin daya saba aje min duk safe ya miko min. Kaina kada nace a,a Abbu yanzu kuma in ban taimaka maka ba ba zan karbi naka ba kuma Allah ya rufa wanan asirin cikin hikimarsa ya kawo muna sauki a saukake. Hakane tabbas Nanata Allah ya kara tsare muna ku dama ance garin kwarai baya ruwa wajen damashi balle ya sake ki dai rike Allah da Annabinsa a zuciyarki kiga fiye da hakan a rayuwanki. Aimana dake tsaye ta daskare tana kallon motar da Auwal Awilo ya bude yana dan gogewa saida Abbu yace Aimana yaya wajen su baban naki kuma ta juyo tana sauke ajiyan zuciya tace suna gaidaku Abbu. Muka mike kafin ma mu iso Auwal din ya nude baya inda zan zauna ya kallota yace ke zauna gaba ko kibar hjyn mu a baya ita kadai. Hakan tayi nidai ce mai nayi Auwal sister dinace fa don Baku taba haduwa bane gidan mu daya dakin mu daya da ita itama a nan Jami,a take karatu ai. Oh ita wanan din amma gaskiya ba za ace ba don ba hadin kifi da kaska ko daya tsuki taja tana kawar da kai sai lokacin nace indai Auwalne ki gani ai Aimana wanan sarkin barkwancin. Ai hjyta in fada maki jiya ogana ya dawo kinsan me a cikin daren nan ya saida ya tambayeni ke wallahi duk da gajiyan daya debo kuwa. Duo hiran da mukeyi Aimana tana can ta lula a cikin duniyan tunane ba jin mu takeyi ba a lokacin don ita abinda take gani kamar a mafakine yake zo mata. Ita da tayo dinke dinken da zata razanani sai gashi nina zaranata a karshe bayan hakan kuma wai har mai kaini school ke gareni yanzu cikin wanan uban motan mai bala,in kyau. To wanan da taji ina kira Auwal shine saurayin nawa ko kuma wanine can na samu mai kudin da shine mafalkinta koda tsohone ko mumuna. Tsab ya shirya ya fito yana kallon lokaci jikin agogon fake daure a hannusa kofa yaji an turo ko bai dubaba yasan salman ne don shi kadaine wanda ke shigo masa daki haka kai tsaye ko wani lokaci yaga dama. Saidai muryan mami dinsune yaji sabanin na salman din da yake saka ranji a lokacin tana fadin dama nasan zaka iya fita da safen nan bamu gaisa ba dakai. Yasa na hana idona barcin safe yau don in ganka tunda kai baka damu damu ba a yanzu sai kai ficewanka ba tare da mun gaisa ba . Dan murmushi ya saki yana fadin mami ba haka bane wallahi koda nake fita lokacin baku tashi daga barci ba haka kuma in nace zan kara lokaci sai in makara. Tsuki taja tana zama race na rasa dadin me kakeji a wanan koyarwan da kasa kanka a yanzu wallahi me zaka tsunta a rayuwanka cikin koyarwan kasan nan magaji ? Kai ya dago yana murmushi kafin yace mami ba zaki gane bane ko nayi maki bayani amma ai kinsan bawai koyarwan bace manufata dole akwai dalilin hakan gareni. Kwarai kuwa ina zan gane kuwa magaji tunda yar kwara din da ta dauke maka hankali har kake son muzanta yar uwarka tana wajen inako zan gane komai a yanzu. Cikin mamaki ya maimaita sunan yar kwara din da Mamin ta fada yace wacece hakan kuma mami ban fahinceki bane fa ? Ina kuwa zaka fahinceni tunda kana son dauko min magana wajen hjy dake ganin nice ummul,aba,isin daurema gindi kakeyin komai. Saidai ka sani shi sure wani lokaci akan yisane don't nasaba ko asali ba wai abinda zuciya ta nace was so ba karka manta da gidan da kafito shine fadakarwana a gareka. Yau koda yarinyar nan yar wani hamshakine ko wani kusan gwaunati idan ita din ba jinin sarauta bace hakan ya zamo ragage a cikin family din nan . Duk da naga mahaifinku ya kamama ya hana ayi ma magana toni dolene in tunasar dakai hakan magaji son abinda ka iya ye ya komo gareka wata rana. Idan har kana son kanka da arziki kayi biyayya ga hjy ku shirya da yarinyar nan da tace zabitace gareka ka zauna lafiya kamar kowa da ita. Sai lokacin ya gane inda zancen Mami din nasa ya dosa akan hjy mai isa take magana da Hindu watau ke nan har yanzu suna nan kan bakarsu na sai ya auri Hindu din shida ba zancen aure yanzu a zuciyarsa. Wanan tsohuwar bata sanni bane wallahi dare guda zan turo a sace min ita in koya mata hankalin da gobe bata kara shiga min hanci ko wani yace tayi hakan gareni. Don't dare try that noses in your life don nasan ba hankali gareka ba zaka iya nan ba turai bane kada ka jawo muna la,anta don Allah a wajen mutane. To ku fada mata ta fita harkata wallahi tunda ba haihuwana tayi ba tsohuwar nan ta fara isata a rayuwa wallahi why zata sani a ido hakane ? Ido uwar ta rufe ta haushi da fada sosai don kada ya dauko masu magana saboda sanin halinsa da tayi sam baida dabi,um malam bashe a rayuwansa sai ya aikata abinda ya fada din yaja masu zagi a banza wajen yan uwa. Haka salman ya samesa rai bace saidai baiyi magana ba don yasan shigowan Mami din ne sanadin hakan daya samu dan uwar nasa din. Har suka kai school baiyi maganan komai da kowa ba duk kwarin gwiwan days dawo dashi sai yaji komai ya tsaya masa cak mami ta dagula mashi lissafinsa. Kan son sai yabi umurnin hjy don kawai a zauna lafiya akan me zai bi ra,ayin abinda baiso bai kauna a rayuwansa shi don kawai wasu suji dadi zai batawa kansa lokacinsa a banza. Tunda Salman ya fahinci hakan baiyi kokarin yi masa maganan komai a lokacin ba don hakama ya fice ya barshi office din don ya dan sarara shi kadai. Baka jin komai a office din sai karan na,Iran sanyaya waje dake aiki sai kuma na fridge dake nasa aiki saiki dauka ba kowa a office din lokacin. Murda kofan nayi na shigo office din cikin mamaki duk da banji alaman wani a ciki ba haka kuma yasa nake mamakin fitarsu subar kofansu a bude ranan don koda wasa basa hakan tsakaninsu saboda muhinmancin kayan dake cikin office din. Hangosa nayi ya kifa kansa saman table din kamar yana barci a wajen yasa na dan Dade tsaye ina kurawa sumar kanshi idanu dake sheki tsakiya yayi dan wani round dashi ya kwanta mai gwanin sha,awa kamar anzana mai su hakan. Saida na kare masa kallo na dan lokaci na juya ina kokarin fita daga office din lokacin naji muryan shi kasa kasa yana fadin come here. Tare da dagowa daga yadda taken yana bina da wani irin kallo kamar ranan ya fara ganina a duniya kasa nayi da kaina da sauri ina fadin sannu da dawowa. Is that the way da zakiyi welcoming dina haka kerere dake come and have your seat ya fada tare da dora takardan dake hannusa saman table din. Na turo baki ina zagayo ga kujeran dake kusa dashi na zauna idona saman takardan daya aje din a lokacin wanda heading din takardan an rubuta in vestige on MADINA SALIU. Takardan da yaga na tsurawa ido kamar ina nazari yakai hannu ya jaye daga gani yana turawa a drawer table din kafin ya dago yana fadin ya karatu ? Dan farrr nayi da gwala gwalan idanuna kafin na nisa