← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 101

Sashe 19

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

da fadin ina zaki da kyat na bude baki ina fadin bayi a takaice. Zaki iya ko in kamaki ta fada cikin kulawa nace cikin karfin hali zan iya Ammah na mike na fita kodana fito na samu ta fito daga dakin ta dauki tsintsiya a hannunta. Alwala na duka na dauro don duban yanayi da nayi ya nuna min an dade da sallah axahar a lokacin hakan yasa cikin karfin hali na daura alwala. Nazo nayi sallolina don tun ina alwala aka kira sallah la,asar duk da yau sauri saurine amma dai nasan lokaci tane yayi don basu muke bi sallah ba a gidan sai hudu daidai muke la,asar. Na dade a zaune ina mika kukana ga sarki Allah wanda yafi kowa sanin dumbin damuwan tattare dani a zuciya wanda ba kowa zai fahinci hakan ba sai wanda kaddaransa yazo daya da nawa din. Don ace baka da uba kasan hakan da girmaka ba karamin tashin hankali bane a wajen mutum saidai Allah ya kyauta kawai. A inda nayi sallah nakai kwance a hankali ina bin dan dakin nawa da ba komai na rayuwa a cikinsa sai dan tsohon katifana da akaiwa cikon ragga gefe daya kuma dan tarkacen ghana most go din kayanane a ciki wanda idan ya lalace nakan fadawa Abbu ya sayo min wani in canza a lokacin. Naso in koma barcin saboda jikin bai sakeni ba amma sai hakan ya gagareni sunayen Allah mai girma na ringa kira don na samu natsuwa a zuciyana a haka barcin ya soma daukana kuma. Saida naji muryan Ammah a kaina tana fadin haba Aeesha duk da ciwone ki dan tashi zaune barcin yamma baida kyau aiga musulmi. Hakan yasa na mike na zauna na jingina da bangon dakin nawa ina faman raraban ido tare da tunane kala kala a zuciyana don ji nake na gudu naje saudiyan ayi wadda za ayi acan din nida Nana idan naje. Amma a take zuciyana ta tambayeni da wani kudi zan tafi din nida banda ko dubun dayan kaina a jikina nake zancen zuwa saudiya a yanzu. Wasa wasa kwana biyu nayi ina fama da wanan zazzabin na karaf daya kuma nasha allurai gareshi na samu na mike kacar majar daga zazzabin. Son gaskiya gun iyayyena na samu kulawa sosai har ina mamakin hakan saidai sanin halinsu na kirki yasa banyi wani shakkun hakan da yawa ba. A dan wanan takin kuma nayi iya bakin kokarina da shawaran da zuciyana ke ban na watsar da zancen Nana da wani mahaifina wanda ma kowa bai sanshi ba a yan uwa. Ya zama dole gareni in rugumi iyayyena dana taso na sani a matsayin iyayyen haihuwana din don sune dai sanyin idanuwana a duniya. Don a duniya sun min komai a rayuwana banga abunda zaisa a yanzu in nuna masu wani halin banza ba in tayar masu da hankali alhalin su basu gujeni a yadda nake ba. Musanman ma Abbu da ban hada komai dashi ba amma ya rikeni riko na fissabillahi in ace ita ammah yar uwatace shiko fa mena hada dashi kuma cikin hakan kuma bai kasa dani ba. Zance Alhamdullahi a dan takin don yawan addua da kuma kulawan iyayyena yasa na daina wanan tunanen na rugumi kaddara a zuciyana duk da dai ba zan taba manta hakan gareni ba a rayuwa. Sai hakan yaiwa iyayyen nawa dadi don sun nuna min hakan zaki samemu zaune da Ammah muna hiran mu ta duniya gwanin ban sha,awa duk da ba fita dai nakeyi ba ta gaji ta saka min ido tunda haka na zabawa rayuwana ta barni. In Abbu yaji tana min fada yakan ce ikon Allah wasu na neman nasu su zauna a gida haka ke Allah ya baki salihar ya kina fada akan fita kuma ? Ammah din kance malam ace ya mace kullum kumshe a gida ina zata samu manema da zasuso aurenta haka ? Yakanyi murmushi yace wata rana kyace nace don sai kin kore a gidan nan hakan bai kan gamsar da Ammah din don takan amsa masa da Allah yasa kawai. Ko jikina ka kalla zaki san hankalina ya kwanta a yanzu don har dan jiki na fara girkawa alaman kwanciyar hankali dai a tare dani din lokacin. Saidai kullum ina a cikin zullumi da tunanen makoma na haka wani abu dake tsaya min a rai shine wanan kudin da nana take turo ma su Amma din akan meye shi ? Ita tasani ni dai ban bukatan komai nasu na iyayyena ya wadatar dani a yanzu nakan fada a zuciyana idan nayi wanan tunanen. Damuwata alokacin jerabawana ya fito yayi kyau in samu zuwa gaba da Abbu yayi min alkawari kullum hiran mu dashi ke nan isan mun zauna. A wata rana naje islamiya nake jin labarin fitowan jerabawan mu din na dawo gida da murna ina fadawa Ammah itama murnan tayi tare da min fatan alheri. Haka yasa na kwana ina addun,a da rokon Allah samun nasara akan jerabawan namu don tsoro daya kamani kuma don jerabawa sa,ace akace ba wai iya kokarin kaba. Banyi sanyi a gwiwa ba washe gari na shirya zuwa duba don an fada min yadda zanyi saukin abin tare da Abbu zamu tafi duba don haka yake da kula akan komai na iyalinshi. Tun shigan mu school din Abbu ya shedawa kansa yadda na kasa damu suke murnan ganina suna fadin ga anty Shu,wa ga anty social don nina rike wanan mukamin saboda tsabata a lokacin. Ba wanan ne a gabana ba sai addua nake faman yi a zuciyana tunda muka tunkari office din examiner da yar fa,asab ya tarbemu yana fadin. Mahaifinki kega nace masa ehh naji yana fadin baba Allah yasa kubar yarku nan taci gaba da karatu don nan gaba insha Allahu akwai alheri idan taci gaba da hakan . Yakai zaune yana zaro wani dogon takarda a gabanshi yana dubawa tare da fadin saidai muce alhamdullahi baba don bana jerabawa yayi kyau gaskiya munyi alfahari sosai da yaran nan. Sunana ya dago yana tambaya na fada masa har lokacin jikina yana dan rawa ya dan tsaya dubawa kafin ya sake dagowa cikin fara,ansa yana fadin Alhamdullahi. Sunanta ya fito a cikin special list baba yanzu zaka biya kudi sai kuje kuyi print out a wancan malamin ya nuna muna inda zamu. Abbu sai hamdallah yakeyi yana samin albarka kafin ya maida kallonsa ga malami yake fadin malam nace ba wai da naso ta danci gabane a karatunta kafin miji ya samu. Shawara nake nema gareka wani makaranta jerabawan nan nata ya dace taje don Allah kasan ba sanin kai nayi ba ni . Baba a cikin fadin kasan nan yanzu wanan jerabawan nata za a iya daukanta a ko ina kuka nema don jerabawa yayi kyau sosai gaskiya. Ehh to ai alhamdullahi amma karin haske nake so dai tunda na fadama ba sanin kai nayi ba nan malam din yace dashi ehh to baba saidai bansan ra,ayinta ba ita yana kallona. Na danyi kasa da kai nace teacher nake son zama Abbu malamin ya kwashe da yar dariya yana fadin irin mu kike son zama ke nan a rayuwa. Hakan ba laifi bane gaskiya amma zan baki shawara da ki dan canza wani ra,ayi ga hakan don jerabawanki gaskiya tayi kyau sosai zaki iya yin litanci ko aikin jarida ko lauya ko dai gasu nan dai da yawa ana neman mata masu kwazo a wanan fannin. Lauya nake so na fada sai naji malamin yana fadin hakan ba laifi bane ya danganta da abinda suka baki dai a can din . Nan Abbu ya kara fadin a inane yace ko nan jami,an gari ai zaki iya zuwa don yanayi bayan haka kuma idan akwai hali akwai sauran jami,oi a sauran jahohin kasan nan haka kuma nan ma makwabtan mu akwaisu yanzu kuje dai can ku karbi sakamakon inyaso daga baya baba zaka iya nemana idan akwai wani taimako da zan maka bayan wanan. Yadda yace haka mukayi din don bamu dawo gida ba saida muka karbo komai a ranan muka dawo gidan namu.
Chapter 19 · 0% Book details