Sashe 40
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abbu ne ya dubi kayan ya girgiza kai yana nisawa yace anya Ammamatan bamuyi sakaci ba duba ga irin zarahin da yaron nan yake kashewa kan yarinyar nan cikin dan kwanakin nan ? Daga abinci zuwa suturun yarinyar nan har ma komai wanan zancen adubane fa kada shedan ya rudemu idon mu yarufe akan abin duniya har yarinyar nan ta fada a halaka ba tare da mun ankara ba. Saukin abin dai da Allah yasa ita Nana akwai natsuwa da sanin ya kamata komai da takeyi bata gaban kanta ta aiwata sai tasa an nemi izinin mu amma ni ina gudun abinda zaije ya dawo kuma nan gaba idan iyayyensa suka sani bayan da mun saba da wanan daulan nasa. Naso ace zancen nan yakai ga iyayye sun sanni sunda abinda ke tsakaninsu a yanzu kada aje a dawo ana kaiwaye ke waye a karshe. Duk da banyi kasa a gwiwa ba saida na binciko nagane shi din jikane na maimartaba sarkin gabas maici yanzu kinga ko yayi wanan yana da zarfin yin haka ba rikici ko wani abin asha yakeyi ba amma . Ina gudun wani abu wanda ba lailai bane kuyi wanan tunanen ku a yanzu ba komai Allah ya shige muna gaba baki dayan my sai ku dauka a raba don ba za barshi ya lalace ba ai. Ammah da tayi zurfi ga tunane lokacin nisawa tayi tana fadin aini malam jikina ya mutu kan zancen nan dakayi yanzu don gaskiya hakan abin dubawane bawai a zauna aita murkusan kayansa ba haka. Yanzu dai ya riga da ya kawo wanan zan gansa muyi magana dashi ta fahinta yadda zai fahinci me muke tunane kan zancen wanan dai a dauka a dibi naci saura Ku gyara ayi amfani dashi gaba kuma tunda ba za a zauna acisa haka kamar abinci ba. Dan tsokan rago hudu na dauka sai cinyar kaza nace ya isheni kayan marmari daine nasha lemu sosai da abarba sai kankanan da anty safiya ta bare ta yanko min. Aimana kan ranan bata runtsa ba haka da safe kiri kiri tace ba zata bimu ba ban dora ba ta tafi Auwal yazo nafito muka tafi ranan kan muna da lectures sosai har dashi ya shigo ajin mu ya bamu darasi saidai bamu hadu ba sai washegari dashi. Nice naje office din god so kind baya nan ya fita lokacin sai security dinsune ya fada min cewa ai sun fita tunda safe wajajen eight yanzu hakane bana yawan ganinsu son basu zama. Said dai a waya zamu kai wani lokaci tare dashi muna hira amma ko hakan ta hanyar charting ba wai ta voice ba zakice bashi bane idan muna charting din amma da zamu hadu da rana sai ya rikide ya koma Man Bashir dinsa na gaskiya. Yakan yawan fada min a wanan lokutan idan muna hira yana mamakin yadda na shigo rayuwansa a lokaci guda abin yakan bashi mamaki yakan fada min. Saidai nayi dariya idan yana wanan zancen don na fahinci hakan saboda dagani har shi ba wait gwanewa kowan mu yayi da iya soyayya ba don alama ya nuna hakan. Alheri kuma ko yaushe cikin yi min yake bai fasa hakan ba gareni ba zato zanga Auwal ya kawo min kyauta daga wajen shi haka ya matsa min saida na bude account acewansa ba a dalibi ba account wata rana alherin gwaunati zai iya wuceni idan an bayar ba account. Hakan yasa naje na bude ranan tare da Auwal dayasa ya rakani ya kuma tsaya min har na kammala na dawo gida shiya kira yana tambaya na fada mai sai cewa yayi in turo mashi account din ya gwada ya gani ko ya fara aiki. Kudi ya turo min masu yawa abinka da dan baka saba ba saida na nunawa Aimana ta yanka ihu tare da fadin amount din kudin ta bini da kallo kafin ta dora da fadin anya Aeesha wanan kuwa yasan abinda yakeyi wanan mahaukacin kudi haka ? Nayi dana sanin nuns mata din da nayi son hassadace karara a tsakani da ita tun lokacin ya karu har yakai a sannu ta kwashe kayanta kaf tabar gidan mu wai ta koma hostels da zama. Nakan yi dariya idan Auwal yace ogansa yace a koya min mota nakance ina yar tallaka ina mota saidai banki ba cikin sati biyu na iya komai yakan ban daga school har zuwa unguwar mu. Yau tun safe dana tashi nake jin raina a bace nayi tunanen rashin Man Bash kasan ne don kwana biyu ina cikin kewarshi sosai da rashin ganinsa . Saidai wani lokaci mukan dan zanta a waya ko hakan jefi jefi ranan dai nake tambayan Auwal don' a yanzu na fahinci shima na hannun damarsane ashe tako kawai sukai min tun farko nida Abbu don' su kusanceni. Auwal din ke fadin hajjaju oga fa babban mutum ne a turai don yanzu haka mutane da yawa suna mamakin kasance warsa nan don abin yana daure masu kai sosai. Yanzu haka yaje buga wani game ne acan zai dawo kuma sai gashi an gayaceshi wasan tseren mota da sukeyi duk shekara wanan yasa ya dakata sai next week zai dawo. Amma fa sirine wanan tsakanina dake don Allah kada ki fadawa kowa zancen nab if not zaiyi fushi dani sosai nace insha Allahu babu maijin zancen a bakina. Saidai a ranan na kwana da mamakin hakan a zuciyana sosai ban yards nayi wanan hiran kuma da wani ba. To na dawo din gida na samu ran Ammah abace ga kuma Abbu a gida duk da nasan lokacin dawowansa baiyi ba idan ba karya zuciyana ta ban ba zan iya cewa har kuka Ammah tayi don idonta ya nuna hakan. Saidai ba wanda yai min bayanin komai daga cikinsu hakan yasa nima shan jinin jikina sai a wajen samira dake kwarmata min abinda ya faru nake jin komai. Wai wasu mata hajiyoyine sukazo gidan namu bayan sun gaisa Ammah ta kawo masu shimfida sun zauna sukace iyayyena suke son gani Ammah ta tura Samira din tazo da Abbu. Amma sukace a,a sufa iyayyena nagaskiya sukazo gani bawai marikana ba koko dama in din yar tsuntuwace banda asali na lekewa dansu don' a bata masu irin gidansu. Nan Abbu yace dash don Allah meya kawosu in cin mutuncine su fita ba gadon hakan a nan sai kashedi sukaiwa Abbu cewa yayiwa shegiyar yarsa tsaraban Arab magana tafita harkan dansu run suna sheda juna dashi . Abbu yace suje su farawa dansu daya lake min kashedi akan ya rabu mashi da ya tunkan ya lalata mata ita ya bata mata suna. Bata dai ban labarin exactly yadda zancen yake ba don tana jin tsoro saboda Abbu yaja masu kunne kan kada wanda ya fada min sai bayan yayi bincike a maganan. Ranan nayi kuka sosai a rayuwata ga wata zuciya na fada min in rabu da Man Bashir kawai shiyafi min alheri da rufin asiri wani bangare kuma na zuciya nace min meyayi maki shi da zaki rabu dashi ? Don ko wani kika samu hakan ne zai faru a karshe tsakanin ku gara kawai ki jira kiji a bakinsa idan shi yace ya hakkura dake sai kiyi hakkuri. Wani lokacin kuma zuciyan nawa na saka min indai kula kowa ga baki daya tunda anyi biyu ke nan haka yaya Suleiman' kiri kiri umma ta raba tsakanin mu ta turashi kaduna wajen yan uwanta an samo mashi aiki a gidan gwaunatinsu yanzu can yake aiki sai a dade bamuyi ways dashi ba. Yanzuma yafi wata biyu bai kirani ba nima ban kirashi ba saidai mutunci ya rage kawai a tsakanin mu dashi na yan uwantaka yanzu. Gidan nasu tunda umma ta dauko yi min wullakanci kan danta na daina shiga sai jefi jefi ko wani Abu kwakwara ke kaini cikinsa a yanzu. Haka na kwana ina jin kamar in kashe kains in huta da wanan rayuwan kaskancin da nake gani wajen jama,a. Yau da ace agidan marayu na taso hakan zai min saukin tozarcin da nake gani wajan jams,a tunda kowa zaisan asalina na gaskiya ba boyo ko sakayawa don za ace yar gidan marayuce kai tsaye. Amma yanzu fa ni inga tozaraci masu rikona sugar tozarci haba dai wanan alhakin ina za a kaishi jamma,a saboda na tabbatar ranan kamar yadda banyi barci ba haka Abbu da Ammah ba zasuyi ba dole zukatansu na a cikin kunci kamar nawa din game da zancen. . Haka yasa washegari na tashi da ciwon kai da Dan zazzabi shiru gidan namu kowa da abinda keci masa zuciyarsa kan zancen. Har ciki Auwal ya shigo yana kwada sallama Asmau ta fito ta gaidashi yace tayi mai magana dani lokacin Abbu da dawowansa daga massalaci me nan yayi mai magana yace bata fito bane ko me ? Daidai lokacin Asmau ta dawo tana fada mashi tace wai ka tafi yau bata zuwa bata jin dadin jikintane. Subbahanallahi don Allah kiyi mata sannu ya fada ya wuce Abbu ya shigo ciki yana tambaya wai Nanata bata da lafiya yanzu nake jin hakan gun Asmau. Lafiyarta dai kalau ina jin yaran nan sun kwarmata mata abinda ya farune tun jiya dama nasan yana da wuya basu fada mataba indai wa yan nan yarane. Baiyi magana ba ya nufi kofan dakin nawa yana kiran sunana bakina yai nauyin amsawa a lokacin dakyat na samu na amsa bayan kira da yayi min yakai uku na fito fuskana kawai ya kalla ya some kansa kasa. Tambaya naji ya jefo min da meyasa ba zaki school ba yau naga yaron nan yazo daukanki kince ya tafi bakya jin dadi. Ban zuwane kawai Abbu yasa nace ya taxi kawai banjin dadi Abbu yace saboda me Nanata nayi kasa da kai cikin hawaye nace saboda INA son rabuwa da Man Bashir ga baki daya Abbu. Ba zan juri iyayyensa ko yan uwansa na zuwa gidan nan suna ciwa iyayyena mutunci ba saboda shi gara kawai na hakkura dashi Abbu. Kaiyya kurciya hoo Nana in kin hakkura dashi damu zaki tabbata a gida sure ko wani urine aisai an samu wanan kalubalin acikinsa dama . Tunda ko mun haifa dole ko mu shanye ko wani irin wullakancin gun mutane dama shine rayuwan idan ba ai hakan ba hausawa sunce aure