Sashe 58
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana nan yadda nasan shi a baya saidai dan murjewan da yanzu yayi ya kara jiki da haske sosai yadda na hango ya zama wani abu yanzu da har mutane ke biye dashi a baya haka. Cikin ladabi a bazata naga su maryam na gaidashi hakan yasa na dauke kaina da sauri zuwa cikin gidan inda mukai karo da wata mace yar bakar mace tana waya a kunyace nace sorry please ta daga hannu alaman ba komai. Nayi mamakin ganin kwana daya amma gidan a cike yake da jama,a fam a lokacin ga manyan tukwane an dora ana motsa yar gwaunati wasu a zaune. Ban tsaya gaida kowa ba kai tsaye dakin yan matan na nufa Asmau na biye dani a baya saidai bamu shiga ba muka tsaya a kofa harsu farida da maryam su karaso. Jefi jefi hiran yan dakin da yan wajen yake shigowa kunne a wajen da muke tsaye din na waje na bayani kan yayan gidanne wance ta haifi wani da wani ai . Na daki kuma ina jin suna gardama kan kudi da angonne zasu basune bansan anty fati na da layina ba sai ga kiranta ya shigo wayana lokacin ganin hakan yasa na leka dakin ina fadin gani a waje anty fati. Wai dama kun shigo ashe ina farida da maryam nace tare muke suna waje mun barsu zasu shigo yanzun nan. Zakice a ranan wasunsu suka fara ganina nida wayar hannuna suke kallo suna tambayan wacece ni ? Naji lokacin da anty Fati din ta juya tana fadin sister din muce diyar brother din babane wanan din wata ta tambaya. Hangosu da nayi tafe yasa nakarasa shiga daga cikin dakin ina gaidasu a jam,i suka karaso amaryan ke fadin maryam kinsan zakuje amsan kudi kuma kun tsaya bata lokaci haka don Allah. Zaune nakai don ba zanje ba kudin ne har sai an wani binsu in suna da niyar bayawa kalloni tayi tana fadin kin zauna mana Aessha kai na gyada ina fadin suje kawai anty su karbo. Yau ga tsiya keba zaki bane nace ban fito da shirin fita ba ai kinga yadda na fito na dauka iyakarmu nan ne ai. Amma dai na fada maku tun jiya ai to dolene saida ita Saratu ta fada dolene ai kinji abinda baba dai ya fada ko to kimatsa tunda fitina kikeso ke . Fitinan me anty tace bata zuwa ba sai mu mutafi ba ku kuke daukanta wata tsiya wallahi har take ganin wani abune ita haka kawai wanda bai fika asali ba zai nanuwa mutum daukan kan banza. Dadin abinda dai yan asalin basu sukace hakan ba ai na fada daga inda nake ta juyo tana fadin me kikace dakin yayi tsit ana jiran jin amsan kowan mu. Nace ke kinyi kadan in sake maimaita abinda na fada dan tsugunnin nan naki dai saratu duk da ta gime min sosai ga haihuwa banjin zan iya bata girman a yanzu. Fitsararace ta gaske wai kamu na zagin koko a yau nace ashe koko yasan asalinsu daya ke munsan diyan sunna da yayan dore fa duk munsan komai ba wani zancen asali a nan kam uba naji shaka a bayana kafin ai haka Asmau takaiwa wace ta kama min kai duga kamar mahaukaciya. Fada sosai Allah ya bamu sa,a mukai masu kaye a wajen ga zaki duk abinda yazo muna a baki mun fada masu ido rufe cikin dan lokaci guda. Lalai yan sokoto bala,i ne kinji iyayyen suka zo ana tambaya take kuma Asmau ta lauye zancen ta zaro ido tana fadin ku koba haka akayi ba ai gara da mummy kowa yasan tana da uba ku da ake tantama akan ku fa ? Abu ga taron mata nan da nan zance ya fara tafiya masu cewa ashe ma ina da ubana tunda ga Asmau ta fada kuma ashe shike min aike akai akai kuma komai dadewa zaku ganshi nan. Uwar gidan rabakaya maman su ya habib ta kiramu tayi muna fada tare da ja muna kunne kan wanan tonon asirin na raba zumunci da mukeyi idan iyayyen mu maza sukaji sai rayukan mu ya baci sosai kafin ta juyo kan mu nida Asmau tana fadin keku Aeesha kada wanan abin ya dakatar dake cikin sha,anin nan ki shigo kuyi komai tare da yan uwanki kada wanan zance yasa kice zaku dauke kafanku badon saratu ko wani kuke gidan nan ba abu dayane ya hadaku a nan din. Nagode mama na fada na mike ina cewa saratu muje zuwa lokacin har anty safiya ta iso gidan cikin tashin hankali saita samu an kashe maganan ko ince ya lafa a lokacin dai. Koda muka koma gida banyi niyar komawa gidan ba amma anty safiya ta matsa min da na shirya muje din dole na tashi nayi wanka. Wurine na kure adaka kowa ka gani yaci kwalliya masu anko kuma sun zuba anko dinsu inda bangaren gidan amarya suke daban na angoma haka. Bamu samu zuwa wajen ba sai da akai nisa da shagali muka shigo daga can baya kadan na samu wuri na zauna nida su Aimana da zuwanta ke nan muka dungumo zuwa wajen bukin ban jima da zama ba akace yan uwan amarya su shigo suyi mata liki. Dole na taso sai lokacin ma wasu suka sanda muna wajen kayan wasu material ne an min dinki mai combination dinkin yayi kyau sosai sai shara sharan hannu daya zuba min inda na daure sumana da ribon daurin dan kwalin dake kaina zaisa ki hango gashin nawa baki wulk da yake walkiya a daure. Tun a mota munyi canji duk da ba kudi masu yawa ba a hannun mu amma sai ki dauka wasu kudine can. Liki mu kaiwa yar uwarmu nafada daji da yan canjin hannun mu muka dawo mc din yana ta wasa mu kowa ya fada masa sunayen mu oho ? Ban saba zuwa irin wanan wajen ba don haka nake jin kaina wani iri hakan yasa na mike na dan taka don barin wajen taron zuwa inda motoci suka faka. Nida samira da maryam da itama tace hayaniya yayi mata yawa a lokacin muka bar Aimana da Asmau tare da farida suna kallon abinda akeyi. Mun karaso wajen wata mota zamu gitta a daidai lokacin waya ta dauki kara na dauko ina duba wanda ke kirana Auwal ne a lokacin. A daidai lokacin kuma wata bakar mota mai kyau ta tsaya gaban mu kadan saidai na ciki basuyi saurin fitowa ba a lokacin. Can kofan motan ya bude ya habib din nan nasune ya fito cikin motan tare da matarshi da yarsu mace yar kimanin shekara uku ko hudu da haihuwa . Haka kawai ganinsu ya sanya kirjina bugawa don rabona dashi tun ina shekara tara ko goma tunda yai min munguntan dana kasa mantawa dashi a raina Kaina kawar gefe daya ina cigaba da waya don har ranan ina jin kamar a ranan yai min wani hikunci cikin muguntan daba zan taba mantawa dashi ba a rayuwata. Akan munyi wasa da ruwan fanfo ya murde min kunne saida nayi zazzabi a lokacin sosai har asibiti aka kaini a lokacin muna tsohon unguwarmu. Tun ranan ban kara yarda mun hadu dashi ba sai gashi a wanan bukin na gidan nasu bayan shekaru mai yawa muna ta hadu dashi wajen shagalin nasu. Niko da bakin riko irin na larabawa ban yarda ko gaisuwa ya hadani dashi ba a yanzu ma dana hangonsu dai din kaina kawar gefe daya ina cigaba wayata. Don sam ban so hakan ba sai gashi haduwa din dasu wajen ya zamo kamar wajibi don yanzuma dai mun kara hadewa sai nayi saurin kawar da kaina gefe daya. Fuskansa dauke da murmushi dana sansa dashi ya amsa gaisuwan da maryam din tayi masa cikin girmawa kafin yace wai wana ba yar gidan baba umar din nan bace mai yawan tsale tsale din nan ni meye ma sunan ta? Itace Aeesha ko yace exactly sunan ta kenan kuwa ke kin girma yanzu bakya iya gaida mutane ko ? Maryam ce ta zunguroni alaman dani yake fa na juyo mukai ido da ido dashi kafin nace ina wunin ku ? A sake ya amsa kamar bashi ba da ada yake cikin daure fuska ga kowa don har manya gidan wasu na tsoronsa a lokacin. Matar naji tana fadin muje mana D gasu can suna jiran mu fa sunyi gaba hakan yasa ya juya suka tafi ba tare da ya tsaya amsa min ba. Allah maryam yau kin cuceni wanan mugun mutumin mai mugunta aini ko sunansa banso a kira a gaba don ban manta muguntansa a kaina. Ke dane fa yanzu ai kila koshi baison a tuna masa hakan bakiga duk yayi laushi ba kamar ba yaya habib ba ko jiya da akace zasuzo naji umma na fada sam bata son wanan matar nasa bansan meyasa ba wallahi. Ina ya aurota ne gata kamar kabila na fada ina jingina jikina a motan da muka tsaya bayansa tace naji kamar ance yar lokajace ita irin dai kabilu din nan ne dake tarewa Abuja. Sune ai daidai dashi na fada ina dago kai nagansu a tsaye da alaman yar tasu suke saurare don tana nuno inda muke tsaye din sake kawar da kaina nayi daga kallonsu. Nama mayar da hankalina akan waya ga baki daya na juya masu baya saida mukai sallama da Auwal ne na juyo garesu. Ke din nan yar iskace Aeesha yarinyar can fa da alama akanki takewa iyayyenta magana amma kika sharesu kamar baki gani ba. Nace ke bakiga uwar yadda ta nuna bata ma ganmu a wurin nan ba wa tafi da zamu kama binta gata kamar guntun doya. Samira tace irinsu ko sai masifa ba rabu da gajerar mace guntuwar mara kiba irinsu masifa na nan garesu wallahi nace ai maganin mazan ke nan yanzu wa zaice wanan abin matarsace ? Sai muka hango Aimana zuwan Aimana din yasa muka canza topic din zancen tazo muna da labarin an daukewa amarya sarka a cikin taro. Kinga mu bar wajen nan don Allah ina farida da Asmaune tace suna can ni ban iyawa naga ana kokarin daga hammata yasa nafito. Ina ganin Asmau tafito itama wuri duk ya yamutse da hayaniya nace muje mota gara mu bar