← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 101

Sashe 25

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

maman Aimana tace hjy bagata kina jin muna hausa ba da ita. Tubarkhallah masha Allah ta fada bayan ta mike na zauna ina fadin kalaba mama din tace ai dama na sani kitson ki bai wuce wanan ke ta dora da fadin manya ko kanana ? Da sauri nace manya mama ina tuke hijjab din kaina dama shi kadai na saka a kaina ba hula ko dan kwali tunda kan a banye yake min. Nan matan ta sake kaiwa zaune tana faman zuzuta kan nawa da ace ta sani da bata zauna din ba don ni abinda na tsana a rayuwana ke nan. Haka kuma ga zafi da nake ji har nakan kamawa mama din hannu don zafi wani lokaci sam banson abinda zai taba min rayuwata don haka nake akoda yaushe . Dan abu kadan zai tabeni yanzunne jikina zai ja a gurin da abin ya dan tabani donshine ko yaushe zaki saamu dakina tas don hakan yakan ban wahala. Shigowar wata da suke da ssanaiya da matar farko yasa gaba dayansu suka tsaya sharfi akan nawa kafin su gaji dayan tayi sallama ta wuce ya saura macen dakebi mun ta rage a gidan. Ina Allah Allah in tashi saiga wasu har mutum biyu sun shigo a lokacin da kyat na samu mama ta tsaya kama min kan na fito na barsu ko sallama bamu samuyi dai Aimana ba a lokacin. Ban shiga gida ba na biya gidan da ake murda taliya a unguwarmu na sayo na nufo gida da kyat na gama sulala taliyan nawa saidai bankai ga ciba dole na kwanta don kaina dake min ciwo. Ammah data zaci nagama bataji nayi magana ba ta dauka don ta kishingidane lokacin ina zaton barci takeyi ta fito tana fadin kin gamane Aeesha ? Taji shiru hakan yasa ta nufi wajen da ta hago tukuyar aje na sauke na aje budewa tayi taga ban taba ba yana yadda na dafashi aje. Hakan ya bata mamaki ta taka zuwa kofana tana magana sai ranta ya bata ina bayi kila kamar zata tafi ta dan leka hangoni tayi a kwance nayi rub da ciki kwance din. Salati ta soma tana fadin yau ga tsiya ki gama abinci makin ki zauna kici sai ki dawo daki ki kwanta kuma don shashanci. Ke Aeesha fa ta ambaci sunana da dan karfi hakan yasa na dago na dan kalleta da idanuwana da suka kade sukai jawur a lokacin. Subbahanallahi badai kitson bane yaja maki ciwon kai kuma yanzu kasa magana nayi sai kai dana kada mata kawai. Ikon Allah ta fada hankali tashe ta koma ta shiga dakinta sauran magani ta dauko min kwara biyu na panadol daya rage ta debo ruwa a randa ta tsureni saida taga na shanye ta juya tana fadin . Daga ciran kaya sai ya zamo kari ni tunda nagane hakan na daina damuwa da zancen kitsonki Aeesha ayi mace ace ba gyara ni na taba ganin hakan inba gareki ba ? Allah sarki duhun kai da jahilci ya hana Ammah ta gane cewa har yanzu jikina da nasu halittansa akwai bambamci sai take ganin hakan kamar wani surface kawai jikina keyi don ko nan din akwai ai wace bakace amma hakan yana faruwa dasu sai ya kasance mace bata son abinda zai taba lafiyan kanta din. Shan maganin a sannu kan ya fara lafa min jin yadda Ammah ta matsa min ne kan in tashi inci abinci yasa na dan fito na tsankwara zuwa dakina ina dan loma biyu bakina ba dadi don haka na koma na kwanta. Koda salman ya shigo office din kai ya dago ya dan kallesa sau daya yaci gaba da aikin da yakeyi ba tare da yai mashi magana ba. Basket din abincin da ya shigo dashi ya aje a gefe yana kallon wanda ke tsaye gabanshi a lokacin kafin yaji ya furta mai zaka iya tafiya amma ka maida hankali sosai don Allah ga aikinka . Don kasan mutumin nan ya iya takon saka sosai da mutane ta yadda zai bat da kamanshi yayi aikinsa ba tare da an gane hakan ba yace yes sir ya sara mashi ya fita. Sai lokacin salman din yakai zaune yana fadin good morning bai damu da amsawanshi ba yace a zuba breakfast ne yana dan kallonshi. Kasa yaga yakai yana dan kwantar da kansa saman hannayesa da yayi makari kamar filo dasu don yaji taushi alokacin. Ganin yadda ya kwanta yasa ya dan zuba masa ido kadan kafin yace dashi akwai matsalane yana mai kafeshi da idanuwansa. Hannu ya karkada masa kafin ya gane nufinsa ya mike tsaye yana shirin fita jin dan uwan nasa yaja tsuki yana dagowa yasa ya dan juyo garesa yana fadin ka zauna kayi break din ka niba yanzu ba kasani. Barin dawo akwai abinda zanyi a waje yanzun nan bai iya amsa mashi ba don kansa dake damunsa da ciwo ya kara kaiwa kwance din yadda yake da farko din. Salman din yana fita yabi wani dogon corridor dake wajen da yake weekend ne yasa ba mutane da yawa a cikin school din . Dan nisa kadan ya zauna yana fuskantar wani waje kafin can da sauri ya tura hannunsa a cikin alhijihunsa ya ciro wayansa kiran iPhone yana daukan wani photo ya mayar da wayan a aljihunsa. Yakai wani lokaci a zaune wajen kafin ya mike ya bar wajen bai koma office din dan uwan nasa ba kai tsaye ya nufi cikin haraban makaranta tafiya ya danyi mai nisa zuwa wani lungu yayi abinda zaiyi a can ya juyo koda ya dawo har lokacin dan uwan nasa na a yadda ya barshi dan barci ya samu a lokacin da har yai mai nisa kadan jin an shigo masa office din yasa ya dago ksi yana kallon maishi. Nan salman din ke fadin lafiya dai ko ya nuna masa kansa alamun shike damunsa dan shiru a lokacin hakan yasa ya zauna yana fadin ko zamu gidane don ina ganin ai kamar mun gama da yau. Saida ya dago da kyau ya tsurawa dan uwan nasa ido kafin yace dashi akwai wani abinda ka samu ne a yau yace ba za a rasa ba amma sai nan gaba kadan zakaji komai. Bai yarda da shirmen dan uwan nasa ba a yanzu don hakane ya kawar da kansa gefe daya kawai donshi baya son ma ya sako shi a zancen aikinsa ya dai fi barinsa a matsayin yaronsa kawai anan din. Basu jima ba ya mike don tafiya gida har yakai kofa ya juyo yana fadin kazo da mota ke nan yace ehh ko dai na kaika gidane sai in dawo in dauki motar tawa. No muje dai kawai ya fada dan haka daga shi har dan uwan ba wanda yaci abincin saida ya kai get yaba wanan yaron nasa ya karba yana godiya.
Chapter 25 · 0% Book details