← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 101

Sashe 42

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

ya hanani magana samira data karbi uwarta data fara zuba ke fadin hakan gareni. Gaskiya kudi yayi kinji shiyasa masu kudi suke jin dadin rayuwansu macen da baka aura ba kake kashewa wanan galarin haka ? Jiya mun kwana da mamakin kayan can yau sai ga uwa uba anyi muna kayan kallo ta ko ina yanzu gidan nan mai kallon waya saita huta Anty safiya ta dora da fadin hakan. Anty wallahi duk zancen nan idan nace dake bansan komai ba kada kiyi mamakin hakan don bansan za ayi duk wanan abin ba wallahi asalima sai yanzu nake gani nima kamar yadda kuka gani din. Ke yar nan yaron nan yace da saninki mana akai hakan ko don' kada ai maki fada zaki wani nuna baki san da zancen ba aiba abin fada a nan don wanan yafi karfin fada yanzu kuma ? Yau yaron nan ya nuna muna shi dan babban gidane na zahiri son mu shedane ga hakan yau na kara tabbatar da zancen malam kai tun ma jiya zance wallahi.
Chapter 42 · 0% Book details