← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 101

Sashe 48

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hjy kura dake tuki a haukace cikin tashin hankalin abinda idonta ya gano mata ta juyo tana fadin watau hjy Nasare matukar ba rabashi da yarinyar nan akayi ba babu yadda yaron nan zai lankwasu muna a yanzu matukar wanan tana cikin rayuwansa. Abune mai wuya hjy kura rabashi da ita yadda like nufi farat daya haka don ni kaina badon na daure ba ba zan iya ciwa yar nan mutunci haka a gabanta ba don' yarinyar nada kwarjini matuka a idon mutum. Gumi taji ya zubo mata kamar wace aka watsawa ruwan zafi ta dankai hannu ta share kafin Dan juyo kallo year uwar nata tana fadin . Nasare ki duba fa yaron nan tunda ya kyala ido yaga yarinyar nan gaba daya lokaci guda ya birkice har ya manta ko suwaye a tare dashi hankalinsa gaba daya ya koma gareta. Amma aisu iyayyen nasa basu kula da hakan ba basu san babban illa bace jefo iron su a cikin zuria don a karshe gaba daya zata jaye masa hankalinne ga kowa sai ita da yan uwanta ai mugun abin a cikin jini yake masu rabu da mace maikyau kinji hjy balle wanan din da idonta ya bude haka lokaci guda . Ki duba sai wani nuna yakeyi tankar baisa damu a wajen ba tunda tazo fara,a ya sauka a fuskanshi danice ke kawai hakkura zanyi da zancen hadin nan yaje ya karata da ita shi zai yabawa aya zaki ai akarshe. Wasa kokeyi ko ba,a hjy Nasare ai tunda nayi niyar hadashi da Hindu kuma na dace itama tana sonsa angama in baki labari yayi kuskure data fado a komata don ko wayayi masa tsaye a duniyan nan sai ya auri Hindu. Shi kuma yaya nasan yadda zanbi dash har ita hjy mami din don saina dasa kiyayya da gaba a tsakaninsu da dan in raba tsakaninsu muga ta tsiya son da kuma. A,a yaya kura ki bar masu dansu don Allah kada kiyi hakan tunda kema nakine yaron nan yaya bai cancanci hakan agareki ba yanzu gaskiya karki manta alherinsa garemu fiye da sauran yan uwa. Wani kina ganin zan jaye a niyatace Nasare ai yanzu aka soma ina ganin baki san baiwa da arzikin yaron nan bane har like ban shawara a yanzu injaye . Da wata ta shigo gidan nan taci banza mu kara komawa yan amshi gara ina ganin tawa gidan duk hanyan da zabin a yanzu na shirya sai ya dawo yana bin Hindu da kafarshi wallahi. Wanan fa ba yakina ni kadai bane Nasare yakin kan mune ga baki daya nake muna harsu iyayyen nasa haka kawai in zauna kallon ruwa ,,,, Shiru hjy Nasare din tayi tana tunane a zuciya kafin ta furta a fili yanzu na fahinciki yaya tace koke fa kin tsaya ana baki kina roko. Ido rufe na nufi get da zumar fita daga gidan yayinda Auwal ke bina a baya yana kwala min kira har ya cin min ja nayi na tsaya yake fadin kar kiyi haka man's Aeesha ki tsaya in dauko mota mu tafi. Yadda ya marairaice yana magana yasa naja na tsaya din ina bin bayansa da kallon yadda yake wani sauri a lokacin Atake naji zuciyana yana wani irin bugawa da karfin gaske lokaci guda sai wani abu nake jin yana yawo ajikina wanda na rasa meye wanan din don yafi gaban damuwa a lokacin. Tambayan kaina nayi meya kawoni irin gidan nan meye hadina dasu dama kome suka fada a kaina aigaskiya suka fada din don bankai matsayin bin dasu ba ai. Daidai nan Auwal ya karaso ya bude min mota don in shiga banyi musu ba son inaki ko tafiya ya isheni kafin nakai bskin titi nan da get ma na kasa kai kaina balle inda zan samu mota da zai karasani. Ina zama ya rufe ya shigo ya soma ja dagani har shi ba wanda yai magana na dan lokaci sai can naji yace hjy kura ke nan itace kebiwa daddyn oga wajen haihuwa. Amma tafi kowa fitina da izza a dakinsu fitinaniyace ta gaske komai nata a gadarance takeyisa da mijinta mai kudine sosai amma tunda ya mutu ta kama dukiyan ta kumushe ita da babban danta yanzu sai yan dabaru . Duk kuma wanan bai isheta darasi ba kowa a wullakance take kallonsa har gobe ko mu nan saboda ita saida muka dauke kafan mu wani lokaci gidan nan saboda cin mutuncin da tayi muna. Saida Man Bashir ya dawo shine ya dawo damu ba yadda zatayi don kamar tana tsoronsa kuma fa dashi Salman dash Abu dayane iyayyensu son kawai dai shi salman ya fito a gidan maluntane alma duk da hakan ba tayi masa kallon daraja a idonta. Balle ni da tasan iyayyena a Barga suke zama cikin fadawa ai banda ko digon daraja a idanunta kawai su ahalin daddy ne kawai suka fita daban a cikinsu. Auwal ai gaskiya ta fada ina ni ina Man Bash dama ai kowa yasan yafi karfina kawai dai haduwan mu dashi gamon jinine na dauka amma bawai nakai level din da zan tsaya dashi bane. Balle har suyi zargin ko ina soyayya dashine ko wani watsewa don kawai ina yar tallakawa Auwal zaisa su dauka banda gata ko tarbiya shin laifine don nazo duba wanda ya damu da damuta sai hakan ya zamo laifi a wajensu na dauka kana kula wanda ya damu da naka ne ai. Kar kice haka Aeesha donsu a zaton su soyayya kukeyi da Man Bashir zama dake zaki iya hana ya auri yarta kamar yadda suke fatan hadusu bakiji meta fada a cikin zancen ta ba. Shiko a yadda na san sa yana da wuyama ya auri yar nata kamar yadda suke fatan hadasu auren don banga alaman wani kaunanta ba gareshi. A school dinku take itama amma ko sau daya kin taba ganin ya tsaya kulata balle yasan da tana nan sudai me sukr haukansu kawai a kan sa don sam bai zancenta da kowa. Idona na lumshe tare da cigaba da tunane ina duban sakamako wanan wani irin abune shiya akeson musulmi da biyayya ga ubangiji da manzonsa akan duk abinda suka hani bawa dayi don rashin yinsa yafi sauki ga bawa akan ya aikata abin ki din. Don yanzu gashi ni da banji ban kuma gani akarshe nice da uwayen rikona muke girban wahalan dake cikin hakan duk da Abbu yana kan jadda min ni din ba shegiya bace ina da ubana saidai balarabene kuma ba,an inda yake ba. Yanzu mai gari ya waya agareni sunan ina da uba wazai taba yarda da hakan cewa ni mai ubace wai tunda ba,aga uban nawa ba a zahirance ? Hakan dole na nufin bandashi ke nan tunda ko kudi aka zube babu mai kawo uban nawa yanzu kawai makomana da mara uba yanzu dayane. Bansan lokacin dana fashe da wani irin kuka ba mai tsuma rai da yasa Auwal cin burki da sauri yana tambayana ko lafiya karshe dai ya samu wuri ya packer motar ya shiga lalashina fita yayi zuwa wajen wani shago ya also min goran ruwa ya kawo min wai insha. Kai na girgiza masa alaman ya barshi yace karbi ki wanke fuskanki dashi to kada ki shiga mutane a gane kinyi kuka. Zancensa gaskiyane dole na karba din na Dan sauke kafata ta waje na wanken fuskan nawa da ruwan kana na danji sauki ina ajiyan zuciya. Auwal din yana tsaye cikin damuwa da nuna kulawansa akaina kafin yace dani mu tafine ? Na gyada masa kai a hankali alaman eeh yana tsaye saidana zaune ya rufe kofan ya zagayo ya shiga ya tayar da motan saida muka kai kamar five second a motan ba wanda yai magana kafin can inji yace addua da sadaka ya kamata kiyi Aeesha. Addua yana kau da komai ga bawan daya yarda Allah shikeyi a duo lokacin da yaso sai kiga abin yazo maki a cikin sauki ba anbinda ya gagari ubangiji matsawan ka dogara gareshi. Can kamar ba zan yi magana ba sai yaji nace Auwal tawa kaddaran ta riga data faru a kaina ko gaskiya suka fada Auwal dan asali sai yar asali nima rigimace yasa nayi saurin yarda da malam a yanzu. Don matsayina baikai ga ko dan tallakansu ba ballesu diyan sarakuna masu kuma fada aji a gari irinsu komai sun hada a wajensu ilimi sarauta kudi mulki duo akwaishi wajensu . Inani ina gwamatsuwar irin wanan ahalin nida banko san asalina ba balle makomata sai bayin Allah nan dake rike dani suna gatana da komai nawa Auwal Don Allah kibar fadin hakan akanki Aeesha ki godewa Allah daya baki masu rikeki din wasu na can kamarki ga gata ga komai amma sun taso a gidan marayu basu da kowa a duniya sai Allah da manzonsa kuma haka suke rayuwa suna my,amula da kowa cikin salama. A hankali na gyada masa kai kafin nace kwarai hakane Auwal tabbas akwaisu yace kin gani ashe ke naki mai saukine tunda yau kina da wa yanda zaki nun a matsayin iyayye a gareki. Sosai naji maganansa ya kwanta min a rai tabbas dole in kara godewa Allah bisa ni,imar da yai min da bai barmi hakana ba cikin duniya kara zube kamar yadda yabar wasu . Da sauri na furta astagarullah a fili yace haka ya dace dake a yanzu shawara da zan baki shine ki cire zancen kowa a zuciyar ki yanzu ki maida hankali ga karatun ki koshi kika kama ya isheki a rayuwa. Haka kuma zaki samu madogara mai kyau da kowa zai manta da asalin naki kiga an koma ana binki son abinki wanan haka duniya ta gada a yanzu ko ba,a soka don komai ba za a soka don abin hannun ka. Na tabbatar tunda kika shigo rayuwan Man bashir yana da wuya ki tabe a rayuwan ki haka kara zube don yadda kike tsamani din nan donshi mutum me mai kaifi daya ga duk abinda yasa a gabanshi. Ko bashi ba na tabbatar har daddy a yanzu sun tunzurashi a kanki yau Allah kadai yasan abinda zai biyo bayan hakan zakice na fada maki wannan watarana ki dai dage da addua ki yawaita sada kuma kina tawakali ga ubangiji. Nagode Auwal na fada a sanyayye ina
Chapter 48 · 0% Book details