← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 101

Sashe 3

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

fara sol ta kurawa photon ido kafin ta juya bayasa taga rubutu a jikinsa da larabci kokarin karantawa tayi ilimjn ta na ajami baikai ta gane me aka rubuta a photon ba amma ta gane shekarun photon da akarubuta shima da larabci ana nufin 1982. Idan ta juya zuwa boko ta sake juya photon tana karewa matar da yar kallo kafin ta kawar zuwa dayan photon dashima saboda ajiya ya fara baki a lokacin. Wanan matar daice da yar nata tare da wani matshjn balarabe rugume da ita saidai wanan yana da bambanci da wacan don yarinyar photon ta dan tasa sosai a wanan lokacin girmanta yakai kimani yar wata takwas ko tara a lokacin don ga ribon din yara an mata dauri gida biyu irin mai zare dinban uwar tana saye da bakin jallabiya nada a jikinta hakan namijin shima farace sol irin na larabawa ya saka shima dai wanan hoton an masa rubutun larabcin a jikinsa. Tatattara ta mayar yadda ta sameshi har zata mayar a inda ta jawoshi sai kuma tayi wani tunane ta saita dorashi saman dan teburin da Ammah din ke dan ajiye ajiyenta. Ta samu ta karasa aikin dakin gudun kada malam ya dawo ya samu bata karasa ba ta makara wajen girki wutan abinci ta dora kamar kullum ta zauna jiran tsamani can taji kararawan keken yadda yake alama ya dawo. Da murnan ta ta tareshi ta karbi Aeesha ikon Allah tun daga waje naga wanan aikin naki ai nasan ba kowa bane kece. Abbu naga ban aikin komai yau kuma ba islamiya yasa nace bari kawai inyi yan gyare gyaren nan yace ikon Allah kin dai gado tsabtan nan kema Nana. Donshi da nana Aisha yake kiranta dashi sunan da uwarta tazo masu dashi ke nan tun farko kuma ya rike a bakinsa har yau dashi yake kiranta kuma a bakinsa. Allah ya gani yarinyar tausayi take basa a duk lokacin daya kalleta tun tana karamarta saidai ba yadda ya iya nata kaddaran a haka yazo mata ita. Duk da wahala da talaucin da yarinyar ke ciki hakan baisa hasketa na asali dushewa ba yanzun ma datake girman nan hasken yana dada kara fitowane a jikinta. Zuwa lokacin tana tankaden gari zatayi talge don yamma yayi sosai hakan yasa ya kewaya ya fito yana fadin nana bari na dan zagaya kafin yamma in dan samo icce a kara zube maku. Tayi masa Allah ya tsare ya fita kafin ya dawo ta gama komai ta gyara waje don sai ana kiran magariba ya dawo da daurin icce a bayan kekensa yana fadin kai kasan nan dan inda muke samu icen a yanzu duk a sare filin . Masu kudi sun saye wai zasu gina ma,aikata a wajen saida kyat na dan samo wanan ta gama alwala ta mike tana fadin Abbu sannu da dawowa ya amsa sannu da gida nana yanzu kan sai ku fara tatali don abin ya fara wuce tunanen mu. Saida ta taimaka masa suka kwashe don yayi saurin fita ya samu jam,i ta shiga daki ta tayarda sallah bayan ta saya kyauren gidan. Kamar yadda ya saba dawowa hakan ya shigo shifida ta dauka takai masa waje inda suke cin abincin dare kafin ta dawo ta zauna taci nata saidai ga gidan ba dadi rashin Ammah ga kuma zancen hoton nan data gani na matan nan don abin ya tsaya mata a rai sosai tun lokacin. Inba zato bane tabbas itace a jikin photon nan hakan kuma na nufin matarda ta gani itace mahaifiyarta ke nan tare da wanan namijin balaraben na jikjn photon. Don hakane ta yanke shawaran tambayab Abbu gaskiyan zancen aka mutanen cikin hoton don tasa da wuya yadda tasan halin Abbu din ya boye mata gaskiyan zancen. Yau Abbu bai dade wajen hiransu ba sanin su kadaine a gidan duk da yana zaton a yanzu nana din tayi barci ai don akwaita da saurin baci amma son rikon amana irin nasa yasa ya shigo gida a lokacin. Ganin hasken fitila a dakin nata yasa yana aje tabarman yake fadin nana ikon Allah har yanzu baki barci ba ashe tace yanzu nagama bitan karatuna Abbu. Ta karsa fitowa tana fadin a shimfidama tabarmane anan yace ehh dama tasani ko Ammah ke nan yana kai wani lokaci wajen gidan yana shan iska kwance a tsakar gida tunda ba fanka bane dasu a gidan irin mutanane masu sarin jin zafi a jikinsu. Saida ta gama shifidar har ruwan sha ta debo mashi ta aje a gefe ya zauna yana bissimillah ta juya ta shiga dakinsu ta fito da wanan hoton gefen shi ta samu ta zauna tana fadin Abbu tambayanka nazo yi don Allah idan ka sani kafada min gaskiya Abbu ko zanji sanyin abinda ke damun zuciyana a yau. Cikin mamaki ya kallota gabansa na fafuwa yace me kuma ya faru nana har yake damun zuciyarki amma baki fada muna ba muna a matsayin iyayyen ki cikin garin nan nana ? A,a Abbu ba hakan nake nufi ba ta fada cikin ladabi tare da fadin kasan Ammah taja min kunne da kada in kara zuwa mata da zancen nan ba gaskiya bane abinda ake fada akaina cewa ni din banda uba shine yau ina gyaran dakinku da rana naga wanan hoton ta dauko ledan da takardun dake cikinsa ta mika masa . Karba yayi ya kurawa photon ido na dan lokaci kafin yace bincike kikaiwa Ammah din a dakinta har kika gano wanan hoton ? Da sauri tace haram Abbu wallahi ina gyarane na daukosa har zan zubar saboda ledan dana gani haka a cikwaikwiye sai kuma nayi tunane na tsaya na bude shine naga wanan hoton a ciki. Yasa nace bari na tambaye ko kasan waye a cikin wanan hoton don Allah Abbu kada ka boye min duk da nasan Ammah zatayi fadan hakan idan ta sani amma ba zan taba barin ta sani ba insha Allah kome ko zaka fada min. Hannu ya kai ya kara dago photon ya kurawa hoton idona dan lokaci kafin ya sauke ajiyan zuciya ya kalleta duk da akwai duhu a lokacin hakan bai hana yaga yadda ta kafesa da idanunta ba .
Chapter 3 · 0% Book details