← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 101

Sashe 46

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

har suna hada kafa wajen fita. Dan shirune ya biyo bayan fitansu kafin daddy nasa yace kada wanan abin ya dameku Ku barni dasu kawai zanyi maganin su shima ya fita. Shi ko dan nasa sai faman murmushi da yakeyi a fuskansa baice komai ba har daddy din nasa dana ga alamun so karara yakewa dan nasa ya fita. Sai can ya kalloni ina zaune na sada kaina kasa zuciyata tana min suya da kokarin rufewa lokaci guda kan abinda ya faru din. Muryan shi yane naji ya ratsa min kunnena da fadin . Are you OK hakan yasa na dago naga yana kallona na daga masa kai alaman eeh iam OK din kamar yadda ya tambaya . Sai naji yace right yana kokarin daga kafar ya sauke ta kasa yacewa Auwal ya dauko min abin sha lokacin nace dashi. No iam going dama nazo naga jikin nakane kuma Alhamdullahi naga da sauki so ni zan koma don ina da lectures three . So yanzu kin gani hankaliki ya kwanta ko na dan kara murmushin karfin hali ina fadin gaskiya hakane na mike tsaye ina karasa fadin hakan. It's means kin dauki zancen su da zafi ke nan ko na ji ya jefo min tambayan a bazata. Da Saudi na girgiza masa kaina cikin alaman dakewa nace ba komai ai Allah ya kara lafiya na juya ta hanyar da muka shigo na fita da sauri Auwal ma ya biyoni yana kirana saidai ban kara juyowa ba. Saida na fita na hango fitar matan tare da yaran nasu gidan sai lokaci naji hawayen bakin ciki yana sauka min a fuskata lokaci guda
Chapter 46 · 0% Book details