Sashe 55
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tayi part din yan matan da suka cika daki dam ana hayaniya. Muna shiga kuma kallo ya dawo garemu aka fara gaisawa zaune nakai saman wani dan Stoll da wasu kaya ke sama nacewa Asmau tazo ta zauna na dan gusa mata muka zauna a tare. Yanzu anty Fati idan ba munzo ba ba za a aika muna da anko din ba farida ta fada wace aka kira da fati din race to farida ankon kala ukkune bansan wanda kukeso ba ciki. Hakan yasa ta juyo gareni tana fadin wait wani zamuyi Aeesha nace wani event zamu tafi a ciki ? An kwaso anko din ba laifi gaskiya dana dinner saina kamu sai sai kuma na ranan yini yadda akai muna bayani yarinyar dake bayani din tana wani kaudi take fadin idan duka zakuyi yakama sha biyu ko wani mutum guda lokacin kaya suna da sauki sosai zeey don da yanzune zaikai almost to fourty thousands gaskiya . Yanzu dai a bamu muje dashi muyi shawara sai a dawo da sauran amaryan ta fada kamar jira wace ta kawo kayan keyi naji tace a,a anty gaskiya ba bashi ba zan bayar ba kizo ki tafi gidan mijinki ki barni da yawon hanya karban bashi karshe azo a fadama maganan banza. Farida ta barshi don Allah na fada ina mikewa tsaye don yadda take kokarin bamu kunya a gaban kawayensu zakice bata san inda muka fito ba. Sai naji amaryan tace kamar ya abarshi Aeesha a barshi mana aiba dole bane sai kunyi dama maryam da take mai saurin zuciya har takai kofa tana fadin kuzo muje don Allah. Amaryan tace haba maryam kema kinsan halin saratu ai da zancen banza idan basuyi ba suwaye zasuyi su yan gida da kike wanan magana haka ? Nan dai amaryan tayi cikinta tare da sauran yan dakin suka nuna mata rashin kyautawanta kafin amaryan ta juyo tana fadin yanzu wani zakuyi ciki nidai in son samu ne kuyi duka don Allah. Gaskiya kam wata ta fada saratu din ta kara fadin wai barnan baki Allah yasa ko kala daya dai ayi din. Asmau cire muna Iowa kala guda kala ukku harda Samira lokaci daya naga sun kalloni tana cirewa na mike na hada kaf din mu na juya wajen amaryan ina fadin bamu leda mu saka anty. Nifa inji wars kudi a hannu ba barazana ba wai isan baka isa ba galadiman tusa inji kudi a hannu kawai ta fada tana miko hannu ki bimu ki karbo kudin ki. Don isan galadiman yan Adam ai in ba a isa ba ayi saratu isance ya kawo hakan yanzun ma nan ko amaryan ta hauta da fada har iyayyen sukaji suka shigo. Daya daga cikin yan matan nan ta mayar masu da abindake faruwa ta kare da fadin ba a haka saratu ai komu nan mukai zuciya nesa da ita wallahi da bamu zo gidan nan ba. Mukan zamu zo tunda mun gane nufinta ai da ace bukintane idan munzo duk abinda taga dama tayi muna amma anty Fati ba tai muna komai ba kuma har gida ta bimu taci muna mutunci yasa mukazo. Iyayyen na magana tanayi muka dauki kayan zuwa gida Asmau ce ta dauko a kai kowa da abinda yake fadi ina jinsu ban daiyi magana ba saida muka kawo kofan gidansu muka tsaya. Yanzu Aeesha dan kalula kinsa mun dauko anko din nan ta yaya zamu biya ke nan nace Ku dauki naku ku bar muna namu zuwa gobe kwaji komai . Ina baki labarin nan nan ne tiryan tiryan zeey don abinda zai biyo baya gaba saboda ku fahinta karfe takwas na baiwa Asmau kudinsu takai masu karfe tara alheri ya shigo min daga Man bashir galleleyar Montana ta tsaya a kofan gidan mu. Inda gidan rabakaya kuma ke alhinin kudin kayan da Asmau ta tattara ta kai masu cash babu kwandala da yai ciwon kai ciki. Auwalne yazo da motan tare da sauran alherin data biyo baya ya dade tare da Abbu suna magana kafin Abbu ya aika na fito nazo muka gaisa ya dan yi min bayani a gurguje tare da mika min key din motar a hannu na. Ban tambayeshi komai kan man bashir din ba illa yana lafiya ko nayi hakanne don in nusa masa tunda yace including me wanan kalman ya tsaya min a rai lokacin. Alheri kuma yayi niyar min ne yasa ya aiko dashi donshi mai kaikayin hannu kullum a cikin susan hannu yake ga wanda rabosa ya koka gareshi dama. Munyi murnan mota yayin da Abbu ke murnan sabon shagonsa da za a gyara wanda Auwal yai masa albishir lokacin. Motar tazo min a bazata don na debe rai ga zancen malam Bashir yanzu gaba daya tundai da banjo komai daga garesu ba na tsawon kwanakin da aka diba ko Auwal ya dauke kafa banji komai a wajensa ba, A ranan Abbu ya kira masu aiki suka gyara min tsohon get din gidan mu dake rufe shekara da shekaru aka budeshi aikai masa siminti . Saida yamma muna zaune tsakar gida muna hira Asmau ke muna zancen gidan Rabakaya wanan saratun abinda tace data kai masu kudi wai hakan yafi sauki ita ko ina yarinya zata fito da kudi aibai dameta ba ita kuma Asmau tace da ita balls kowa yasan muba cima zaune bane ai muna neman na kanmu da karfin mu basai mun jira an muna ba. Ammah ke tambaya Asmau ta fara bata labarin abinda ya faru tun farko nan naji amma tace ai dole tayi hakan uwarta ba can Alh ya aurota Okene ba yana raba kayanshi lokacin. Kinshin yan uba takeyiwa Fati a fakaice ita ta biyo ku gida kunzo mata kara hassadan hakan takeyi a fakaice ai. Ammah don dai Farida ta matsa da wanan bukin ne in bashi ba sam nawa baizo daya da yaran gidan nan ba don rashin mutuncinsu yayi yawa wallahi. Ku daije mata tunda ta biyoku balle yan mata na son suga bukinki ya haska kowa ya hallara an cika waje hakan sai ace bukin wance ya haska har dasu wance sunje balle ku da kuke yan gida anty safiya ta fada. Washegari muka kai dinki don su farida da maryam sunzo wanan shagon da khairat ta kaini wanan karon ma can nakai dinki ya fada muna ranan da zamuzo mu s karba. Mun dawo gidane muka samu maman Aimana tazo muna wuni nayi mamakin hakan don yana da wuya sana,anta na kitso ya bari ta fito don kullum cikin yan kitso take ita. Nan na zauna falo muka gaisa take ta yabon yadda na girma na koma kafin tace Aimana yanzu fafir taki bokon nan bayan wahalan da tasha a baya nasa tasa wanan aure a zuciyarta. Aure kuma na tambaya cikin mamaki tace wait baku wayane nace a,a mama mun kwana biyu gaskiya bamuyi waya ba. Ashe baki san da zancen auren ba ke nan nace bata fada min ko dai wanda tun tana nan take zancensa wanda ke zaune a turai amma tace zancen a gurinki ya fito mama ? Kwarai kuwa zance shine dai har yanzu ita da ubanta sun hau sun zauna basu taba ganin mutumi ba ko sanin waye shi alma wai haka suke son ayi aure. Sai naji Ammah tace hakan na yuyuwa kuwa ai aure ba wasa bane wajibine abi ka,idojisa kafin a aura mashi ita. Ni a yaddama nake ji shine wai kowa fa baisan dan hjy ba an daiga tazo ta tare a gidan daga bays data fara sabawa da mutane take fadin ai danta dake kasan wajene ya gina mata gidan amma har yau din nan ba wanda ya sanshi gaakiya. Amma haka baban Aimana yayi tsaye wait sai shi don kawai hjy na masu wasa da kudi abin takaici yanzuma suke sintirin binta ko yaushe kan zancen. Amma ko Aimana batayi dabara ba shine zata bar karatunta tun yanzu kan zancen da baida tushe baida dalili haba dai. Bari inna koma zan turo maku ita ai yar gandoki muje bukine da taji zancen buki yanzune zaku ganta gidan nan ni dai na barsu nan da Ammah tana fada mata irin halinda suke ciki yanzu gidan. Banji dadin jin zancen Aimana na barin school ba don zatayi aure saita bar karatunta ina hankalin Aimana ya shigane wai ? Sunje kitso da kumshi duk akan bukin da nake gani ba wani muhinmancin halartan mu wajen duk da a yanzu kan hidimar bukin zuwan anty Fati biyu gidan mu kan bukin. Duk da dai ni ba gwanan zuwa bukin kowa bane amma wanan yanzu dole na halarta tunda ya zama kamar na family din mune. Kaina na wanke kawai sai mai dana shafa mai ya kwanta banyi kumshi ba ko wani iri amma dai na gyara jikina don in fito fes kamar kowa. Ranan saka lalle ban samu zuwaba su samira sukaje sun dawo suna hira abubuwan da akayi saboda Ammah ne banje ba don zata fita ga anty ma tace zataje kamun yasa na zauna gida. Sai washegarine da za ai kamu zan je sai gasu maryam da farida sunzo akan muje gidan Rabakaya din anty Fati tana neman mu wai . Banso zuwa ba amma dole na shirya muka tafi wani dan dogon rigane a jikina mara nauyi marron colour sai gyale dana dora na rufe kaina dashi sai kuma wayata a dayan hannu tare da keys din dakina dana rufo. Banyi zaton bukin ya kankama ba haka da banzo da wanan shigar ba haka don sai najini kamar sakayau wajen duk idanuwa a kaina. Saboda tufafin basu wani rufe min jiki ba sosai duk da a yanzu na rage saka manyan hijjab yadda nakeyi da can don dokan da aka saka muna har na fara sabawa da fita haka kuma. Motocine a kofan gidan da dan yawa sai mutanen da suka cika wajen naji maryam na fadin ango ya iso ke nan don gashi can na hango . Ai tunda kikaji ya sulaiman yace yau zai iso ango yazone gabana naji ya fadi lokaci guda don ambatan sunan sulaiman din da tayi a lokacin. Wai wai wai ke duba can ya Habbib ma yazo ashe inda take nunawa din na kalla a take na tuno da murde min kunnen