Sashe 21
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk wani fadi da Abbu yayi a kaina wanan bawan Allah ya taimaka hakan ya samu har Allah ya nufa na samu gurbi a jami,an BUK anan kano. Saidai matsala dayace yai mun nisa da gida sosai gaskiya ga kuma Abbu yace shi bai yarda da kwana a can ba yafi amincewa jeka ka dawo. Hakan ya jawo dan cecekuce da tsaiko ga tafiyan nawa saidai ina zuwa yin abubuwan da suka dace wanda kafin a fara karatu akeyi. Saidai ina shan barazanan kallo a wajen mutane wajen bama maza ba har gun mata yan uwana wanda abinda na tsarga ke nan a rayuwata yawan kallo din nan ga mutane. Yadda abin ya faro a rana ta ukkune da naje school din hijjab dina tare da face mark dina like a fuskana don bata da kama. Amma sai wanda zan gani din ya sawa takardan nawa hannu akace ya fita baya nan don haka saina jira har na dan zauna inda sauran dalibai irina ke zama na suna ta hiransu har na kusa dani suka dauko zancen mutumin da zamu gani din duk abinda suke fada akunnuwana. Hakan yasa naji na kagu don tsoroma saina bar wajen kawai na koma can wajajen da motocine aka jera birjit masu kyau da ma marasa kyau don kada in bata jikina na hari wajen wata mota dake rufe nasan ko maishi yayi hakan ne don yawan kuran da akeyi da iska a lokacin. Durkushe nakai a wajen kaina kasa yayin da hijjab dina ya baje a kasa ya rufe min kafafuwa sam banji zuwan mutum ba na daiji kamshin turare a gabana kamar an kura min ido wanan yasa na dago darara daran idanuwana mai suffam na juda na sauke saman kafan maishi ina dago da kaina zuwa kallon shi tun daga kafa har zuwa kai. Hakan yasa na mike zubur tsaye yayin da naga mai shi ya danja baya ya fara waige waige kafin ya mayar da kallonsa a takardan dake hannuna yana fadin. Excuse me a dan siririn murya da bai fita kamar a cikin izza da isa da takama meka fada yace bakiji bane kauce a nan ki ban waje please ni ai ban tare ma waje ba na sake fada. Ina jan tsuki cikin takaici nake fadin in badon wanan mugun mutumin mai izzan tsiya ba da akace ni bakako ganina wajen nan ai. Kamar yana son tantace wani abu naga yakai kallo ga kafana da hannayena ya koma fadin zan shiga mota hakan yasa na juya da sauri ina kallon motan sai kuma nace yi hakkuri fa hauahin wanan bawan Allah daya shanya mu tun safe yasa na dan dumaice na jaye kadan daga gefensa naga wani yana yaye mai motar wa iyazu billah na fada a raina ashe gun motan manya naje na tsaya ban sani ba. Hakan yasa na juya na fara takawa a hankali raina a bace sanin yau jumma,ace kuraren lokacine gashi monday ake son mu fara daukan lecture din mu don har ance wai wasu sun fara attending ko. Motar naji an tayar don ni har na juya zan bar wajen cikin mutuwan jiki kafin naji dayan mutumin na fadin ke kawo takardan a gani hakan yasa na dan juyo na kallesa ina fadin waini ? Ke mana bakiji me nace bane tunane na dan tsayayi kafin kuma na daga kafa zuwa inda suken don ban sani ba ko zai iya taimaka min ga hakan. Karba yayi don har lokacin shi yana tsaye waje bai shiga motar ba tunda na mika mai naga ya kalla yayi murmushi kafin ya mikawa na cikin motan. Ina nan tsaye jin kaina a kasa can ya kara miko min yana fadin karbi zance ya kare ko inji dayan mutumin dake waje tsaye shima farine sol kamar dayan a cikinsu bansan wa yafi wani haske ba a idona tunda ba kallon kurulla nayi masu ba. Karban takardana nayi na juya ina kunkumi cewa gulma yanzu har da maza kunsa ba taimakona zakuyi ba kuka tsaya min tsegumi da sa ido. Ke ya sake fada na juyo cire face mark din nan naki ban tsaya ba na furta akan me zan cire abuna kaji mai kai da wani magana kuma ? A rainon Ammace da Abbu fa shagwaba har sari don ma ban da time din shiga mutane balle yanzu da nasa a raina kowa yaimin zan masa don in tsira da raina wajen mutane masu bibikon kan asalina. Daga cikin motan naji anyi min wani tsawa daya firgitani nakai hannu na sabule dan facemark din kadan ina murguda baki baifi second ba na mayar da sauri yadda yake sai karan tashin motar naji a kunnuwana da sauri sun bar wajen. Bin bayan motar nayi da kallo number kano ce a motar saidai special number ce a motar nagani hakan yasa naja kafata a raunane zuwa inda na baro sauran dalibai irina zaune suna dakon mutumin. Dan wuri na samu nisa dasu kadan na tsaya nakai minti goma kamar ance in sake kallon takardan dake hannuna sai naga is signed abin ya ban mamaki matuka har ina furta la,illah a fili. Dan tunane na tsaya nayi kafin na nufi inda zanyi surmitting na mika ta dan kusuwa naga da sauri maishi ya lekoni haka sauran ke bina da kallo yace dankari kinyi sa,a ke ashe ? Haka na fito duk suka bini da ido suna kallo ganin an karbi takardan nawa alaman ke nan an saka min hannu a nawa naja zulunbun hijjab dina na bar wajen a hankali duk da nasan idanuwasu a kaina yake. Titi na nufa na tari abin hawa sai gida a gajiye nake kamar nayi wani aiki don wahalan da nake sintirin yi a yan kwanakin Ammah kawai na gayar da gida na shige daki na kwanta ban falka ba sai bayan la,asar koshi yunwa ya tayar dani. Fitowa nayi na debi ruwa a bucket na daureye jikina tunda ina fashin sallah a lokacin har brush saida nayi kafin in nemi abinci. Abinci naci sosai inaba Ammah labarin na samu na kammala komai a cikin sauki ba yadda nayi tunane tace Aeesha kin fita da albarkan iyayye fa akafanki . Addu,an mu iyayye an fada maki yana faduwa kasa banzane ni dai ki kara tsare kanki don Allah wanan wurin da zaki wurine daya tara mutane daban daban daga yayan manya har tallakawa don haka ki zamo mai natsuwa da kula da wa yanda zakiyi hurda dasu don Allah. Nan nace ni zan baki labari yau Ammah ba iya yina ya kwasheni zuwa wajen daba jama,a ba na tsaya nan na kwashe labarin kaf na bata. Tana dariya kuma ga tsoro a fuskanta tace dama nasani kabu kabunki da ji dai kai din nan naki sai ya kaiki da haka to shi wanda kika zaga din gabanshi har yasa maki hannu ba mamaki ma shi dinne ya saka maki hannu ai. Shi kuma na fada a zabure tace kwarai in bashi ba haka kawai zai karbi takardan ya saka maki hannu akan wani dalili kuma su karba bayan kin kai ? Na shiga ukku indai shine Ammah din na zagesu tas a gabansu nikan shiyasa nake cewa ki rage wanan girman kan naki malam yace wai in barki a jinin ki yake na sani ko ke din yar sarautane ? Allah sarki kilama yar mai wanki da gugane nacen din wani dan sarauta zai auri bakar fata a can hakan yasa Amma dagowa tana kallona niko na fuske. Sai naji tace koma dai waye ai dadin abin ta hanyar halas aka haifeki Aeesha kuma Allah maji rokon bawansane ako yaushe . Abbu ya dawo da yamma da ledojinsa niki niki ina daki ina jin muryansa na fito ina taroshi kayan na karba yana a hannunsa. Ya miko min leda biyu daya fara saukewa sama kekensa nakai dakin Ammah zan shiga ya juyo yana fadin yaki Nana ajeshi nan waje inzo don haka na dire a inda yace din na aje na koma na dauko sauran nakawo na juya zan shiga daki yace yaki zo nan ai. Hakan yasa na juyo zuwa gareshi Ammah ce a lokacin take shimfida masa tabarma tare da gyara kayan nan dai na dawo na karba a hannunta kafin mu dukka ukkun mu samu wuri mu zauna. Ammahce ce take fadin arziki haka malam jabe jabe daga ina nunani yayi yana fadin duk na yatace ga baki daya don shirin karatun ta da zata soma jibi. Ikon Allah har haka malam anya ba bata yarinyar nan zakayi ba da hakan kai ya girgirza tare da fadin assha Ammamatan banyi zaton jin hakan a gareki ba kan yata. Da sauri Ammah din ke fadin sam malam ba hakan nake nufi ba gaskiya to banda abinki Ammah nana shiyafa yaro ga iyayyensa ya kamata ace ya dogara. Su tsare mai komai na rayuwa da karfin su ba sai yaje yana hange a waje ba wanan wajen wajene na mabanbanta mutane zata shiga a yanzu. Yau in mun tsare yar mu da dan abinda Allah ya hore muna wanan zaisa hankalinta ya kau akan duk wani abinda zata hango a wani zata tsaya iya karfin mu ta goga da kowa a wanan wajen haka kuma zata fita daga kaidin tarkon dake dakon ta a can sunan jami,a ke kikeji a baki Ammamatan a yanzu. Hakan yasa naje gun yarinyar nan mai dinki na gaban shagon mu nayi mata bayani da yake yar arzikine kudin yadi dana kayan aiki kadai ta karba a waje sai gashi yau wai har ta gama komai ta miko min kin gansu nan sune nan data dinkawa yar mu nana ya fara jawo kayan yana fitarwa daga ledan. Dan murmushin jin dadin nake fitarwa daga fuskana don Abbu ya gama min komai a rayuwata kuma gaskiya ya fada kan tsarinsa. Murnushina ya dakatane a daidao lokacin da ya furta kinga idan ta hada da wanan da wanda nana ta turo mata nasan zasu kaita wani dan lokaci tana ja. Take naji fuskana ya tsuke lokaci guda don ambantan sunan wanan matar da yayi a lokacin gaba bansan sanda bakina ya bude ba nace. Abbu wanan ma ai zai isheni ko ban hada da wancan ba,,,, nanata da wancan nake