Sashe 66
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai waye dan iska yaro me kake daukan kankane cikin mu Bashir hjy kura ta mike tana fadan hakan gareshi. Ta nunashi tace kana dauka kafi wanine a cikin mu nan kome hjy zata fadi magana ka ketare a gaban mu ? Har kana kokarin fadin maganan banza ko ita hindun ka fitane data yarda, saima ince taimakonka za ayi har hindu ta zauna dakai ai Ooh soryy aunts zancena da tsohuwar nan ne a yanzu ya shafeki ko don Allah kiyi shiru ba daku nakeyi ba a yanzu ina zance da kakatace wanan da tayi zamaninta take son ta shigo na wasu nake magana ban kawo gareku ba tukun ya hada hanayesa waje daya lokaci guda alaman ban hakkuri a gareta ya juya zai fita. Hakan yasa hjy kura fadin tabbas ya tabbata kana shaye shaye bashir wanan iskancin har ina kai kuma yaya ka zuba masa ido yana ciwa hjy mutunci haka a gabanka ? Babu mai kallon bashir ya kira sa dan shaye shaye yarki daice yar shaye shaye kowa kuma ya sani wajen nan mami ta fada. Shima saida ya kallo uwar balle su da suke ganin abin mamaki a yau don sunbar zancen bashir sun koma mamakin mami da ko hannu kasa mata a ido bata taba cewa don me ? Yau sai gashi a gaban kowa tana fada akan danta da akai wanan zaman donshi ba tsoro ko shayin idon kowa ta tarewa danta fada karo na farko a rayuwanta. Af hajiya yau dai kinji kin gani da idonki kuma hjy maryam tana kokarin kare danta ta aibanta min tawa yar a gaban kowa. A,a Kura inza a fadi gaskiya kowa yaji sanda kika fara aibanta mata da kafin ita dan galadima ya fada don shima yana zaune tunda taron na dakinsune iya su kadai aka kira a lokacin. Au kun yarda ke nan zaku hade min kai su aibanta mi ya anan a,a fa ya kara fada zaici gaba da magana hjy mai babban daki tace kuyi min shiru don Allah da wanan abin kunya da kukeson jawo min a yanzu. Duk wanan abin ke kura ke kika jawoshi bayan nagama magana meya kaiki tofa wani zance kuma a baya koma meye yanzu ai yarki taja komai ta dauka duk tabar gazan da tayi a can wajen karatunta kafin su korota ba a sani bane ? Yanzu anbar kiwon dabbobi an koma kiwon mutane yan adam duk abinda kakeyi da masaniyar mutane akanka don haka ku kama min baki anan. A haka suka watse saidai ba a san a inda zancen hadin ya tsaya ba a yanzu don hjy kura ba kyalewa tayi ba asalima tana ta faman shiri a bangareta yadda hjy Nasare ta kyankyasawa su umma labari. Dad ya fada mai komai hakan yasa ya murmusa don tuno da rabuwan nasu da tsohuwar kakansa fitinana tare da fadin trouble woman ya furzo da iska. Kafin ya koma tunane anya hukuncin daya daukarwa rayuwansa yayiwa kansa adalci kuwa bafa Allah bane ya haramta tsakaninsu camfi ne kawai na yan adam hakan. Duk lokacin da irin tunanen nan yazo masa abinda yake tambayan kansa shine meye laifin irin yayan da aka haifa ta wanan tsigar da sune ke ganin ukuban hakan a karshe. Don gashi kai tsaye yarinyar nan take fada mashi bata da asali wani irin rayuwane wanan itama mahaifiyar nata ina ta shiga ta gudu ta barta kamar uban. Photon yayi zooming ya kura mai ido na dan lokaci kafin ya sauke wani irin zuciya acan kasan zuciyarsa ya furta Allah ya zamo gata a gareku baki daya masu irin laluran nan shikan a nasa irin tunanen baiga aibun kulla wani halakan arziki da irin yayan nan ba gaskiya. Kamar yadda hjy mai babban daki da hjy kura suke kokarin kushe yar mutane akan asalinta duk da basu san halakan dake tsakaninshi da ita ba amma su suna daukan hakan da wata manufa wanda bashi ba. Karshe dai haka kawai yaji kasala na sauka masa sai faman tunane yakeyi shi kadai a gida ya kasa fita. Ranan sai ya ji gaba daya kasa fita ko ina abu daya ya tsaya mai azuciya shine zai taimakawa rayuwan yarinyar nan kota halin kaka. Kada ta nakasa tazo ta wullakanta a banza duk yadda zaiyi alkawari ya daukarwa kansa kan hakan tun farko tun daga ranan da hjy umman su salman tayi masu sharhi akan irin yadda rayuwan hakan sukan kasance a karshe. Balle wanan din da yaga tana da kyakyawan niya zama abin kwarai a rayuwanta don haka yayi alkwari zai taimaka mata tun daga wanan ranan sai daddy shine yasan wanan niyar nasa tun lokacin. Bayan haka yana son ya taimaka masu ako wani bangaren rayuwa yadda iyayyen rikon nata ba zasu taba jin sun gaza da ita ba irin tunanen da yayini yanayi ke nan shi kadai a gidanshi. Aike kan muzo gidan Rabakaya tun aika Asmau da nayi da kudinsu na amarcin su ita kuma iyayi yakai ta ga fada masu ba zan sake zuwa ba Abbu yace har dani don yawan takuran da saratu take min. Shine hjy su Anty fati take ta min aike har wurin Ammah ayi hakkuri abarni inzo dan Allah amma naki fita saida akai sallah azahar na shirya na shiga gidan a lokacin yana dam da yan buki . Ko kwaliyana ma abin kallone ga mutane don haka na zamo masu abin kallo dakin hjy umma muka fara shiga muka gaisheta nan take min fada da nan gidan mune saboda da saratu ba zan daina shigowa ba. Karshe dai muka mike da wanan yar ta yaya habib data leke min tun shigowana dama suna falo ne ita da uwarta dake kwance tana ganina tazo ta rikeni muka danyi hira da ita tana fada min sunan ta da sunan makarantanta irin dai hiran yara. Da zamu fita zuwa dakin amare kuma ta lake saita bini uwar tana riketa umma tace ki barta mana yarinya nason bin yan uwa kin riketa ? Idan ta zauna a nan wani abu zatayi maki ai gara dai tabisu taga gari tunda Aeesha ba bakuwa bace yar gidace sam banso zuwa da ita ba yadda uwar ta kankame abinda cikin daki. Amma maganan umma yasa na kama hannun yarinyar muka fita tare zuwa dakin amaren samira na fadin walle da bakizo da yar shigiya ba ta rike kayan ta mana waddamu da ita ? Ni dai dariya take ban haka muka shiga dakin yana dam da yan mata sun baje suna cin taliya group group mukai sallama muka shigo. Yauwa ga Aeesh din ina zubaida da tace bata gane Aeesha ba wai ita bata sanki ba saudat ta fada anty fati tace da ita aiba kowa yasan Aeesha ko unguwar nan saboda basu wani dade da dawowa nan ba. Ai yar gidan yaya Habib ce ashe saudat din ta kara fada wai ya akayi uwarta ta yarda ta biyo ku wanan yar da ake rowanta kamar tafi kowa. Sunga wace tafisu class mana wata ta fada kafin su fara min bissimillah muzo muci abinci ana faman kus kus kus a kaina duk da gamu a cikin dakin lokacin. Yauwa Aeesha zance dinner nefa akeyi kinsan wurin special ne ba kowane zai tafi ba ga yan gida sun nace kowa na fadin shi zai tafi. Zaune nakai ina fadin ai sunsan wanan ba tsarin mu bane gidan ango keda wanan tsarin don haka ku kyale kowa kawai idan sunje an hanasu aisa dawo kawai. Yau akwai butar kashi saratu ta fada daga inda take zaune tana fama loda taliyan a cikinta kai kanawa akwaisu da son filawa Asmau ta fada. Kuko dawo ko wata ta fada tace aigara dawo hatsina yana kara lafiya a jiki shiko filawa fa ko can dinner kuka tai shi za a zuba kuyi ta kwasa daga nan in kunga taliya kun rude barauniya ta shiga harka ta hade sarkokinku dana amarya duka ta nade tayi tahiyar ta kuna can kun rude kan hilawa. Dan hausa ba haushene rabu da bassakwacen mutum duk abinda ka fada yasan mai kake nufi amsan tabawa saratu a take da take fadin akwai kaza yau. Nan sukaita cacan baki nikan surutunsu yana hawa min kai hakan yasa na riko hannun yarinyar nan muka fito da maryam wajen gidan. Wai bakizo da motarki bane maryam ta tambaya nake fadin haba dai nan da nan zan wani dauko mota kuma ? Wai me Asmau nan naku ke fadane naga saratu tayi shiru nace koma me take nufi Asmau ta fita dabanci wallahi nima nan tsoronsu nake ji dukkansu biyun. Suka kwashe min da dariya Aimana ke fadi nima nayi mamakin ganin yadda kuka shirya dasu yanzu wallahi ? Haba dai yau da gobe basai Allah ba ana waje guda kuma yan uwa sai tayi shiru bata kara tofawa don ba zan bada kafan da zatayi tsegumin yan gidan mu dani ba. Photo suka farayi da waya kafin nima in shiga muyi tare harma da wasu suna shigowa nayi da yarinyar nan sosai don tana lake dani ko ina sau biyu uwar na turowa ana fada mata muna tare Can naji wanan yar na kokarin fisge hannunta daga rikon da nayi mata don kada ta bace min a cikin taro nawa ya sameni ashe babanta ta gani saida na waiga naganshi ya faka mota gidan massalaci yana zaune a ciki abinka da naka wai har yarsa ta gashi ita. Asmau nayiwa magana ta mikata wajen uban ta rikewa yarinyar hannu ta nufi inda yake tsaye takai masa yarinyar nan yarinyar ke fada mai cewa tayi photo da sabuwar anty din can. Nan ta dinga masa hira wai zatayi photo da uban dole yasa azo a kira mu sam ban dauka mu duka yake kira ba saina tura Asmau taje. Sai gata ta dawo tana fadin yace muzo na nuna kaina irin na mamaki kafin nace muje din a zatona zaice wani abu ya faru da yarsu ne. Saidai muna zuwa yake fadin tace kunyi mata photo take son nuna min sannu wazan baka so a jikinka kaga murde muna kunnuwa yanzu zaka nuna muna son yar cikinka a fili na fada a zuciyana Yar bakin nan Asmau ke fadin da wayan mummy Aeeshace akai