← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 101

Sashe 90

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayar akawo mata tsarabansu . Naji ya kira kaninsa da sunan Nazir bude boot din nan ka tayata daukan zuwa ciki ka gaidasu lokacin idan ka shiga don Allah . Lokacin nayi magana nace ai daga mamata sai mu da antyna ne a gidan Abbu ya tafi kasuwa tun safe sai dare zai dawo yace next time don Allah . Next time idan mun dawo zamu shiga ya sake fadan hakan na dauka dan leda zan gani sai naga sabanin hakan don ko kayane sosai a bayan motan ake fitarwa a lokacin. Su drinks su galon din turkey taliya macaroni kayan shayi sabule omo da dai tarkacen daba zance gasu ba a lokacin a cikin ledan suke ban san meye a cikin shiba. Nace wai duk wanan tsaraban mune haka amma kasa hjy wahala da yawa aimin godiya don Allah wajen hjyn mu din duk da nasan yadai fada ne kawai kilama bata sanda kayan ba ita. Can Asmau ta kara fitowa da basket din da aka shirya abinci a ciki tace Ammah tace nafito maku da abinci kuje kuci a mota tunda kunki shiga ciki kuci . Kai mama nason wahala haba dai har sai an biyo mu da wani abinci kuma haka ya zama wahala ai nake gani . Na tare da fadin amma kasan ba zakuzo ku tafi hakana ba bakuci abinci ba fa a gidan mu gaskiya duk da baka sanar damu ba balle a shiryawa zuwan naku ? Amma kince baki san da zamuzo ba yau nace wallahi kunyi sa,a an dafane daidai da zuwanku ai shi Nazir din ya amshi basket din daga hannu Asmau yana fadin angode kinji. Zata tafi samira ta fito da kayan drinks tana gaidasu itama ya amsa cikin kulawa mun dan taba hira kafin ya kalli agogonsa yana fadin a fadawa Nusaiba ta fito mu tafi. Kada muyi dare a hanya don hajiya taja min kunne na dawo mata da yayanta kafin magariba yanzu fa two ke batun yi matazun . To ya na iya zamu gidan wata sister din hjy daga nan shima wanan abokin nawa yana son ganin wani abokinshi ne . Sun takura min da banzo dasu ba kinga ina nan har magariba ina kallon sahibata don ba gajiya zanyi da kallon ki ba ai. Muka dan kara taba hira dasu nake fada mashi zancen zuwa IT da zanyi abuja ya nuna jin dadinsa har kanin nasa na fadin aida kaduna nazo in zauna gidansu. Nace haba dai Nazir gara dai kada ai hakan nashiga na samu wanan yar uwar nasa har tayi sallah muka dan taba hira don suma sun tafi suyi sallah din a lokacin. Nan na daji wani labarin shock a bakinta take fada min ai wanan yar da suke tare diyar S matazunce amma basu tare da mamanta a yanzu. Nayi ta satan kallon yar tana da dan kama da mahaifin nata gaskiya da zata tafi na dan hada mata abinda Allah ya sauwaka min a lokacin tana ta murna muka rakosu gaba dayan mu kofan gida. Nazir din yana ganin mu ya fito da kayan abincin ya mikawa Asmau yace ga goro nan yayana yace a baki agaida mama kuma mun gode. Suka ja motarsu suka tafi kafin nayi a jiyan zuciya mu koma cikin gida ina shiga anty safiya tana bude kayan tana fadin wai wanan yar da sa,an samun maza kike saidai matsalan abin da sunji kome ke nan sai su gudu. Mijin daine baizo ba ai idan lokaci yayi mijin na gaskiya yazo kome ake fada akanta ba gudu ba saida ya matso wanan cikin jerabawanta yake haka a rubuce. Wani yana da komai din a rayuwansa amma kare ma baija balle ya sunsuna ai abin baiwane daga Allah Ammah naji ta bata amsa hakan. Ta dan tsuke fuska kafin tace niba wani abune nace ba ai mama ganin dai wanan abin kamar za a bude shago dasu yasa na fadi hakan ai. Shine ai na baki amsa daidai da maganan ki laifine kuma yanzu kai don Allah waga maganan ai baiko dace ba wallahi mi ar ranan shi yanzu karshe fa duk mu zamu amfana da kayan da a wuringa to mezaisa ki fadi waga magana don Allah ? A ikon Allah kuna dai son ku juya min zancen da wani ma,ana ni yanzu gidan nan banfi kowa moriyan Aeesha ba tunda komai nata bai wuce yaranga ? Hanyan daki na nufa kai tsaye kafin inji Asmau tana magana kasa kasa tana fadin mi da kika waga tabi,an ne mama wallahi dai wanga abu baiyi ba wallahi. Kayan bukatuna ta kwaso a cikin kayan irin su manshafi sabule turare da wasu abaya da english wear dake cikin wasu ledoji ta shigo min dasu dakina. Koda ta shigo ta samu nayi alwala na fito daga bayina bayan na kara wankewa take fadin mummy ga kayanga da naga kanwarshi a daki na ajesu a gefe daya falo dazun . Sallah zanyi Asmau banyi sallah ba tun dazun ga la,asar ya gabato jiki na fara harama tayar da sallah hakan yasa ta dora min kayab saman gado tafita. Koda na idar tagama sabon abincin data dafa jeloup din shikafa tayi muna sai sauran ganyen data zuba muna a sama tare muka zauna mukaci da ita lokacin samira ta shigo. Take fadin wasa tare ci bambanko gara da Allah ya kawoni nishigo ke kwasowa mummy na sama ke barmu da gaya can zama tayi muka hada hannu da ita. Can naji samira din tace mummy an kiyi hakkuri don Allah da maman mu kesan halin mama haka taka hwadin magana kai tsaye bata taunawa wani lokacin. Samira yau idan ba Ammah wa nike dashi bayan su anty safiya daku a duniyan nan ni naga gaskiya ta fada ai ba karya a cikin zancen ta. Haka mazan suke kwana biyu daka sake da mutum yanzune zakaga ya gudu kuma bai sake dawowa ni banga abin haushi ba a ciki ? Amma mummy ai bai kamata haka ya fito bakin mama ba ko yau duniya ita damu wa muke dashi da zai muna waga abin da muke samu ta sanadinki haka don Allah dai ? Yanzu fa zancen karatu kike muna waya tuna damu duniya har yasan da haka garemu inba keba ai fatan alheri ya kamata yanzu ya fito a bakin mama wanan lokacin gareki kuma. Ke gani nan duk abinda wani zai fada kan mummy a yanzu ni baya shigana ko yaro na goye yasan mai kyautata mashi ai balle mama halintana haka kawai. Mummy ma bata damu da waga zance ba ai haka dai mukai ta magana har muka gama kafin mu koma kallon kayan daya kawo muna din . Naso in kwanta bayan la,asar sai kuma naga rashin dacewan hakan yasa nake gyara daki mu shiga gidan akwai wajen su maryam da farida. Muryan yaro daga waje yake fadin wai ana sallama da Aishan gidan nan inji Auwal cak na tsaya ina maimaita sunan nace Auwal Auwal fa ? Filon dake hannuna na aje na saba gyalena na fito Auwal din ne kuwa cikin wata farar mota mai kyau yana ganina ya fito yana washe baki na daure fuskana lokaci guda. Haka ya karaso yana fadin ni dama ai nasan mai laifi nake a wajen ki Aisha tun wacan lokacin ban kara lekoki ba zakice don oga Bash baya kasan ne yasa hakan ?. Ummm,humm Auwal ke nan ina gajiya ya amsa da lafiya kalau ya kwana biyu ya karatu kuma nace Alhamdullahi . Yau dai nasan in nazo ai dole na jiki tunda shirun yayi yawa haka Auwal na katseshi da fadin kaima kazone ka ci min mutunci ka fada min magana yadda Salma ya fada min kwanaki ? Salman salman fa kikace Aisha nace kwarai ya fada min maganan dako makiyina banyi tsamanin zai iya fada kallona ido da ido yafada min shi ba . Yayine don yana ganin banda gatan da zan iya kwatarwa kaina yanci kome saukin abin dai koda yace kwadayi yasa na bawa Man Bash kaina yayi amfani da daman shi akaina. Saukin abin ba amfanin iskanci yayi dani ba daiko amfani na hikima irin nasu na mayaudara yayi min a lokacin ? Saidai duk da ban fahinci amfanin da yake nufi yayi dani ba abindai da sauki bisa a ce yau iskanci na shashanci yakeyi dani ai a karshe ya gujeni kuma. Wanan wani zance da wani dalili nasa can da ban sani ba kuma hakan ya faru danine a cikin,,,,, Don Allah dakata Aisha shi salman din da kansa ya fada maki wanan maganganu irin haka ya tsureni da kallo nace zan masa kazafine ? Tunda a girme dai salman ya girme ni nisa ba kusa akan me zan masa karya don naga baya nan yanzu kome zaisa nayi masa karyan hakan ko kazafi ? Zancen kazafi ai bai taso ba zancene naji kaina ya daure da jinsa don yanzun hakama ogane ya turo ni inzo in kawo maki sako wallahi Aisha . Sai shekaran jiyan nan na wallahi na dawo garin nan ina can oga ya turamu wani aiki a cikin kwanakin nan da kika jini shiru . Au yanzun ma ya dawo ke nan yayi amfanin dani a karo na biyu ke na ko me ? Saidai niko a yanzu sako na fito in baka ka isar masa da cewa ashe dan tallakama yana da ranansa don shine na fito a yanzu din daba zaka taba ganina ba kuma again tunda na gane yaudarata kukeyi ashe ? Sai naji yace dani dakata Aisha ki saurareni don kina kara ban mamaki a cikin zancen nan a yanzu . Yadda yace din dani na daka nayi cikin kura masa ido inji me zai fada min lokacin sai naji yace zancen yaudara ko wani abu a tsakanin mu kinsan wallahi babu shi alkawari na daukarwa kaina da hakan. Kema kin sani tun farko wallahi balle shi oga bash a rayuwana tunda na sanshi ban taba jin wani mahalukin da yace bash ya cutar dashi ba tun tasowan mu har yau din nan sai ko yau a bakin ki da kika fadi haka har naji kuma ban yarda ba. Duk da nasan ba halinki bane akasi aka samu ko a yanzu din sai
Chapter 90 · 0% Book details