← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 101

Sashe 2

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani lokaci mutum ya kanga kamar kaddaransa yafi na kowa girma a duniya saidai da zaran kaji shakuwar wani zaka dauki naka ai ba komai bane kadan ne bisa ga nawani haka duniya take dama. Irin hakan yakan damu Aeesha a kullum a zuciyanta dan har hakan yakan hanata fita wani lokaci don duk da anan ta taso gaban yan uwanguwa haka bai hana a kullum idan ta fita sai an nuna taba kamar yadda yake al,adan mutane ako ina indan sunga wani bakon al,amari ga mutum. Wanda hakan ba farko bane a gabanta ansha nuna ta ko taji ana bayar da labarinta a cikin kus kus wanda hakan yakan matukar bata mata rai wanan tasa ta tsani fita a rayuwanta sai yanzune kuma tasa dalilin hakan da mutane ke yawan mata. Asali dai zamu iya kiramta da diyar mace ce don irin yaran nan da matan muna arewa ke zuwa kasashen larabawa su samo cikin su ko bayan haihuwa sai su dawo gida su jibgesu a nan gaban iyayye ko wasu dangi suna walagigi da ganin taskon rayuwa a cikin al,umma don basune da laifin ba amma hukuncin laifin karshe saiya koma akansu su yayan. Mai karatu zaki san labarin irin yayan nan da basuji ba kuma basu gani ba don akwaisu a cikin kasashen mu harma da ta wajen sauran kabilun mu duk ana samun irinsu ta dalilin zuwa kasashen wasu neman kudi ko wani abin ita a Aeesh ta kasance a cikinsu nata kaddaran rayuwan ke nan da aka haifeta a hakan. Wanan yasa launinta yake daban da namu na bakake don ita ta kasance yar ruwa biyuce rabi bakar fata rabi kuma zamu iya kiranta a takaice da yar balarabiya. Aeesh ta kasance yarinya mai tarbiya da rikon addini don irin tarbiyan data taso a cikinsa tarbiyane tsatsan irin wanda akeson iyayye suba yayansu. Gata ta kasance yarinyace mai kwakwalwa a wajen ko wani irin karatu na boko dana arbiya bata da girman kai amma yawan kamun kanta yasa mutane ke mata hangen girman kai da jin kanta ita din watace a yanzu. Wanda ba hakana bane zalla kamun kaine yasa take mayar da kanta gefe cikin tsaranta akoda yaushe don gujewa gori ko wani abu makamancun hakan.l Bata taba sani asalin ta ba amma dai tasan duk yadda akayi akwai wani dalili data fito daban da mutanen nan nahiyar da take ciki don har yar balarabe wasu daga cikin yan makaranta suke kiranta dashi wanda hakan yaso batar da sunanta na asali a yanzu. Duk da hakan dai komai na Aeesha namu na hausawane don ba wani dabi,an larabawan da ake danganta ta dasu da takeyi illa kawai zamuce Launin fatane kadai ya banbantamu da ita. Batason hayaniya don in kaji muryan Aeesh lamari ya baci don bata iya fada ba idan ranta ya baci kuma tana da karfin zara saboda kaf unguwan cikin sa,annita ba wace ke iya kayar da ita hakan yasa ta dan samu sauki kan hattaran har yanzu data dan tasa take abokai a cikin unguwar duk da ba wasu abokai bane can data makalewa sai ma mutum daya zuwa biyu. Ta dawo daga school ta samu Ammah zaune tayi tagumi kamar a cikin yanayin tunane don sallaman tama kamar a cikin damuwa ta amsa mata shi a lokacin. Saida ta shiga daki ta kwabe tufafinta na islamiya ta fito ta zauna kusa da Ammah din tana fadin lafiya dai Ammah na ganki haka ? Kakar nata data kira da Ammah ta dago kai tana kako murmushin dole a fuskanta tace lafiya kalau Aeesh tunanen duniya nakeyi a nan ke dai. Nisawa tayi da har sautin sa yana iya fita take fadin Abbu bai dawo bane tace ai kinsan lokacin dawowansa da dan saura . Mikewa tayi don ta gyara madafinsu don jiran tsamanin dawowan dattijun data kira da Abbuh din wanda yake uba kuma kaka a wajenta yanzu. Don sai dattijun ya dawo in kasuwa tayi sa,a ya sayo masu dan abinda zasu dafa aci a gidan in kuma ranan ba sa,a suyi hamdala ayi dan dabaran mata aci kar a kwana da yunwa. Ta saba da wanan don kusan sai ince dashi ta bude ido kuma har ta saba da hakan maimakon suga Abbu da suke sakawa ran dawowanshi a lokacin sai sallaman bakuwa sukaji daga kofan shigowa gidan. Da murnanta take fadin lah maman Gwarzo ta mike zuwa taron ta ta karban mata kayan dake hannunta din a cikin murnanta tare da nuna jin dadin ganin bakuwan nasu. Wai yatace tayi wanan girma haka bakuwar data kira maman Gwarzo take fadan haka tare da dan murmusawa tana fadin tubarkhaka masha Allah ina angama karatun yanzu sai aure ? Karatu da saura kadan ta kusa kammalawan dai itama ta huta kamar kowa ai kayan ta karba ta shiga dakinta dashi tunda tasan a nan zata sauka don gidan nasu dakuna biyune kacal a cikinsa sai ban daki sai madafi dake can dan gefe daya na kwana da Abbune ya gyarashi haka saboda wahalan da sukeyi lokacin ruwan sama a gidan. Daki Aeesh ta shiga dan kudin taranta da bata kashe ba ta dauko ashirin ta tafi nan wajen mai shago ta karbo ruwa ta kawo mata tana fadin mama ga ruwa. Wace ta kira da mama din ta dago tana fadin yauwa yar albarka sanni da kokari Allah ya nuna muna mun ksiki dakinki lafiya a zuciya ta amsa da amin. Ta nufi kitchen din nasu ta fara shara don rage aiki yayin da matan duk suka bita da idanu lokacin matar ke fadin har yanzu dai Nana shiru ba labarin ta. Ammah cikin rage sautin muryanta take fadin bari anjima mayi zancen da dare da dabara ta hada wutan ta doras tukunyar ruwan zafi don tasan tuwo daine zasuyi a lokacin. Haka tayi ta yan aikace aikacenta har lokacin da Abbu din ya dawo anyi sa,a kasuws tayi kyau a ranan don haka da ledan cefanensa ya dawo gidan ? Ta taresa da murna ta karbi kayan takai gaban Ammah din yayin da shi kuma ya jingine kekensa yanawa bakuwarsu sannu da zuwa matar nasa kuma tacigaba da bude ledan da yarinyar ta kawo gabanta shimkafene ya auno sai kayan miya da yan kassa na tsotso da zasu watsa a miya aji dan zaki badon asan anci nama ba dai. Kafin wani lokaci ta hada girki da taimakon wanan matan gidan Ammah sun kwashe har ankaiwa bakuwa nasa Abbu kuwa ya fita zuwa masalaci bai dawo ba koda ya dawo din dabi,an nan na mutanen da har yanzu sunayinsa shida makwabtansa na kowa ya fito da abincin gidansa a saka hannu gaba daya aci . Wanan yasa makwabtakarsu har yanzun yake da karfi don al,adace ta rufawa juna asiri da mutanen baya sukeyi wanda a yanzu duk an watsar da wanan al,adan a cikin unguwa kowa yaci bidansa shi kadaine yanzu. Missalin tara da rabi a zaton matan yarinyar na barci don ta kwanta tun wajajen takwas da rabi a dakinta hakan yasa Ammah fadin . Dazun kina zance ina kauda kai kinsan har yanzu Aeesha bata san asalin ita wacece ba duk da nune da gorin da mutanen garin nan ke mata har yau ban fada mata komai akanta ba. Ita kuma Nana duk inda take inda rabon mu gana wataran zata tunomu ta dawo gida don har gobe ina kaiwa Allah kukana kan lamarita . Jin hakan yasa Aeesha din lafewa don ta dan tsunci wani abu daga bakin matan biyu saidai har lokacin da maigidan ya shigo zancensu akan wace suka kira da suna Nanace. Nan kuma taji Ammah nayiwa mijinta bayanin dalilin zuwar yar uwata din tazone kan saida filin gadonsu da yan uwan haihuwansu keson yi a kauye bada saninsu ba. Shine tazo suje ayi wada za,ayi kafin wajen ya salwanta ya fita hannunsu saboda an mayar dasu mata ana son yi masu yau hakan yasa taji Abbu yace goben nan ta shirya su isa kauyen asan fita kan zancen. Inma ya kama a sayarne abawa kowa kudinsa zaifi sauki sai su karbo nasu su ukku suzo nan cikin birni su samu filin da zasu saya a madadin wancan din. Hakan yasa washe gari bayan ta shiryane taji Ammah na fadin Aeesha koda zaki dawo zaki samu ban gida don zanyi tafiya a yau zuwa kauyen mu wani lalura ya taso min don haka. Ki shiga wajen tabawa nayi mata magana ki zauna a nan har zuwa yamma in malam ya dawo don ba lalai bane in dawo yau ko gobe saidai yadda abin ya kaya a can din. Dan marairaicewa tayi tana fadin Ammah baki zuwa dani inga garin ku kowafa yasan garinsu nice bansan nawa ba ko yan uwa ban san kowa ba. Kiyi hakkuri Aeesha da sannu zaki sansu nan gaba ai komai ya kusa zowa karshe nake gani a yanzu zaki dawo da yamma son girkawa malam Abinci kada ya zauna da yunwa kinsan halinsa dai. Hakan akayi ta fita daga gidan ranta a bace don gaskiya dolene hakan tunda Ammah bata zuwa ko ina ko garin nasu yanzu sau biyu ke nan taga taje wancan karkn gaisuwa ta tafi sai kuma yanzun din banda maman gwarzo bata san kowa ba a dangi dai da zata nuna ga dan uwanta. Haka takai makarantansu ranan dai har aka taso bata ganewa kanta ba makin tabi shawaran Ammah djn taje gidan tabawa sai ta kwamacewa ta zauna gida tayi yan gyare gyare gyaren gida a lokacin. Da tsakar gida ta fara har ta gangara zuwa bandaki madafi har wajen gidan dama gidan ba wani girma ke garesa ba don hakane taji saukin aikin har ta karasa yamma baiyi ba. Hakan yasa tayi shawaran gyaro dakin su Ammah din tarkace sosai ta fitar a dakin can kasan gadon amma din ta kwakwalo ta sharo wani leda da aka nadesa sosai harda dauri. Don haka taga ya dace ta bude ledan idan ba abin amfani bane a cikinsa ta hada da shara ta zubar saidai yadda akaiwa ledan dauri yasa tagane abune mai muhinmanci a cikinsa. Sannu a hankali ta warwale ledan taga alaman photunane ciki ta zarosu tana dubawa a hankali tabi na cikin hotunan da kallo. Wata macece rugume da yarta
Chapter 2 · 0% Book details