Sashe 28
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ni malam aiba nace wani abu bane kada dai ita nana din ta dawo kuma babu kayanta an batar dasu kaga hakan ba zataji dadi ba ta bamu amana munci ke nan. Din wa take turo wanan kayan a nan yanzu ina dai don yarinyar nance amfanin karatunta baifi na ajiyan sarkokin nan ba ashe Ammah? Tayi shiru hakan yasa na mike tsam na koma daki sarka dai guda ukkune banga dalilin aje wanan kayan ba ga bukatansu ya taso mutumin nan yana iya kokarinsa wajen ganin ya ban kula da karfinsa da abinda Allah ya hore masa amma kamar Ammah bata duban hakan ita. Irin wanan tunanen na kwana dashi a raina da safe da Abbu zai fita rakani na dauko maganan inda na kara bashi shawara yace zai duba insha Allahu. Don sam baison kan abin duniya ya samu matsala da uwayena Allah zai bashi mafita insha Allahu duk da hakan ban dadara ba na daiyi shirune a lokacin. Bayan na dawo kuma na kara tuntuban Ammah kan zancen sai cewa da tayi dani ta gane ina son hadata da mijintane da yar uwarta. Nakan zauna inyi mamakin irin tsoron da Ammah ke ji akan nana wani lokaci Abbu dai bai taba kayansu ba kuma bansam yadda akayi ya samu kudi ya saida gidan nan da muke ciki ya cika ba duk a cikin dan kakanin lokaci. Sai ji nake ana fadin wai zamu tashi daga unguwar nan da muke ciki hakan yasa muka kara matsa kusa da unguwar yan uwansu Abbu don zan iya cewa a unguwa dayama muke yanzu dasu. Abbu sam bai iya mikani daya daga cikin gidajen yan uwansa in zauna yace don yan uwansane shiya san halaiyan kowa da ace ni yarsane ta cikinsa da zai iya yin hakan gareni. Da dai wasu dalilai daya barwa kansa sani ya sayar da gidan nasa muka koma sabon wuri amma Ammah kance wai akan dalilin karatuna da baida amfani karatun mace da yake ragage gareta tunda aure zatayi. Sai gashi dawowan mu nan sabon wajen a yanzu Ammah din tafi kowa jin dadin hakan saboda sana,anta takeyi sosai a unguwar kuma ya karbu don tana saida kayan miya. Tana dahon taliya tunda safe kuma tayi na rana haka na marance yara harda manya suna shigowa sosai saye sai ya kasance kamar mun shigo da sa,anmune cikin unguwar. Karatuna yanzu kuma yana cigaba sosai don kaina a kullum kara budewa yakeyi don banda wasa haka nake raba dare ina karatu sosai don kare mutuncina. Nan yan uwa suka fara dan kus kus akan dawowan mu nan din don sunyi mamakin yadda za ace Abbune ya sayi wanan gidan da kudinsa wai kullum yana yawo akan keke. Shi dai Abbu din yakayi murmushi kawai idan suna zancen a gabanshi don ba huruminsu bane da dole sai ya zauna ya fada masu illa iyaka shidai ya barwa Allah sani don baiwane daga Allah hakan gareshi. Cikin haka mukai hutu makaranta don dama koda naje an danyi nisa ga karatu lokacin don hakane nayi dan watani muka samu hutu. Sai lokacin na fara tunanen wani makaranta zan jona islamiya don ci gaban karatuna a lokacin akwai gidan wani tsohon mai kudi dake da wani babban islamiya can nacewa Abbu ina son a kaini naci gaba. Inda Abbu yaji dadi sosai da wanan shawaran tawa baiyi sanyi a gwiwa ba ya kaini saidai irin kalubalin dana samu a wacan unguwar shina samu a nan din na yawan kallon da nake sha gun mutane balle a yanzu dana zamo yar matshiyar budurwa. Ko a jami,a hakan nake samun wanan matsalan dasu wasuma a gabana zasu dinga gulmana saukin abin banda abokiya ko wani kungiya ni kadai nake karatuna da komai . Gashi ko wani malami yayi aiki zan haye don maida kai da nakeyi har sauran yan uwan karatuna suka fara zargi waiko dai suna banine wani malamin mu dan dattijone ranan da yai muna aiki na samu yace bai yarda ba saina fito na wanke kaina gareshi . Haka na fito din nayi solving a gaban kowa tun daga wanan ranan suka daina zargina ga malamai na samu saukin hakan garesu.