Sashe 65
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaye take rike da labulen window tana shakar iska yanayi na subbahanahu wata,ala a dake saukar mata da ni,ima a lokacin cikin jikinta tare da saukar mata ds natuwa a tattare da ita. Hakan ya farune saka makon yawan msfalkin da takeyi cikin yan kwanakin nan wanda a sanadi hakan ta kasa samun natsuwa. Hasken ranan da yaiwa fuskanta yawa a yanzu yasa ta koma ta zauna tana mai bin dakin da kallo kamar tana neman wani abu a lokacin. Idonta ya tsaya cak saman drower saidai kasala yau ya hana ta jin dadin jikinta ga baki daya ga wani yanayi na bakin cikin haka kawai da take ji ya tokare mata makoshinta a lokacin tare da hanata sukuni. Ido ta runtse a cikin yanayi take abinda ya shude shekara da shekarune ya biyo mata a rai lokaci guda wanda bata san lokacin da hawaye ya sauko mata ba jin karan bude kofa yasa ta bude idanu mai aikinsuce wata yar togo ta shigo dakin dauke da shayin da ya zamo masu al,ada sai kasha shayi kafin komai tunda farar safiya don watsake jijiyoyin jiki tare da samun kuzari. Ta aje shayin kafin tace da ita Oummu Banna Kaifa Subbhi ta dago cikin yanayin kasala tana amsa mata da Subbhi bil hair ya bintu kudirat Ga shayi na hado ko zaki bukata kafin abinci tace Shukuran bintu kudirat ya kwanan yaran kuma ina dai ba matsala komai ko ? Tace Alhamdullahi lafiyansu kalau sun tashi suna shirin school driver kawai muke jira a yanzu yazo masha Allah sannu da kokari ta fada karo na kusan uku ga matar dake duke tana tsiyaya mata ruwan shayin da zalla ganyene akai amfani dashi sai kayan hadin kamshi da ya dan bashi dandanon dashi ba zaki ba shiba dandanon ganyen nasa ba don basu damu da sugar ba su. Wani gaisuwan karo barkatai tayi mata ta fita cikin jin dadin yadda uwargidan nasu take kula dasu tankar a gidajensu suke zama. Ajiyan zuciya ta sauke bayan fitar matan daga gidan ta mika hannu ta dauko ruwan shayin dake turiri a cikin cup saman table. Baki takai da zumar sha yadda ta saba kurbi daya taiwa ruwan ta sauke da sauri daga bakinta don gabanta daya fadi ajewa tayi tare da dora hannu saman goshin ta ta dafe na dan lokaci . Ta jima wajen zaune kafin karan wayarta ya dawo da ita cikin yanayinya firgigita sauke hannu tana bin wayan dake faman ringing saman gado da idanu har ta samu ta mike da kyat ta dauko wayar nata. Wanda take zaton ya kiratane shi din ya kira kuwa ta dauka tana karawa a kunnenta muryansa mai taushi na larabawa ya sauka mata a kunnenta lokaci guda. Ido ta lumshe tare da fara gaidashi ya amsa cikin jin dadi tare da tambayan lafiyansu dana sauran jama,an gidan. Sundan jima suna magana kafin suyi sallama ta kashe wayar nata a cikin kundura da zancen zakice ba ita bace akoda yaushe takan zauna a daidai wanan lokacin zaman jiran wayasa ba sai gashi a dan kwanakin ko wayar nasa bata kaunar taji yanzu. Hawayene masu dumi ya gangaro mata a saman fuska wanda tasan da zuwanshi don hakane batayi mamakin jinsa a fuskanta ba lokacin. Yar uwarta da take tankar uwa a gareta da wani bangaren rayuwa take mata gizo akoda yaushe a yanzu yanayin da take ganinta a mafalkin suna magana ya tsaya mata a rai ya hanata sukuni da jin dadin rayuwa a yanzu din. Kwance yake don ya kasance weekend hakan ya bashi daman hutawa a gida tun bayan sallah asuba daya samu yayi ya koma ya kwanta barci saida ya gaji ya tashi. Wayansa ya lalubo ya kunna ta bayan ta kawo ya fara neman mahaifinsa don yasan yanzu gari ya waye masu a nan saidai safiyane sosai cikin irin wanan lokacin yakan kirasu su gaisa dama. Saidai yau ya kira har wayan ta katse bai dauka ba hakan yasa ya hakkura da kiran ya fara shiga wajen sakonni kafin ya danna WhatsApp dinsa da bai damu da shiga ba ko wani lokaci. A gurguje yake bin sakonnin kafin ya kai kan wani photo daya dauke mai hankali tabbas Aeesha ce jikin photon babu tamtama itace a wajen buki akai hoton kuma bai tantama da cewa ba a cikin satin ake bukin ba. Photon ya kara zooming yana karewa yarinyar kallo kafin ya fara karanta abinda dake kasan photon na dan lokaci ya runtse idanuwansa a hankali. How comes suka samu photon yarinyar nan haka ya tambayi kansa kafin ya kara zooming ya kurawa photo ido na dan lokaci kuma shigar ba assha a cikinsa gashi kuma alama ya nuna tana cikin farin ciki alokacin. Kodai yarinyar nan ce take aure ya tambayi kansa bayan ya gama kallace hotunan kaf da sauri ya ba kansa amsa da no bai yuyuwa ina ya mike zaune zubur lokaci guda. Wani zufa da baisan daga ina bane ya feso masa a goshinsa duk da sanyin da dakin dayake yake ratsa jikinsa amma wai munafukin zufa yaji a jikinsa yanzu kuma. Ya jima zaune kafin ya mike ya shiga wanka bayan ya fito yana tsaye yana goge ruwa akansa ya dan tsaya kamar mai tunane kafin ya aje tawul din ya dauki wayar har lokacin tana kan photon daya tsayar da wayan nasa photon ya kurawa ido na dan lokaci kafin yaja tsuki yana yarda wayan saman gado. A gurguje ya shirya ya sauko kasa abinci ya samu an shirya masa zama yayi don yaci abincin amma zuciyarsa ta kasa samun natsuwa sam. Wacece ita yar waye agarin nan ko acikin kasan nan waye ubanta ita din kayi bincike a kanta bata kasance cikin tsaraban takaranci ba. Don babu balaraben arziki da zai jefo yarshi Nageria ta zauna haka cikin wanan kasan tare da wasu tarkancen dangin kala. Zancen shi dasu mami a falin mai babban daki na karshe akan Aeeshane ke masa yawo a kwakwalwansa lokacin haka kawai hjy kura tasa aka tarasu take masa wanan yankar kaunan a gaban iyayyensa . Hjy meya kawo wanan zance kuma yanzu magaji bai taba kawo wata yarinya ba da sunan aure a gaban mu har yanzu. Ai kuma hjy naga koda ta kasance ba yar kowa bace indai tana da hali walillahi,hamdu inji daddy tunda shiya ganta yace yana son abinsa ko. Matsalan ku ke nan maza da kuma iyayyen yanzu son diyanku sai ya rufe maku idanu kan halaka baku damuwa . Haka kuma da zaran kuna son mace idon ku sai ya makance ku kasa tunanen abinda kaje ya dawowa rayuwanku gaba sai idan kukai kwadan ku ya fada kuke komawa da kun sani wani lokaci hjy mai babban daki ta fadi hakan ga mahaifinshi da yai magana yana kokarin kare yarinyar da take zance a lokacin. Hjy naga in ma abinda kuke tunanene inhar hakan gaskiya ne meye laifin yarinyar a cikin zacen nan tunda ba itace ta aikata wani sabo ba balle a kyamace ta ? Kaiyya naka tunanen ke nan Ahmad na zata a shekarunka zaka san illan wanan abin a yanzu ba sai anje ba wata rana me zaku fadawa yayanta idan ta gauraya daku ta haihu da danka ? Hjy ai duk wanan abin baikai can ba ayi tunanen mafita a yanzu a gano ita din yaya take kafin a fara tuna zurian da zasuzo gaba. In ma har bata da gata aishi magaji sai yai mata gata Allah yai masu baki daya ina dama ko wani namiji shine gatan iyalinsa dai. Rufa min baki Ahmad da zancen kana banza na fahinci son dan ka yasa kana kokarin abinda zai zubar muna da mutuncin mu da kimar gidan mu nan gaba . Na fahinci Idon ka ya gama rufewa a yanzu kan son kai irin na nasara da ka koyo zamanka cikin su ni zaka jawa abin gori cikin zuria ta don kawai kada ran dan ka ya baci ? Ga yar asali jikan asali wace asali ya haifa ka tsaya kana son yiwa mutane wasa da hankali Hindu ce na zabar masa ita kuma zai aura nagama maganata ta fada tana wani kaiwa kishingide saman tintin din gefenta. Mikewa man bash yayi don ya fice daga falon saboda bai iya jure jin zancen tsohuwar nan na shirme a kunnuwansa donshi a shirme ya dauki duk zancen ta. Har ya kusa kai kofa zai fita din yaji tana fadin kaje duk inda zaka magaji sai ka dawo nan ka sameni indai nice. Aure da hindu ba fashi tsakaninku don na riga dana yanke wanan hukuncin babu kuma mahalukin da ya isa ya tayar da wanan zancen a cikin iyayyenka. Har yakai kafa zai fita din ya juyo ya tsaya don jin abinda ta fada ya kalleta yayi murmushi kafin ya kara tako biyu zuwa gareta ya nunata yana fadin . Gara dai da kika gyara zancen ki hajjaju don su kika haifa ba niba ya nuna iyayyen nasa dake zaune a gefe tsit kamar ruwa yaci su wajen. Don sunsan kwanan zancen duk wanda ya motsa cikinsu zata hada dashine tayiwa mashi rashin mutunci don haka kowa ya kama bakinsa yana kallon draman da sukeyi tsakaninsu ranan. Akidan nasara kuma da kikace munayi ni da ubana yanzune zan nuna maki an haifeni cikinsu da nasan akan wanan shirmen naki kika taramu don ki yi hakan wallahi da ban zan zo ba. Haka kuma indai Bashir ne ki sani ba zan kara zuwa nan don ke ba bance gidan ba a,a nan dai matukar kina raye a doron kasan nan mubar haduwa dake har abada tunda nagane son kai yayi maki yawa. Don ko a cikin yayanki dukkansu diyan kine amma kina zabe a kina nuna masu son kai balle wani. Tau ba zan dauki wanan ba zan kuma fadawa mijinki ya tsawata maki karo na biyu a kaina ko na dauki mataki da kaina. Ahmad's kana jin yankan kaunar da danka ke kallona yana min kuma a gabanku kuna kallonsa . Ai basu sukace ki kirani ba kuma ban yake maki kauna da kikace na yanke maki a gabansu ba, sai nan gaba . In har kikai gigin daura min bakar yarinyar can da sunan aure zaku rainawa kanku wallahi.