Sashe 91
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
dai abinda nakeso dake shine ki kwantar da hankali don Allah. Har zuwa lokacin da zamu gano gaskiyar wanan maganan me Salman ke nufi da hakan da yayi a gareki ? Shiru na danyi cikin nazarin zancensa kafin in nisa nace abin mamaki wanda ban tabo tunane ko zato ba saiga malam salman a gabana yana fada min wayan nan maganganun haka ? Audi ai bai fadawa talle hakan dake dashi dani da kowama yasan waye Oga Bash yasan mutumin kirkine akan meke zai damfareki karamar alhaki a dake wajensa . Idan ya damfareki Aisha yaci riban me ga yin hakan idan yayi maki yaudara ? Yaja wani huci yana fadin lalai Salman inda wani manufa ko wani ya turoka ka tafka babban kuskure a nan wanan karon don har Man bash yaji wanan akwai rigima a tsakaninsu gaskiya . Wallahi koda ya kirani jiya yana fada min sakon nan zai iso na tabbatar da kuma ya iso hannuna na kawo maki shi don zaki bukaceshi a yanzune. Saida nace a zuciyana lalai kina da wani kima da daraja da nauyi a zuciyar Oga Bash yadda ya ke magana dani a jiya din. Don haka har in kin yarda kibi wanan shawaran tawa ki bari mubi zancen nan a sannu mu gane meke faruwa dayasa Salman yin hakan . Amma kuma nafi kyautata zaton kamar dai wani ya turosa yai maki hakan don cin ma wata manufa na a raba alakan da ake tunane akwai shi tsakanin ki da Oga Bash. Na katseshi da fadin wace halakace banda kyautatawa da mutuncin dake tsakanina dashi da har za a iya turo salman yai min hakan. Yace ke kike ganin hakan Aisha kibar abinda baki sani ba akan baki sanshi ba tunda ba,a taba ganin ya kula wata ya mace ba a cikin garin nan saike a karo na farko. Ai koda ya kulani Auwal tsakanina dashi mutuncine kawai da girmamawa dan bai taba nuna min wani alaman so ko wani kalman banza daga gareshi ba. Asalima duk zan shiga wurinshi shi malam salman din yana a office din mafiyawan lokutan suna tare koda nake shiga din . Amma sai cewa yayi dani wai daga taimako na dauka man bash yana sona ne idan haka nake tunane na yaudari kaina. Har Inma wani abune nake tunane ai Man Bashi din ya biyani amfanin da nayi mada don haka kada in sake nemansa da sunan son jin labarin Bash a bakinsa. Alhali ni kuma naso in fada masa zuwan wasu manyan mutane da sukazo gidan mu wani rana suna tambayana wai lamban Man bash suke nema da ake samunsa a waje na ? Wanan naso fada masa amma saiya tare da wanan kalaman marasa dadin ji daga bakinsa har yana ikirarin cewa haka mu mata muke da munga wani dan oppotunity yanzune sai mu lakewa mutum don kwadayi. Sunana ya kira da Aisha na dago na kallesa kafin yace kiyi hakkuri don Allah zanyi bincke kan wanan zancen . Do min ina ganin akwai wani abu a kasa wanda bamu sani ba koma meye zamu sani insha Allahu nan gaba. Don maganan nan da kikayi a yanzu cewa anzo wajenki neman number Oga Bash yasa na danyi tunane su waye zasuzo gidan nan wajenki neman layinsa. Waya nuna masu gidan ku har sukazo dole akwai dai akwai akwai abinda ya faru har salman din yayi hakan gareki? Yanzu kiyi hakkuri don koshi bash din banson yayi saurin fahintar da matsalan saboda yadda suke dashi salman din don banjin yasan da wanan zancen ayanzu . Ya juya zuwa wajen mota da sauri ya bude baya ya fito min da wani babbab jakka haka irin na kasan waje din nan da ake tura sako dashi . Ya dawo inda nake tsaye yace ga wanab in kawo maki kayan aikine a ciki zaki bukacesu a yanzu wajen da zaki iya bayanin da yai min ke nan. Murmushi nayi na kalli jakkar a lalace nace Auwal na fada maka sabon yaudarane wanan kuma me zan bukata dani ban sani ba sai shi zai aiko min tun daga can ? Ki karba don Allah Aisha kada daman nan ya wuceki oga dai ba zai taba yin abinda zai zubarwa da mutuncin gidansu ba kin sani. Wanan kalamin yayi kama dana Asmau yasa na karba sai naji abindake ciki yana da nauyi kara kallon jakkar nayi nace kace nagode na juya na shiga gida kai tsaye.