Sashe 78
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anty Basira matar yaya habib ne ta leko dakin ta kasa shiga tana tambaya wai Aisha take nema ? Sai wata kawar fati tace wata Aisha tace Arab Aisha Arab nan saratu ta cabe da yar kwara dai wanan muna Arab ne ai. Jin ta ambaci yar kwara yasa na juyo don nasan ni mafi yawan mutane ke kira da yar kwara ko a gabana wasu na kirana da wanan sunan. Don haka yasa na juyo ko bake take nufi ba matar yaya habib ce ke neman ki ban tsaya kulata ba na mike daga kan gadon zuwa wajenta. Muje dakin mummy muci abinci ta fada nace to gani tafe tabar wajen nabar shashashan na bayanin wai ma,anan kwara muka fito nida Maryam da Asmau don tare mukafi tafiya ko ina dasu mu uku su faridama su uku da Aimana da samira. Tana zaune saida muka shigo ashe tuwon garin doyane na amala miyar ewedu zamuci Allah ya gani duk sha,anin nan da akeyi ko ruwan pure water ban taba sha a gidan nan ba . Ta fito da abincin a tsakiya bayan mun zauna maryam ke fadin amma dai abincin nan ba a gidan nan aka girkashi ba ko naga ya fita daba . Anty Basira din tace anty maryam tazo dashi daga gidanta jin hakan yasa na mike na dauraye hannuna saiga umma mai dakin tashigo tana fadin. Amma dai abincin nan ai yayi maku kadan ina maryam din ta kara maku tace ta fita yanzu ana zancenta sai gata ta fado tace maryam ki zuba masu abincin wanan yayi kadan. Umma bafa na taro nayo ba kin sani mutanena da zasuzo min nayiwa shi saita juyo ta dan dubemu au kune maryam aiban kula ba ta fada . Ta dauko muna abincin da yawa haka miyar ta zuboshi ciki a wani kula ta miko muna tana fadin aiko don Aisha da maryam ban isa hana maku abincin nan ba. Aisha fa mutumiyatace tana karama yanzune ta gujeni data girma haba dai anty na fada ina dariya mun soma ci ina dan tsankwara samira tashigo dakin karban waya wajen Asmsu . Nan ta zauna itama saina dauki leda biyu na abincin nace a ajewa Aimana da farida suma suci mummy daki bari muci abin mu Aimanan nan wallahi bata da kirki nan ta soma muna hiran abinda ya faru da kairat ta bata sako ta kawo min sabanin yadda Aimanan ta fada min. Nasan halinta yasa nace kuyi hakkuri kowa da halinsa ake zama dashi ai haka halinta yake da akasi wai bakiji ba mummy dazun take fadi da safe wai bukinta ai sai yafi wanan mu bari mugani dai. Ba karya ta fada ba ai me yuyuwa yafi wanab din don wanda zata aura bama kasan nan yake ba haba ta fada nace karyane ashe da gaskene nace ba karya takeyi ba Allah. Iya abinda na fada ke nan kai mata da yawa suna son zuwa kasan waje aure suyi ta cika baki akan hakan anty Basira ta fada. Akwai wata sister din mu da tayi aure irin wanan saida akaje can tace ko satin amarci bata rufe ba miji yace oya ba na kawoki nan bane don ki huta a banza. Neman kudi zakiyi tare damu a nan tace ya bata option biyu ko tayi goge goge a hotel ko ta kama kitso tana kawo kudi yace ko kudin haya ya ishesu aiki a can. Nan kowa ke fadin albarkacin bakinsa har aka daura aure muna dakin don yaya habib sun tafi daurin auren yaya kabir shiyasa matar nasa ta lake min tunda safe muke tare da ita ashe. Su Aimanan nan suka samemu sukaci abincin da muka aje masu Ammah tazo da anty safiya da yaranta biyu da suke zaman gida tare duk muna gidan an rufe gidan namu a ranan don yinin bukin. Sun kafa wasa kofan gida a nan zasuyi wasan karshe tare da dj kafin akai amare dakinsu muna nan dakin umma yan gidan ango sukazo muka shiga gyara masu wajen zama. Wanan ce ai naji wata na fada a bayana hakan yasa na juyo don ganin mai magana a lokacin aiko tubarkallah wallahi wata ta fada. Kaina ya daure ban gane me suke fada ba a kaina saida tace min ga hjy ummi can tana neman ki ai a waje. Zan fita saiga anty ummi din sun shigo wuri ya matse dole na fito muka gaisa dasu wajen tun daga wanan lokacin muna tare da kharat saida zasu tafi muka fito masu rakiya nan suke tambayana nan ne unguwar mu wai ? Asmau tace ga gidan mu can na ukun can shine namu ai ashe har nan kuke ta kara fada zo muje gun motan anty abin bukinki yana ciki tazo maki dashi khairat ta fada. Hakan yasa na bisu har bakin motar buhune cike da abubuwa khairat din ta bude boot din motan ta fito min dashi tana fadin kinsan anty ummi da yaya Bash akwai alkawarin amana donshi take haba haba dake nayi murmushi. Yaushe zata koma na samu kaina da tambaya tace da gobe ne amma yaya A Dabo yace su bari sai friday jibi su koma Ok zanzo har gida in gaida ita nagode . Asmau ce ta dauka zuwa gidan mu da sauri don kada a taruwa kayan tasan halina tace zan rabawa mutane. Ji nayi an dafani hakan yasa na juyo da sauri daga kallon Asmau din anty ummi dince a bayan mu dan dukar da kai nayi ina fadin sannu anty nagode naga sako jiya yau kuma ga wani an kawo min. Kece next fa daga wanan sai kuma munzo naki a wanan unguwa waima kuna waya da kanin nawa koda yake yaki yarda yace shine yayana. Murmushi nayi mata ina noke kai ta kara kamuni tana fadin mu zamu tafi wata kila ba zamu kara haduwa ba daga wanan karon ? Ai tace zatazo gida ta gaida ke hjy a sayi kaya harkafa daga bayan mu aka fadi hakan duk muka juya anty safiyace a bayan mu take fadan hakan ga anty ummin din. Hjy Allah ki gwada zaki nemeni daga baya kayan mu ba irin nasu bane mu kayan el,sutra muke saidawa hadi hadin gida na ainihi babu surki ba algus babu cutarwa idan baki yarda dani ba ki tambayeta gidan mu daya da ita ai ta nunani wajen matar. Kasa ka bude inshige naji a wajeb saboda kunya itako taci gaba da fadin kyautama zan baki hjy tunda naganki tare da wanan bari zan hado yanzu don Allah kada ku tafi ku tsaya ku karba. Anty ummi din ta juyo gareni tana fadin wai da gaske gidan ku daya nace yayatace gidan mu daya da ita sai ta bita da kallo tana murmushi. Sai kuma wata tazo ta dauke mata hankalli garemu wai ance akawo kudin wankin amarya ta danja tsuki tana fadin su duk me suke a wajen nan oya lanti kibi kowa daya dace saiya bada ki dawo na cika akara maza jeki don Allah akwai inda nake son zuwane daga nan. Bayan matar ta tafine ta juyo tana cewa dani zamu gun mai babban dakine yau tunda safe ta aiko min da zagin cin mutunci zan tafi mu kwasa da ita. Ai bana jin tasan da itama anty khairat ta fadi hakan tace oh haba dai kinko huta da bakinsan wainar da ake toyawa bama nikan yau ai nasha zagi tunda safe. Ban fahinci komai a zancenta ba saiga anty safiya din ta dawo tana fadin zanba Aeesha ta baki kan ku tafi don ido yayi yawa anan yanzu. Na hada maki da matar minister, izzar mowa, gumban ukku bala,i amma don Allah hjy in kina da kishiya wanan izzar mowa din kiyisa sau daya please ? Kai matar na very funny wallahi kwantar ni banda kishiya zan iya yin amfani dashi gaba daya kwarai kuwa ta fada tare da fadin don girman Allah kiyi amfani dashi ke kadai a wajen na sayarwa shi kaya mu talla da ikone sai mun soyema muke zaba maka da mun kalli mace musan meya dace da ita. Dan tsuki naja yasa ta kalloni tana fadin kin gani ko ke yarinyace baki san komai ba ja bamu waje don Allah kinji nan zancen manyan mata ake a yanzu. Abinda nake so ke nan kuwa anty khairat ta rigani jan hannuna muka dan gusa zuwa jikin motarsu sai muna kallonsu suna ta zuba kamar sunsan juna saboda dadin bakin anty safiya din wajen sana,anta. Bayan sun gama ta miko min leda cikin dabara tace ki saka mata a mota na karba kamar yadda tace nace gashi tace in saka a mota na anty ummice wai khairat ta karba. Ni dai nasan ta karba kawai don kawaici ne don irin matan nan hamshakai me suke nema kuma a yanzu banda shirmen anty dai. Za a tafi da amaryane a lokacin don haka bamu saka kanmu binsu ba don kowa na fadin zai tafi sun kawo irin manya bus bus din nan na kwasan mutane har guda ukku na yan kai amarya. Anty basira ma bata tafi ba muna tare da ita sai lokacin take min hira wai ai anty fati din da mijin nata dataje wajensu tayi hutune suka hadu a can Abuja. Nikan ina mamaki ina ta hadu da Dan Nadabo family ashe mafari ke nan a in mamaki wai sai gata tana ce min muje gidan mu tana son sayen abu wajen anty safiya. Mamakina ragagene saboda yadda nake ganin manyan mata na zuwa saye wajen anty safiya din kayan da take kira da El,sutura ingantace a fadan ta. Saidai anty safiya din mun samu tabi gayyan yan kai amarya a lokacin mun kirata a ways sai cewa tayi Asmau ta fitar mata da kayan ta nuns mata hakan akayi kuwa ta barni da mamakin yadda Asmau ke bayanin kayan. Karshe ma mikewa nayi na bar wajen sai gashi a karshe ma dai nake ji a bakinsu wai tasayi kaya yakai na dubu ashirin gunsu. Har karfe goma na dare tana gidan kafin mijinta ya dawo ya dauketa su taxi suna ta hira da anty safiya data dawo kai amarya. Sai wajajen sha dayan dare su yaya suka iso da amaryan yaya