Sashe 33
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sam ban san abindake wakana a wajen makaranta ba ashe kamar yadda yaba masu zane umurni haka sukaci gaba da zanamu saidai ba cin zarafi ko daya a ciki kamar yadda suka dauko da farkoyi. Wanan zanen labarinshine ya karade ko ina yayinda wasu da basu san muba abin bai damesu ba wanda kuma suka san mu suna tofa albarkacin bakinsu akai duba ga yanzu yadda ya takura min dole kullum saina zo office dinsu din nan yasa komai yake a baiyane ga kowa halakan mu yanzu ba abin tsayawa tsegumi bane sai wanda so sawa kansa hakan zai tsaya tsegumin wanan. Saidai kowa da yadda yake fassara alakantamu wasu naganin ai mun dace wash kuma suna ganin sallon yaudarene kawai irin ta maza idan mun watse shike nan ya gudu ya barni. Shi dai a bangareshi yana jin duk surantan da akeyi kan mu don har zama sunyi da committing makaranta kan yadda zancen yai yawa a satin ya nuna masu babu ruwansu a tare suka ganmu don haka ba matsalansu bace wanan . Abinka da masu fada aji akai shiru kan zancen don ba mai yarda ya rasa aikinsa kan abinda bai shafesa ba ya zamo mai matsala a wajen aikinshi tunda ya fadi hakan garesu dole akwai abinda ya taka kan zancen ke nan. Don yaron takadarine suma tsoronsa suke ji duk da basu san meya taka ba a lokacin amma shakkunsa ya darsu a zukatansu na dan wani lokaci. Friday ban jima ba na fito da niyar komawa gida kamar kullum don bamu kai yamma ranan Friday din da an fito da safe shike nan kowa zai kama gabansa don yana da wuya ayi wani aikin kirki kuma. Saidai ina doso wajen driven nan nawa na alaikakai nagani a bakin department din mu yana zaune saman mota ganin na fito ya soma washe min baki tundaga nisa yana fadin. Ashe na kusa makara hjy said a oga ya kirani ya sanar dani hakan na tuna yanzuma daga wajenshi nake ya ban sako akwai wace zamu dauka a hanya zata kaimu wani waje. Kallon mamaki nayi masa ya dan sosa kai yana fadin umurnine hjy bai rufe baki ba ya tsayar da motan wata dake tsaye gefen titi ta bude gidan gaba ta shigo motan yaci gaba da tafiya. Shopping center ta fada kafin ta juyo ta sauke kallonta gareni tana fadin sunana Kharat ni kanwace ga salman dake tare da ya bashir zamu danje shopping ne dake kamar yadda suka umurceni. Kinsan yanzu dole shigarki da takonki ya banbanta dana saura don kin,san akwai mahassada masu saka ido don shine ma ake so ki fito clean zuwa jibi da kowa zai gama San in ki. Ina fatan ba matsala ga hakan ni kanwace a garesu dukkansu biyun don haka ki saki jikinki dani don Allah kamar kina tare da yar uwarki ta jini. Baida matsala hakan ma yayi tunda ai muna tare kinsan hjy mahaifita amanan ta ya danka min ita kinsan nauyin amma ga dan Adam a wajen Allah donshine nake kokarin kiyayyewa. Murmushi tayi kafin tace dashi kama kwantar da hankalinka idan sune na tabbatar da ba abinda zai faru insha Allah kasan shi man bash babban mutum ne yana da wata manufar yin hakan da yakeyi a yanzu. Bakin wani shago muka tsaya na daga kaina na kalli manyan rubutun da akayi shopping coplex dan tallaka ina zansan wanan ni garin ma da muke bi ganinsa nakeyi kamar ba garin da nake a zaune ba don iyakata unguwarmu zuwa inda nake shiga motan dake karasamu saiko tsohon uguwarmu da muka taso bandashi ban san ko ina ba a garin tunda ban fita zuwa gidan kowa. Dama gidan dangin Abbu ne kuma yanzu gamu a unguwa daya dasu don haka banda sauran wajen zuwa kuma ke nan. Bissimillah fito mu shiga ta fada hakan yasa na dago kai daga dogon tunanen dana shiga Ina kallonta kafin na bude motar na fito tace shima ya fito don kada yaga mun dade bamu fito ba. Tare muka shiga ciki mu ukku sai naga kamar mafalki nakeyi a lokacin bagaskiya bane nice a zahiri cikin wanan shagon. Ta fara da shiga dani bangaren takalma da jakkuna tace ki duba yar uwa koda wanda zaki so anan namasan zusuyi maki kyau don kayansu qualities ne. Da ido nabi kayan wajen da kallo rasa nayi me zance sai nace ki zaba min kawai ba matsala tako zabo din don yan wasu jakkuna ta zaba masu kya tare da takalmansu daidai kafata. Lokacin ta juyo ga Auwal tana fadin yanzu aikinka zai soma dan miko kekencan in zuba ciki ya garo mata keken ta zuba a ciki. In takaice maki kusan sums nayi da mamaki yadda ta loda kaya don kawai na bata go ahead din zaba nasa a raina wajen biyan kudi nan za,a kwasa ai ashe nike haukana in kadai a lokacin. Har yaran anty safiya saida na daukowa kowa saidai da jikinsa zannuwa kuma ta zabo sunkai kala barkatai da za a dinka ga remade dinkanku daga company data zabo kayan kamshi man gyaran kai tun ina mamaki har yakai na dankare wajen muka fito ta mika card zara kawai sukayi suna fada muna kudin. Nan tace tayi mantuwa ta koma ta hado kayan shayi masu tsada akai packing din kayan tare da hadamu da Wanda zasukai muna a mota. Ita kan wayayyace don banda dan kwalin ganyen shayi data riko ba abinda ta dauka a ciki saida muka kai dinki kafin Auwal ya sauketa gidansu. Tayi muna sai anjima har ta juya sai kuma ta tsaya tana fadin in saka mata number ta a wayar ta na kira ta loda tace zata kirani muka tafi. Ammah na zaune sai ganin Auwal na shigowa da Maya niki niki bayana tayi ina nuna masa inda zai zube min gashi anyi sa,a it's kadaice a gidan duk sun fita balaguro daga uwar har yayata. Aimana kuma wai ta dawo ta dauki kaya tace gida zata ya gama shigo min dasu Ammah na zaune cikin mamaki saida na dawo take fadin Aeesha wanan tarin ledojin meye haka ba iyaka ? Kayane Ammah barin gama shiga dasu zan baki labari na fada dakina nakai kaf kayan na zube kafin na fito na soma fada mata abinda wanan kharait din ta sanar dani. Anya Aishatu baki kai kanki inda Allah bai kaiki ba kuwa ni fitinane banso wallahi irin gidajen manyan nan babu komai a cikinsa idan ba fitina. Ke kuma gaki ga yadda kike sai nake ganin kamar yaron nan ba sa,an yinki bane Aeesha amma Ammah ba rokonsa nayi ba nasani Aeesha ba zaki taba aikata hakan ba ai. To kuma anface rabon kwado baya hawa sama Allah ya tsaga da rabonki a aljihunsa shine kike ganin dabara ta kubce masa amma ruwa aiba sa,an kwando bane. Mikewa nayi don zancen Ammah inda sabo na saba dashi tun akan halakata da yaya Suleiman' naji ta fara fadan hakan balle yanzu ga wanan da batako sanshi bama. Aimana nashiga gida mahaifiyarta tana zaune tawa wasu yara kitso tace kamar kince satin nan ba zaki shigo ba sai wani satin zakizo ? Mama gara dai in dawo din zaifi min yanzu duk tazo da korafin da zata zowa iyayyen nata dashi akan anyi mata jin hakan yasa uwar fadin ki daibi sannu don mutanen nan basu da maraina a wajen mu kin sani. Kina son dauko wani halin da bashi ba kidorawa kanki kuma yanzu fadan uwar yasa ta shige daki ta kwanta barcine ya dauketa bata falka ba sai wajajen La,asar da yake jumma,ace ba yan kitso ranan da yawa sosai haka yasa ta gama da wuri. Saida Aimanan ta fito ta nemi abinda zataci ta zauna a kofansu tana ci take fadin mama na dawone inkai dinkin turamen nan da hjy tazo min dasu dama. Wasu turame Aimana tayi kasa da kai daga kallon uwar kafin uwar dora da cewa Aimana kifa bi zancan nan sannu . Mama to ya zanyi high intuition fa nake amma ina fama da ragga tunda Allah ya kawo aban abina in saka mana nina in fito kamar kowa. Daga kofa mahaifinta ke fadin yayayane wai damashi irin mummunin cikin shirin fatakene ba ruwanshi tsohon dan kwallone shi don haka yake abu kamar na yara kananu gashi kuma yayi zamani da tabar iblis ya barine yanzu da girma ya kama amma kamannin hakan na nan garesa don basu bace ga wanda yasan su. Nace wai yayane daga dawowan yarinya zaki hauta da fitina kuma ya fada yana zazaro masu idanunsa Aimanance ta mayar masa da dalilin zuwanta ta dora da fadin har Aeesha yanzu tafini sutura arziki daddy. Kibata kayan ta mana maryam ko sakawa zakiyine da kika boye yanzune daidai tayi amfani da abinta ai tunda ko gobe turo mata da wani zaiyi. Baban Aimana nifa tsoro nakeji zancen nan bai zaunu ba tsakaninsu azo zance baiyi ba sace a basu kayansu me zamu fada masu karshe ta riga data dinke kuma ? Ikon Allah wayace su kawo kin rokesune da zasuce a basu kayansu kwaso abinta ki bata ta dinka kayanta don Allah ke yanzu ba dadinki bane Allah ya rufa muna asiri a nan. Badon uwar task ba tana kallo Aimana takai dinkin turamen har hudu akayi mata dinkin express akan zata dawo dasu monday ta nuna min kwaruru ba tsaran wake bane . Don tayi gaba dani ba zan taba cin mata ba a yanzu cikin irin hiran da takeyine uwar ta fahinci akwai matsala a zaman mu yanzu hakan yasa da dare uwar ta sameta da zancen. Saida ta gama zuba uwar race asha Aimana banyi zaton jin wanan daga bakinki ba na san ko waye Aeesha don a gabana ta task kuma kema kinsman karyanki kice zakija da Aeesha wani wajen. Gara run wuri ki cire wanan a zuciyar ki game da yarinyar nan Ku zauna lafiya kamar yadda kuke ada nasan duk wanan abin daga garekine Aimana saboda nasan halin kowan Ku don shinema tunkan su bar unguwan nan ta daina shigowa gidan nan . Menene matsalanki da Aeesha bayan iyayyenta basu raina muna ba Aimana, fada sosai tayi mata ta fito zuwa dakinta. Hankalina bai tashi ba