Sashe 63
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gaban mu ya tsaya. Na ciki suka fifito cikin wata farar mota sai sheki takeyi tana walkiya kamar kura haka na zamo a cikinsu don har ga Allah ban taba wani amarci ba sai wanan karon. Bakin saratu kake ji yana tashi tana fadin ai wanan halin tsiyane ku bamu kudin amarci abu ya gagara sai yawo kukewa mutane da hankali. Jin hakan cikin rashin da a yasa nace umm,umm haba ina jan tsoki na juya naji wata kawar Fati na fadin Aeesha karaso don Allah wai kece zaki fadi ko nawa za a banu. Three hundreds thousand's zasu bayar saboda amaryam mai tsadace na juyo ina fadin hakan garesu sai naji sun saka ihu lokaci guda. Kamar zanyi magana sai kuma na dake ban kara magana ba na juya kawai ina jin angwanan sun kwashe da ihu wai na cika kudi suna ganina nice mai hankali a cikin mu ashe nafi saura barna. Shi suka bukata shi zamu basu wani so gentle ya fada ya nufi mota ya cirosu Cash yace amma ni zan karba na juyo nace kaba anty saudat dai. Kece dai zan ba tunda ke kikaiwa amarya kudi suko sai fadi suke don Allah Aeesha jeki karba mugani hakan yasa na taka nazo na mika hannu saiko ya miko min ba musu wurin aka sa ihu lokaci guda matan da mazan. Saratu don bata da kunya harda guda da shewa cikin watse na juya na barsu nan suna hira dasu muna zaune kawai saiga su saratun da wata da nake yawan ganinsu koda yaushe wai in basu kudin. Zakice badani take magana ba ganin yadda nayi banza da ita sai kawai ta fara zagina tana fadin kada ki kawowa mutane rainin wayau wallahi me kike nufi da ba zaki bada kudin ba cikin daga murya. Kudin me mummy na fada masu a gurguje aiko kamar zata tafi ila ya jawota ta dawo tana fadin dole dai ki bayar dasu tunda ba bukin gidan ku bane ai. Ke ta gidanku nah bari yayan kwarai suyi magana don Allah ba irin ku yuyuyu ba ta dauka zata iya nan Asmau ta wanketa kwal a cikin mutane kai wa yan nan yara sun iya cin mutunci wallahi. Da kyat na samu na izzasu zuwa wajen mota suka shiga Allah yasa an rage sosai a lokacin don yamma tayi maryam da Aimana suka biyo mu suka shiga muka bar farida da bamu samu gani ba tare dasu. A karshe akanta fadan ya koma ashe don tace wai na lake kudi ina son in zame wani abu daga ciki ita kuma farida tace haram wallahi badai Aeesha ba kan. Abamu kudi donta zakice zata rike aikuma wai donme farida zata fadi hakan suka kuma kwasa sukaiwa juna kwal a wajen. Ba gidan mu na tsaya da mota ba kofan gidan Rabakaya na faka mota ashe ango da wasu abokansa suna nan sunbar wajen taron tare da amaryansu. Nayi sa,a kawarta din nan saudat suna tare na kirata zan danka mata kudin tace haba Aeesha kamar abin gudu rikesu wajen ki har mu natsu. Akan kudin ga akai bala,i tace dawa nan suka fada mata abinda ke faruwa tace shege wai gara da baki bata ba da yau ta cucemu wallahi saratu fa bala,i ce don Allah ku aje har anjima. Gyale na cire na saba a kafada cikin gajiya ganin mun dawo kofan gida ba mutane da yawa lokacin na nufi mota na bude na zauna. Wayata na ciro ina duba hankalina bai ga surutunsu saijin mutum nayi a gefena yana fadin surutu yayi yawa a can ko hakan yasa na dago kai wanan ne daya miko min kudin yazo inda nake kafin ya jingina jikinsa a motana yana fadin. Da alama ku yan uwane da fati ko nace eeh ina kokarin saka takalman dana da cire kafa daya a kafata na gyara na fito daga motan. Aida kin zauna zamu tafine anjima dai zamu dawo zance da dare gun amaryam mu zamu hadu nace ba tabbas don gidan mu ba aikai wanan lokacin a waje balle dare . Zancen ya bashi dariya kafin yace babban yarinya kamarki haka za a tsayawa fada kada ki sani dariya don Allah yanzu a gajiye nake nima anjima dai zan dawo insha Allahu. Nadago da zumar zance ba wasa nake ba kada ka dawo fa idona ya sauka kan yaya sulaiman gefenshi kuma yaya habib ne da yarsa yana alwala . Saidai muna hada ido ya sako min wani harara dana kasa fassara kona meye a lokacin ko halin nasa na muguntane ya motsa oho ? Kafin na dago har maishi ma ya juya ya fara tafiya saratu ta karaso muka shiga mota nayi ribas zuwa gida a can ta fita ta bude min get na shiga da motar . Tsayawa mukayi kus kus ina bata labarin abinda ya faru sai cewa tayi me zakiyi dasu don Allah shidai wanan ai karsanane yana da mata zai hanaki hirane ? Shi kuma Suleiman wallahi kada kima tsaya kulasa tunda uwarsa bata kaunarki mummy ki rabu dashi kawai don Allah. Asmau bai mun komai bafa kuma muna waya dashi gaskiya da nasan ya iso garin nan bama zuwa kofan gidan nan yau. A,ato mummy kina son wahal da kanki kuma rabu da uwar mijin data fara nuna maka tsana da danta tun a waje wallahi garama wace ta boye sai kaje ta fitar da halin ai. Ke mummy nifa ban maki fatan kowansu a yanzu wallahi suma sunsan kinfi karfin su a yanzu wallahi. Waiku baku shigowa gida kun tsaya kamar masu tsunami muryan Ammahce data leko take fadin hakan garemu sai asmau tace kai Ammah magana mukai da uwata wanan yar iskan yarinyar keson ta raina muna wayau. Nan ta shiga koro mata fadansu da saratu naji dadi da amsan da Ammah ta bayar a lokacin nace mungama zuwa bukin tunda wanan yarinyar dai ta nuna bata kaunanku cikin sha,aninsu. Wanan halin tsiya har ina zata saka min yarinya a gaba cikin mutane da zancen banza tunkan a fara bukin nan yarinyar nan take tsokanar Aeesha ina taushewa kaza na son data koda take takasa. Don ba fin Aeesha tayi asali ba nata kaddaran ke nan yazo mata haka ku shige kuyi sallah lokaci na wucewa ta fada a karshe muna alwala su samira da Aimana suka shigo nan suka fada muna fadan da akayi da farida bayan tahowar mu. Daga daki Ammah ta fito tana fadin kun gama zuwa wanan bukin dama da dai da duniya yaran nan na hjy Aginatu basu gaji arziki basu dan dama dan namijin nata yana da dama shi. Buta na mikawa Aimana na mike zuwa daki don inyi sallah tare da cire tufafin jikina har lokacin ina tsinkayo fadan Ammah har lokacin. Bayan isha,i muna falo ana ba anty safiya hiran abinda ya faru yaro ya shigo yana fadin wai sulaiman na kiran Aeesha. Tsit falon yayi na dan lokaci guda Asmau tace kace tayi barci nace kai ce masa ina tafe kaji lalai kam ya Suleiman nefa Aimana ta fada. Suka hau fada wai wallahi kar inje kawai in fita batunsa kiran me zai min kuma bayan uwarsa ta rabumu. Na dai mike na shiga daki na fito a tsaye na sameshi ya jingina jikinshi da bango tare da harde kafa kamar yana tunane a lokacin yana ganina ya saki ajiya zuciya tare da fadin. Ran gimbiya ya dade ashe zaki fito na dauka ai ba zaki fito ba idan yace maki da kafa nazo ban iya bakar magana ba da nayi masa amma sai na wayence da murmushi ina fadin. Aeesha da ka bari daice wanan ba wata Aeesha bace aka canza idan ma zolayata zakayi ni har yanzu ina nan yadda nake ban canza ba saidai kai kila mutanen kaduna sun sauya ka. Ke kinga alaman sauyawa a wajena Aeesha har yanzu ina nan a Suleiman dina da kika sanni ai nace ni kuma na koma Aisha yanzu ko ? To mu bar zancen Allah na dauka ba zaki fito ba nace saboda me wai yaya koma zaki fitowa wani ai banda kai dan uwana da muke ta jiran dawowan ka kullum. Yayi murmushi tare da fadin haka dai kikace Aeesha ni dazun ai na kasa gaskata idona akan kece nake gani a jikin mota zaune. Haba yaya har na wani sauya maka da idonka zai kasa gaskatanine kuma yanzu wai da yaushe ka iso ne don Allah ? Dazun da yamman nan isowata ke nan ban jima ba na fito in samu jam,i har kika gani nace to yaya kaduna ya aiki da mutanen can kuma ? Saida ya nisa yace komai Alhamdullahi ya Abbu dasu Ammah ina Aimana nace duk suna lafiya Aimana na ciki tace zata fito ku gaisa idan ta karasa cin abinci. Ashe na saura da muka mi a gunku irin haka wallahi cikin shaku nazo nan don ban dauka zaki fito har ki saurareni ba a yanzu. Saboda me kace haka yaya ko ance ma munyi wani abune yace a,a ban hadu da kowa ba balle a fada min amma gaskiya Aeesha kin sauya min sosai a yanzu kasa gaskanta hakan nake a zuciyana har yanzu. Dawowan Abbu yasa muka tsaya gaidashi din ya taka har zuwa kofa ya tsuguna yana gaida Abbu naji Abbu yace wai Suleiman ne yaushe garin namu ? Yace da yamman nan nazo baba mun sameku lafiya Abbu ya amsa da lafiya kalau ya aiki kuma yace Alhamdullahi baba sai naji ya ban wani irin tausayi. Don yanayinsa da gaba daya ya nuna yana cikin duwa a lokacin saida Abbu ya shiga gida ya juyo zuwa wajena na taresa da fadin ga Abbu ya dawo barin koma gida da safe mu hadu ko yace to Allah ya kaimu yadda kikace dai din ai ko hakan nagode tunda kin fito na ganki . Muka dan taba hira mai kama da ba,a ko zolaya ga juna damashi sarkin son wasan barkwancine saidai wanan karon yana da damuwa ko wani abu don duk da duhune amma bai hana min ganin ramansa ba da duhun daya danyi. Mukai sallama ya tafi har lokacib Aimana bata fito ba sun gaisa wanda banji dadin hakan ba gaskiya a lokacin .