Sashe 13
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
malamin mu yace yawan cin tuwo haka da yawa yana sa mutum kiba lokaci guda ni kuma banson kiba wallahi na wayance da fadin hakan gareta. Dakuwa tayi min tana fadin kaiya yaro dai yarone wanan bokon na karanto maku karya a rayuwa kiba kan idan kin gada ai sai kinyi dama kin sani ki daina wahal da kanki don mu zurian mu bamu da gadon kiba can din nan bandai sani ba ko can cikin zurian ubanki idan su sun gaji kiba wata kila. Ai a Nasarawa banga mai kiba ba cikinsu suma duk da ba zubinsu na kwaso ba ban sani ba ko dangin mahaifin nawa can akwai mai kiba dai .? Wani kallo Ammah din tayi min lokaci guda kuma na fuske kamar ban san abinda na fada ba a lokacin sai cin abincin nakeyi a hankali a lokacin cikin daure fuska. Yayin da Ammah din ta danyi dan shiru na dan lokaci tare da zuba min ido kamar tana tunane sai kuma naji ta nisa tana fadin. Kai anya Aeesha sai kuma naji tayi shiru fasa fadin abinda tayi niyar fada a lokacin don dan tunanen da tayi a wajen a zuciyarta. Takai wani lokaci kafin naji ta sauke nauyayyen a jiyar zuciya tana fadin Allah ya kyauta ta tashi ta daga zuwa daki ta barni a wajen har na karasa cin abinci ina gab da tashi ta fito tana fadin. Ni mutanen nan su dagula min lissa na rasama ko dame zan fara a yanzu ni gani ba sabon dinki ba ko takalma kirki bandashi a gidan nan balle sabon zani duk yan tufafin nawa sun sani dashi a baya tun wancan bukin na kwanaki. Ammah meyasa kike son matsama kanki kan wanan zancene wai kiyi amfani da abindake gareki mana irin wanan wajen wasan ma ka saka balle yasama ido mutanen da duk yadda ka iya dasu ganinka suke dan kauye . Sai naji Amma din ta katseni da fadin aini bani nake jiwa ba Aeesha a yanzu kece tunda kinkai munzalin budurwa a yanzu dole ki dan bukaci abin da zai dan sauya ai bari malam ya dawo. Inji ya za ayi da wanan zancen ance da wuri wuri ake fara shiri ba sai tafiya yazo ba inji manya da sauri na dan kallota ina fadin ba inda zani Ammah a gida zan zauna . Kafin in rufe baki naji tace dani akan me wai nifa yanzu na rasa ganr inda kika dosa Aeesha cikin kwana biyun nan komai sai ki dinga jan kanki a baya. Bukin dan hjy karime din ne zakice baki zuwa matar da idan ta ganki take rasa inda zata sakaki tana fadin ke yartane yanzu kice wai baki zuwa sha,aninta wanan ma wasa kikeyi don ko malam ba zaiji dadin hakan ba ai ace bukin dan dan uwansa zakice kr ba zakije ba Aeesha ? Baki na turo gaba ina bata rai nace Ammah ni wanan irin abinda suke min a cikinsu bana so sai a dinga nuna mutum haka kuma duk inda kabi idon mutane yana kanka wananne bana so wallahi . Yo me ruwanki dasu din kedai kiyi sha,aninki kawai kibar mutane don ba,a iya masu makin in bata amsa ko in tsaya saurarenta don ma ta gane ban son zuwa din ai yasa na mike din na barta a wajen. Ina ji can dare da Abbu ya shigo Ammah din ta kara tayar da zancen bukin kuma tundai inajinsu har barci ya daukeni a haka sai washe garine na tashi naga Ammah din tayi kumshi ashe a cikin daren don fara rage hanyar tafiyan dake gabanta duk a cikin garine bukin amma ai kwana zatayi a can har biyu ko ukku. Na fito da shirina tsab na school tana zaune tana saka taki a kafanta ta dago ta kalleni tana fadin aina zata yau zaki huta ki danyi gyaran jiki kije gun maman Aimana kiyi sammakon bin layin kitso ? Shiru nayi nan ma banyi maganan ba hakan ya dan harzukata tana fadin amma kinji mena fada kon kyale kinyi shiru ni wanan takama da izzan naki ya fara isata wallahi. Yarinya a magana sai faman miskilanci kike zubawa kamar bakijina don wullakanci jin hakan yasa na juyi ina fadin nifa sai asabar zan tafi kitso inna kada inyi yanzu ya walwale min a kai kinsan kitso baya kwana biyu a kaina bai tashi ba. Ikon Allah ana gabas kina yamma yar nan ko kin manta da zancen bukine wai yau da gobene kadai muke da lokci a gidan nan. Ammah nace fa ban zuwa kuje sai kun dawo amma ni ba zanje ba gaskiya don,,,,,,, dakuwa data miko min tana fadin karbi naki ni kike mussu dani haka Aeesha ? Muryan Abbune dake fitowa a daki yake fadin haba wai meke faruwa hakane tsakaninki da yarkine tace bata zuwa ki barta mana tunda bata ra,ayin hakan. Koke ai don zuwan naki ya zamo kamar dolene da bakije ba don ba lokacin hakan amma hjyce nasan yadda kuke da ita yasa zan barki badon shiba babu mai zuwa a gidan nan gabaki daya tunda bamuji a cikin lokaci. Amma dai malam za ace hjy tana bukin danta yadda muke ace yarinyar nan tace va zata taka ba duk yadda muke naji Abbu din yace Ammamatan ina gargadin ki da ki kyale yarinyar nan don Allah tunda tace ba zataje ba ki barta. Ya juyo gareni yana fadin jeki ke ki shirya kada ki makara don lokaci na kurewa maki ya juya ya shiga dakin kuma tsaye tayi cikin mamaki tana bin bayansa da kallo a cikin mamakin kafin ta maido kallonta gareni tana fadin kiji dashi. Wanan yar ga baki daya kin sauya min a yan kwanakin nan na rasa inda kika dosa Aeesha yarinya da izza da jinkai kamar wata yar basarke haka ? Nikan a gurguje na shirya da saurina na shiga daki na dauko jakkata banko tsaya karya ba kodana fito na samu Abbu a tsaye kofan dakin yana dakon fitowa ya miko min dari na na karyawa na rusunna har kasa da hannu bibiyu ina karba tare da godiya . Na juya na fita na barsu nasan a bayana zasuyi zance a yadda na barsu din don kowa dai ransa ya baci a lokacin kan zance . Inda niko iyakar gaskiyana ke nan na fada masu ba zanje ba don in ban manta ba zuwa na karshe sha,aninsu da kukana na dawo gidan kan abinda akai min lokacin. Muna fada irin na yara na dan duki abokiyar wasan tawa tasa kuka ranan yan gidan su Abbu suka taso min kamar zasu cinyeni danya Amma sai hakkkuri take basu suko inda suke shiga ba nan suke fita ba a lokacin . Wanan yasa banji marmarin komawa ba sha,aninsu lokacin ban ma san asalina bake balle yanzu din dana sani cewa ni din ba yar kowa bace ashe.