Sashe 41
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
baya karko ya dade. A cikin nazarin dana soma shi uban ganyan da alama baiko San da zuwan matan nan ba gidan nan tunda gashi yau ya turo a daukeki yadda aka saba. Kinga ke nan bada masaniyasa bane zuwansu nan abinda kuma nake sonki dashi shine hakkuri abi komai a sannu duk wanan abinda kike gani a rayuwa wata rana sai labari insha Allahu. Don haka ki tashi ki shirya kije bokonki don't su basu da hasaran hakan kece da hara kings kuwa gara kije din kada ki rasa na yau din donsu ba hasarar bace hakan takice damu. To Ammah malam sai nake ganin Aeesha nada gaskiya anan gara kawai ta kiyayyi yaron nan run wuri tunda abin ya soma da haka maganin abin kar ayi kar a soma tunda sun nuna hakan tun yanzu. Kaiya mata ke nan ku tunanen ku ke nan idan mun hanata kulashi jikata zamuyi gida mu aje muna kallone Ammamatan ina wanine zai fito shima da kalan nasa tsarkon zaizo. Ai gara dai wanan din a gwada a gani tunda ba,asan inda rana zai fadi ba sai ya fadin sallaman da Auwal ke kwadawa daga kofa ya tsayar da Abbu din ya fita wajenshi . Nan yake dan masa bayanin zuwan su hjy Amina kura din gidan mu da batancin da sukai muna a gida cikin mamaki Auwal yace sam oga baisan da zuwansu ba gaskiya. Don yanzuma shiyace in dawo in dauketa zuwa asibiti idan abin ya tsanantane mata ba asibitin da zaku ta dai shirya ka sauketa makaranta kawai. Abbu ya dawo yasa na shirya dole Auwal ya daukeni zuwa makaranta kamar yadda muka saba a mota yake fadin shima gobe ko jibi zai dawo ai. Dama yana asibitine ashe ya dan jimu a kafasa yace amma da sauki zai dawo gobe insha Allahu kasan nan ko jibi. Shi Man Bashir din ne baida lafiya na fada cikin muryan rauni irin na wanda yasha fama da kuka murya ya dakushe saiga wayata na kara na dauka lambar kasan waje nagani. Na dauka da sallamata naji yana fadin my GF meke damunki haka kikace baki Shiga school yau sai nayi shiru don yadda nake jin sautin muryansa na ratsa kunnuwata kamar a cikin dauriya yake magana a lokacin. M Bash wai baka da lafiya akace shine baka fada min ba murmushi naji yayi yana fadin ciwon nawane yasaki ciwo ke nan yanzu nima murmushin nayi ina fadin a,a. Kawai dai daurowace hakan sai naji yace kina gida da matan sukazo gidan ku a,a nace dashi naji ya danyi shiru kafin yace bansan ko suwaye ba amma zan bicika hakan nagonosu. Yanzu dai ki bari na dawo gobe zamuyi magana Allah ya dawo dakai lafiya na fada naji ya kashe wayar ina kokarin tura wayata a jakkana naji sako yashigo min na duba wasu kudine masu yawa ya turo min lokaci guda haka saida abin ya kadani. Tuna binda ya faru wancan karon tsakanina da Aimana yasa banyiwa Auwal magana ba naja bakina nayi shiru ina mamaki kasan zuciyana kawai. Zama nayi a ina bayan mun taso daga school ina tunane akan kudin sai shawara nakeyi a raina daki na samu Ammah nakai zaune ina fadin . Yau ba a dafa taliya bane Amma ta kalloni tana fadin bari yar nan sana,arce ko nayi bani gane kanshi yanzu yaran nan sai su taru su cinye komai a karshe sai ciko ya biyoni baya. Samira da yar wayarta da take fama tazo ta zauna suna kallo zuwa can nace samira gobe ba school ki shirya mu Shiva kasuwa ina son sayan abune . Allah ya kaimu mummy ta fada Auwal na kira mukai magana washe gari sai gashi yazo ya sameni gida shiya dauke mu zuwa kasuwan. Bayanin inda zai kaimu nayi mai sai gamu wajen yan electronic fridge muka taya babba na kwance sai na tsaye sai injimin murda taliya guda ukku sai buhun filawa biyu sai cefane da nayo mai yawa da za ayi amfani dashi gidan wake tare da waken suya sai waya da naba Auwal ya sayo guda biyu tun a gabanshi na mikawa Asmau daya samira daya nace taba sama,ila wanda ke hannuta. Saida dariya ya kamashi yadda suka rungumeni a wajen shiyasa kayan mota muka nufo gida niki niko da kayan mu sai ganin ana shigo da kaya kawai Ammah tayi. Sai bayan angama shiga dasune na fita wajen Auwal da zaki dauka yanzu shi din wani Dan uwanane na jini ko kuma saurayina don shakuwa dake tsakanin mu a yanzu. Godiya nayi masa yake fadin aiba damuwa dama aikinsane ya kulla dani har zai tafi nake fadin Man Bashir dai bai dawo yau din ba Auwal kamar yadda yace ? Wata kila ko zuwa dare su sauka don su tafiya ba aiki bane a wajensu ai zaki iya jin ya sauka ko cikin darene tunda aikin jirgine ba mota ba. Ajiyan zuciya mai nuna damuwa na sauke a hankali tare da furta Allah ya dawo muna dashi lafiya Allah kuma yasa yaji saukin kafar nasa ya amsa min da amin ya tafi. Koda na koma cikin gida na samu su Ammah na bubude fridge din suna kallo kafin ta juyo ta dubeni tana fadin wanan kayan haka Aeesha ? Eh Ammah so nake mu fara sana,a dashi a yanzu tunda gamu da yawa a gidan kinga idan an gane zamu samu abin dogaro anan kuma tunda wacan sana,an yanzu bai shiga kamar da. Amma yar nan kina da abin mamaki yanzu wanan sabon abin zamuyi sana,a dashi nace Ammah shi wanan kinga yadda ake neman kankara dinnan da ansa kwana biyu ba a budeshi ba duo kankarewa zaiyi. Haka shima wanan cikinsa zamu fara sana,an kunnun ayya zobo da soya milki said a raba tsakanin nida Asmau da samira da anty safiya kowa ya dauki nasa sana,an ke kuma mubar making wancan babban kina loda kankaran ruwa a cikinsa. Ihun murna suka saka nace ga kayan aya da zobo da soya beans sai kayan hadi komai mun sayo shi wanan engines din taliya zamu barwa anty safiya da yaranta su dinga murdawa suna sayarwa shima ga filawa nan da zasu fara munayi kuma duk sati anawa fridge zubin adashensa gidan jujama har a fitar da kudin fridge din . Malam yayi gaskiya da yake fadin wanzuwarki cikin mu alherine watarana yau na yarda da hakan tunda abinki bai rufe maki ido akan mu ba Aeesha. Kowa a cikin mu cikin hikima kin masa tanadi yanzu da zai daina zaman banza zaman kashe zani tunda kowa nada abinyi idan gari ya waye. Abbu ya nuna far in cikinsa sosai da wanan abin da nayi bayan yaji bayanin kudin na fada masa Man Bashir ne ya turo naje asibiti dash shine nayi dabara na kashesu anan. Yau da Abbu zai san yawan kudin dake account dina da kila ya hanani halaka da Man Bashir ga baki daya son rudewa zaiyi da ganin hakan da yayi min din. Bai dawo ba kamar yadda yace din sai bayan kwana uku ya sauko kasan koshi da karfen taimakon tsaya ya iso gida. Wanan yasa yan uwa da abokan arziki na jiki da sukaji labari tururuwan zuwa gidan gaidashi saboda alherinsa ga yan uwa . Wanda kafin hakan na katse maki labari zeey mun sayo kayan nan kasuwa washe gari ina gidan akwai ashe Auwal wai yazo da kaya a gidan mu har ya kafa a ko wani daki tv sai katifu da labulaya . Don ya tambaya me na sayo kasuwan yayi masa bayani yadda nayi mai kan zaman banzan da mukeyi a gidan shine ta tambayeshi yanzu meya rage ya fada mai ya turo kudi akai muna wanan sayayya harda wangamemen falon mu da yai shekaru ba komai a cikinsa ya samu set din kujeru da kayan kallo ban San meke faruwa ba ina can gidan akwai dakin su farida ina barci. Said a na falka naga ashe barci sosai nayi son suna ta aikawa inzo mu fitar da ankon gidan Rabakaya da za ayi ban samu shiga ba har yakai sun barwa Ammah sako don Allah in nadawo inzo muyi magana shine dalilin zuwa don yanzu ban sakewa yadda na saba a baya gidan. Saboda yadda muka koma da umma uwar dakina kan danta yace yana sona ita kuma ta nuna bai isa ba don banda asali kamar kowa kada in bata mata zurian ta gaba. Umma tasan nasan zancen bani ba har iyayyena tunda fada akayi kan hakan har ta fada a bainan jama,a hakan bai hana inna Shiva inje har daki ingaida ita kamar kullum dantane dai naja masa baya ga halakan mu yanzu dashi muna dai Dan gaisawa sama sama kawai dashi din yanzu. Bayan na tashi nayi sallah azahar lokacin aka shigo da abincin ranansu sunyi sunyi inci nace a,a gida zan tafi tunda matar bata shigo ba idan tazo sai a kirani. Faridace ta rakoni saidai a inda muka tsaya muna magana na hango wata mota tana barin kofan gidan mu azatona masuyi kwana a wajen wani lokacine don haka ban damu da sanin ko waye ba a lokacin. Saidai tun a kofan gida na fara mamaki don ledojin dana fara karo dasu a kofan gidan namu daidai zan karasa shiga naji massage Arlan dina yayi kara amma ban tsaya ta Kansas ba na karasa shiga gidan kai tsaye ina sallama. Daga cikin falon mu da yasha sabon labule nakewa kallon wanan ba gidan my bane fa Asmau ta sheko da gudu ta rungumeni tana fadin yau kinga yadda gidan mu ya koma saboda ke mummy Ammah harda kukan dadi tayi yau a gidan nan. Da mamaki na karasa falon suna zaune suna kallo a TV sai naga tankar dai ba gidan mu bane wanan gidan a yau kowa fuskanshi da fara,a suke ce min. Ashe kinsan abinda za,ayi kika gudu zuwa gidan akwai yau kan ai kin kashemu da mamaki Aeesha yanzu mutumin ki Auwal ya tafi da masu aikin wai amma suna da saurin aiki gaskiya duka duka fa basu fi away uku ba gidan nan sun kammala komai. Mummy ni yau sai nake ganin gidan nan kamar ba gidan baban kano ba wallahi gaba daya gidan ya sauya min duk mamaki