Sashe 44
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mam Bashir mam bashi me lake nema da boyar Allah nan haka kada ka zuzuta yar mutane a banza wanan abin ashe baiyi yawa ba. Kada kasa a jefawa yarinyar nan zargi fa kasan mutane da rashin fahinta wanan kasan ba a hakan dan yanzune mutane zasu camfawa yarinya zargi saukin abin ma ka faro daga iyayyenta shi tsohon ya yarda dakai tun farko sanin kai waye. Zeey zakice bada shi salman yake magana ba a lokacin yadda yai biris sai waya yake dakila a lokacin saida yai murmushi ya tura sakon daya rubuta ya dago yana fadin. Me kake fadane wai salman sam banji ka ba malam sake maimaita abinda ka fada saidai naji kamar kana dan zancen hassada cikin zancen ka ? Murmushi salman din yayi ya mike tsaye son yasan yaji komai amsa daine baida niyar bashi a lokacin don haka dole ya kyaleshi tunda haka zuciyarsa ta bashi yi kan yarinyar. Saida ya kusa kai kofa yaji yana fadin that is the worst I can do for now don haka shi kadai zan mata a yanzu da zaisa ba zata manta ta taba sanina a rayuwa ba. Lokacin ya juyo yana masa kallon mamaki ya kada masa kai alaman ehh haka nake nufi to amma baka ganin yin hakan kamar kuskure a yanzu gareku ? After all idan ka tafi wa zai dinga bata kudi haka a rayuwanta shiyasa nake hakan ai gareta ya fada kafin salman din ya bada amsa mami tashigo tare da baki falon nasa. Duk da ba wasu baki bane na daban yan gidane su umman salman yan uwa a gareta suka fara gaisawa hakan yasa salman din ya dawo ya zauna shima. Sun dan jima kafin suyi masa sallama su tafi suna masa Allah ya tsare gaba ya amsa da amin umma alma baki zo min da wanan abin ba yau ? Dariya tayi kafin tace gobe insha Allah zan yo maka in kawo ma da kaina tunda kana so yana jin dadin kasancewar umma yar mahaifiyasa don matace mai mutunci da kula duk inda akace wanan jinintane a waje. Sai bayan fitansune ya mike kafar nasa dake nade da bandages kusan duk an nade kafan nasa har zuwa saman wuyar da kyat ya dan mike kafar dakyau saman table din dake gabasa cikin karfin hali yana bata fuska don zafi. Kallon salman din dake kallonsa yayi ya furta gobe GF zatazo gidan nan bansan me zan fadawa mami ba idan tazo ban ma fatan su hadu da ita a lokacin. Haba dai kana haukane da zaka gaiyato ta nan idonsa ya lumshe kafin yace tana son zuwa ganina tunda tasan na dawo ni kuma ba zan iya hata zuwa ba. Don nima ina son ganin ta a yanzu saboda nayi missing dinta nima ya fada yana gyara balance saman kujera tare da kallon darking din dakin kafin ya lumshe idanunsa. Malam in zaka fito fili ka fada kawai ka kamu da so a yanzu kun tsaya kunawa mutane yawo da hankali daga kai har ita dukkan Ku algungumai nagama fahintar hakan gako wanin ku a yanzu. Salman kaima kasan bani wanan shirmen abinda ka sanine ko yanzun ma hakan daurowa tayi a yanzu din don kawai na fitar da zargi a kaina. Kuma ita wanan yarinyar tausayine da jin kai yasa na fada wanan a yanzu nasan ba so bane kawai zalla tsusayine hakan. Wani kallo yaiwa dan uwan nasa na ehh aina gane tausayine basai ka fada ba ya mike ya fice daga dakin murmushi ya bishi dashi yana kada kai kafin ya sauke ajiyan zuciya yana lumshe idanuwansa lokaci guda. Don wani yanayi da yakeji na daban yana sauka masa a lokacin tabbas zancen salman yana da dan kamshin gaskiya don ya fara jin yarinyar nan a zuciyarsa. Saboda a yanzu bai iya awa bai wani abu daga wajenta ba wajen Auwal daya dankawa wanan ragamar kula da duk wani motsi nata a yanzu. Sai bayan fitan salman din ya fara duk wan nan tunane shida kansa wani lokaci yana mamakin kansa akan yarinyar yadda ya damu da lamuranta daga tausayi abin nason ya juya ya zamo wani abu na daban wanda bai tashi yinsa a yanzu ba a rayuwansa yasan ya saba hurda da mata kyawawa jinsi jinsi yana shiga cikinsu kuma suna kawo masa hari ya kaucewa tarkonsu don aikinsa baison wasa yasani. Idan mutum bason cigaban rayuwa kada ya yarda ya fada tarkon mata alokacin da duk yasa wani abu mai muhinmanci a gabansa. Don mace zata iya sanadin da komai nasa zai ruguje plan dinsa ya zamo tarihi a sanadin mace yasan abinda salman din ke kokarin lurar dashi a yanzu kan wanan yarinyar ba wai don baya son halakarsu bace a,a don yasan shi ko yaushe yana iya tafiya ya barta ako wani lokaci shima kansa salman din dake da dan tarihin yarinyar a yanzu wanda tare umma ta basu labarin komai daya shafi Aeesha din tun farko. Wanan yaji tausayin yarinyar akaron farko ya mamaye masa zuciya taya yarinya kamar wanan iyayye zasuyi watsi da ita cikin duniya haka su barta tana walagigi a wani nahiya ta daban yayi alkawari tun wanan lokacin zai taimakawa yarinyar ta yadda ba zata wullakanta ba kamar baya a idon al,umma. Amma tun farko yayi tunanen ta yaya ta wanan hangar daya fito matane kadai zai iya kusantata har ya taimakawa rayuwanta din amma kuma abin a karshe yana son ya juya zuwa wani abu Abu na daban tsakanin su yanzu. Ido ya lumshe karo na barkatai yana tuno da yanayinta murmushinta dariyata tsiwarta fushinta da yawan shiru shiru dinta gaban kowa da yake hango dabi,untane hakan yawan wanan shiru shiru din don ko umma ta fada a zancenta a taikaice dai yarinyar nada kyakyawan zuciya zaice. Murmushi yayi a yadda yaken yana ayyanawa a zuciyarsa keba kowa bace Aeesha amma kuma kina da komai da ko wani namiji yake son mace dashi. Lokaci daya kin yaudari zuciyata da dabi,unki Aeesha dariyan ta da murmushinta kadai ya canza dukkan rayuwata a yanzu ga baki daya lokaci guda. Anya zan iya jure rashin mace irin ki a rayuwata yanzu don kallo daya idan nayiwa yarinyar nan yana wanke duk wani matsalan rayuwansa a yanzu duk akwai yarinta da kurciya a yarinyar haryanzu saidai tana Abu kamar babba saboda tarbiyan data samu run farko. Ya sauke kai a karshe yana anyana kota tsiya kota arziki malaki Aeesha a rayuwansa don sai ya kauda duk wani tsarko da zai kawo masa cikas a rayuwansu. Ajiyan zuciya ya sauke yana bude ido suka hada ido da mami dake tsaye tana kare mai kallo cikin yanayin mamakin ganin yadda ta sameshi a lokacin shi kadai yana faman murmushi tare da sauke bacin rai a karshen tunanensa. Fuska ya tsuke lokaci guda don ganin mami din kada ta fahinceshi ta masa kan wani dalili nata da baison ji a yanzu wanda kusan yana son kawo baraka a tsakanin suma ko har ya kawo din zaice. Uwar ta gane sauyin fuskan nasa a lokacin hakan yasa itama ta hade nata fuskan ta zagayo da abin awon data shigo don' ta aunashi tana fadin da alama na katsema jin dadin ka ko ? Ina jin dadi ga wanda ke zaune ya fada cikin bacin rai yanayinka ya nuna kana cikin shauki da damuwa wani abu da kake gap da rasawa ko ta jawo kafan nasa tana fadin hakan. Dan kara ya sake kafin ya kalli fuskanta yana fadin ni dai zanso daddy ya canza min wani likita mai tausayina a yanzu gaskiya. Bissimillah ko yanzu kana iya kiransa ya sauyama din nima nagaji da duban wanda baijin maganata wanda bai san na isa dashi ba. Mami ke nan indai akan wanan yasa ake min keta a kafata yanzu ki daina donni nagama abinda ya kawoni nan very soon zan barku in koma inda na fito. Wani kallo tayi masa cikin shock tana fadin watau dai har yanzu kana da ra,ayin komawa kasan nan ke nan duk da mai martaba ya nuns maka baison hakan garemu yanzu. Rayuwansa daban tawa daban don haka ba abinda ya shafesu dani saiku yayansu ni ban cikin tsarinsu nasha fadan hakan ko yaushe. Dan matse kafan nasa tayi da gangan tana fadin ina tausayinka yaron nan da kafiyan nan naka ka amsa da yes kawai zance ya kare asha buki ka dauki matarka ku tafi taje can ta idda karatunta wazai takurama ga hakan kuma ? Bai kara magana ba har tagama mai dressing ta fita yana zaune ya rike habarsa ko gezau bai kara mata ba tasan halin miskilin dan nata hakan yana nuna yayi fushi da zancen da take masa a lokacin. Ta fita tana mamakin hali irin na hjy kura da zatasa su takura wa yaron nasu kan wani dalili nata duk dai haka all,adan masarauta yake dama kusan sums duk hadine irin ta masaurata akansu din. Amma yanzu zamani yazo da ko wani da yake da right din zabawa kansa abinda yake gani daidai a garesa ba tare da takura irin na baya ba. Ita kanta saboda halin hjy kura bata son wanan hadin da sukeson yi a yanzu din taxi bukatan abinda danta keso amma ba halin ta mara masa baya ya zamo na farko wajen bijerawa iyayyen nasu a tarihin gidan. Ina shiga dakina tsaye nayi ina mamaki yadda ya koma cikin dan kankanin lokaci kamar rufe ido a bude komai ya sauya a dakin ga baki daya lokaci guda haka. Dan madaidaicin gadon mai ban sha,away da komai nasa set gaba daya nabi da kallo ga akwataiyana dana aje gefe an sauya masu waje a yanzu. Kalmanshi ya fado min a rai da yake fadin nerve given up in life rayuwa zata iya sauyawa bawa ko wani lokaci yau gashi na sheda hakan kuwa. Ya sauya min rayuwa dani dani da iyayyena har da yan uwan dana sani a lokaci guda. Hakan yasa na sauke ajiyan zuciya tare da zama a bakin gadon karo na farko a rayuwata da zan zauna a saman gado cikin gidan mu run tasowana a rayuwata ke nan yasa na zauna da bissimillah a lokaci a zuciyana. Ajiyan zuciyana sauke ina dago wayata dake hannuna wanda tun