Sashe 9
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sam Sam sai ma karuwa da ta yi bayan sun bani tabbacin da wuya a samu wadda tafiki hankali a cikin kaf unguwar . Ya fada cike da jin dadin hirar ta su. Ta yi yar dariya. Kasan ya nake jin kaina daga ranar da kafurtamin kamar aure? Yace a a, tace duk wata mace in dai ta wannan karnin namu ne farace ko baka mai kudi ko mai sarauta bata kaini ba. Halifa ya sa dariya lokacin Hafsi ta shigo ta kawo masa kunu. da hannu ya yi mata alamar ta aje ta fita ba tare da ya saurari abinda Anty ta aiko a fada masa ba, ko kadan baya son abinda zai katse masu hira. Kina nufin duk kin fisu? "Tace" Nisa sosai nake Kallon na yiwa kowace mace, bafa alfahari bane tuntuni inajin hakan a raina, samun ka a matsayin miji ya tabbatar min cewa yadda na ke Kallon kaina haka ne, domin na samu mijin da shima babu wani namiji sama da shi a cikin karninmu kaga na kara yi wa mata tazara. " Mamaki ya cika Halifa yace In tambaye ki? Tace" Baka bukatar izni ranka ya dade." Yace kina karanta littafin soyayya? Ta ce ban taba ba, amma in hakan zai fara ta maka zan fara." Yace ina mamakin yadda ki ka iya magana haka, farko na miki kallon mai shiru wadda magana bata dame ta ba. Asiya ta yi yar dariyar kirsa wadda hakan ke sa tsigar jikin Halifa tashi yarr." Kasan fa shiyasa ba kyau ka yanke wa mutum hukunci daga ka kalle shi akwai kuskure, sai dai kuma nima ina magana ne kurum a gurin da maganar tawa take da muhimmaci, kaga ai bai kyautu mutum ya yi asarar kalaman sa ba musamman a inda basu da amfani ko?" Yace Haka ne. To wai kin fara jin wani abu game da ni kuwa?" Kamar me kenan? " Ya gyara zama so nawa kika tuna ni daga jiya zuwa yau.? Ta numfasa sannan ta lumshe ido. Zan yi karya ida na fadin adadin domin da tunanin ka zuciya ta tare su ke bugawa, harma na tambayi kaina ko wannan shine son da kake magana, in kuwa shine Yaya Halifa ya min kamun kazar kuku, kasan Allah da girma yake yau kowa ya jiki yace min a gidan nan, to alamun rashin lafiya ya bayyana kanshi a gare ni, yanzu haka fa kwance nake ka kira ni, Innarmu ta aiki Abba ya siya min magani. Kasan abin da nake mamaki yanzu haka bai dawo sayen magani ba kaga har na warke da ka kira ni.. Halifa ya saki dariyar da bai san yana yin irinta ba. Yace Asiya kin iya wasa. Tace "Kila in na rantse da girma Ubangiji zaka yarda ba wasa nake ba a cikin duk maganganu na yanzu haka da zan ganka bansan kuma me zanji ba." Yace ko in zo kasuwa zanje yau. Kaje kasuwar ka, amma zan roki wata alfarma a gurinka. * Yace Na miki. Tace "Zaka iya tunani duk awa daya ko ta yi yawa?" Halifa yace zan kokarta. Amma baki tambaye ni ko na cire son wata ba da nace zan cire? Asiya ta tashi zaune. Kar ka wahalar da kanka gurin cirewa nice mai hakkin cire maka shi. " Yarinyar ta tashi kan Halifa sosai wanda har ya kasa shan kunun ya fita ya rufe dakin ya bar kunun a ciki, sakamakon yana tafe suna wayar har ya isa kasuwa sai da yaran shi suka soma bude shagon ya ce mata zai kira anjima. Famcenter a nan ne Halifa yake kasuwancin sai da waya da kayan gyaranta. Shaguna ne guda uku a hade shake da kaya kuma sari yake bayarwa domin kai tsaye daga Chaina da Dubai ya ke kawo su. Da shi yake zuwa daga baya kuma sai dai oder tunda ya shahara. Tabbas Halifa ya gaji dukiya daga gurin mahaifi sa Alhaji Umaru Madugu wanda tsohon attajiri ne, haka kuma 'Yan uwan shi da suke uba daya duk attajirai ne yanzu haka. Gidaje kawai Halifa yana da sama da goma banda wanda suke ciki da su Anty hatta wanda Bros ya zauna da matar sa na Halifa ne. Banda stor stor na aje kaya da ake haya, Shaguna a kwari da Singa duk ya mallaka. Saidai shi Sam bai taba damun kansa ba tun da aka tsakura mishi mikiyan a shirin bayan ya kammala digirin shi a Jami ar Bayero ta Kano ya fara kasuwanci lokacin ne aka ba Bros aron a shirin din shima ya shiga kwari. Duk da Anty ta na yadda take so da kudin Halifa amma ta kasa wadata kullum ya zata mallaki fin haka saboda akwai lauyoyin su na iyalin gidan mahaifinsa masu lura da shigi da fice kudin. Halifa ke biyawa yaranta kudin makaranta kuma ya kawo abincin gidan Dadi cefane kawai yake yi, har su Nihal da Nur yaran Bros tunda suka dawo gidan lokacin da Anty ta sa a saki Uwar su da za a sasu makaranta Halifa ta fadawa ya bada kudi aka kai su, Bros lokacin ya samu karayar arziki Anty ta ce matar sa ce Malamanta suka fada mata, dan haka tace ai ta zage ta dole a sake ta. Halifa na cikin wadanda suka taso Bros saboda shi ya dogara akan inhar ta zagi mahaifiyar sa to ta cancanci saki, shine Bros ya yi kamar ya sake ta. Anty ta kara imani ganin yadda harkokin suka sake budewa Bros bayan ya saki matar sa kamar yadda ta ke zato. Duk wani hakkin Allah kamar zakka Halifa baya Wasa gurin cireta, ga sadaka kullum a kasuwa akwai mutanan da shi suka dogara banda daidai kun almajirai. Baya yin rayuwar karya ko kuma ya nuna kansa a me kudi ko kamar mara shi. Har zuwa yanzu da ake daf da daurin aure Asiya bata san waye Halifa ba, abinda take hasashe a ranta shine yana neman kuma ya samun abinda zai iya rike ta da shi, ko Keke bata sa rai ya na da shi ba bare wata mota. Hajiya Talatu ta shiga Rudani ganin magani bai yi tasiri a gurin Halifa ba, wannan ya sa ta fadawa Sahibar ta zata je wata gaisuwa a Wudil ta juya ta nufi Zariya gurin Malam na shuri, ita kuwa Anty sai ta yarda cewa Malamanta sun turo Aljanu sun cire bison kamar yadda suka yi mata Alkawari. Sai da suka shiga Adaidaita sahu Sannan Anty ta kallo Hafsi in munje fage zaki gane gidan da kuka kai Kaya? Gaskiya in dai ba ta layin ya shiga ba to gaskiya bazan gane ba. Dan Adaidaita yace "Hajiya Fage tana da yawa in baku San gidan ba ku kira waya." Anty tace kira Halifa ki masa siyasa ya fada mana sunan layin. Ta kira ya kai sau biyar bai daga ba, dan haka suka yita yawo, sai Hafsi ta ga kamar layin ne da sunje sai ta ga ba nan bane.. Cikin sa a ta hango Sulaiman a shago suna ta dinki shida yaran sa. Tace yawwa Anty ga Sulaiman can abokin nan na Uncle Halifa kinsan makotan su yarinyar ne. Tace Shike nan wahalarmu ta kare, bari mu same shi. Dansahu yace kodai tawa wahalar ce ta kare. Anty ta Kalle shi, wai kai da kake ta damun mutane da mita, ba kudi ka fito ne ba? Yace "Sune Baba." Tace to in zamu kai wata muna yawo baka da matsala shiyasa ko farashi ban tambaya ba dan haka ka daina damu na. Sulaiman ganin Hafsi ya gane su. Bayan sun gaisa Anty tace gidan su amaryar Halifa muka kasa ganewa, yace Allah Sarki muje in kai ku. Ya fito yana saka takalmi.