Sashe 8
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bilkisu ta shirya tsaf da safe ta hada abin kari ta nufi Asibiti ta samu labarin rashin lafiyar Halifa ne daga bakin Hafsi lokacin da Bilkisu din ta kira ta domin ta samu tabbacin abinda Asiya ta fada mata. Sai Hafsi tace mata ba shakka haka ne yanzu wata zai aura kuma a wannan ranar sai dai yanzu haka yana Asibiti bashi da lafiya. Mahaifiya Bilkisu itace ta hada abinda za a zubawa Halifa a abinci dan sake maido shi ga Bilkisu suna son su gyara abinda suka bata. Halifa ya kosa likitan ya shigo ya bashi sallama domin kwanakin biyu bai leka kasuwar shi ba, yau kam zai fita. Anty da Dadi suka shigo da sallama Tace "Alhamdulilah jiki ya yi sauki Amma na tsorata jiya Halifa." Suka sa dariya, suna cikin gaisawa Bilkisu ta shigo da sallama bisa Jagorancin wata Nus. Halifa ya kalleta sai kuma ya kauda kai yana jin su Anty suna amsa gaisuwarta har ma da bata gurin zama, zuciyar shi ta shiga harbawa da sauri, tabbas yana son Bilkisu har yanzu fa. Ta ce "Yaya Halifa ya jikin? " Yace da sauki ba tare da ya kalleta ba. Bros yace nifa ina son inje in fita da wuri yau muna da baki a kasuwa. Halifa ya kalleshi ya yi murmushi domin ya tuna da hirar su ta dazu. Yace to ya kamata ka tafi nima dai in likitan nan ya kai goma bai zo ba Allah zanyi tafiya ta. Anty Tace "Zuwa ina ai ka kwanta sai gobe ka kara warware wa. " Halifa yece kin san Allah Anty ba zan wuce goma ba, karma ki bata baki ki. Anty ta yi shiru tana tunani inko haka ne dole ta koma gida kafin goma domin ta sa a nemo gurin da Sahiba da yarta suka yi biso. Bilkisu ta katseta da fadin Anty ga abinci a ba Yaya Halifa. Anty ta kalleta to an gode zuba masa ya ci. Halifa yace na koshi ina godiya sosai ki koma da shi. Bros ya fice Anty ta kalli Dadi zo muyi magana ta jashi waje da fatan su daidai ta zata fiye mata waccan yarinyar. Bilkisu ta tashi da sauri ta zube gwiwoyinta a gana gadon da Halifa ya ke zaune tace "Halifa dan Allah Don girma da darajar mahaifanka ka yafe min wallahi na yi kuskure. Bazan sake yin wani Abu mai kama da haka ba kar ka fasa aurena Halifa ina son ka. Kaima na sani Halifa kana sona." Halifa ya mike tsaye ya bata baya Ki tashi Bilkisu na yafe miki tun a ranar, sai dai kin makara domin zance na da Asiya ya yi nisa, ki gyara a gaba. Maganar so gaskiya ne ina sonki sai dai dama ba kowane abu bane da ka ke son shi ka ke samu. Ki yarda cewa labarin soyayyar mu ya kare tun ba a fara cin gajiyar soyayyar ba. Bana son ki tsaya Kiyi ta magiya domin ban cika maimaita magana ba duk da nasan baki cika fahimtar hakan ba. Tafashe da kuka, ya fice a dakin domin bazai jure ba. Anty ta biyo shi har harabar Asibitin inda ya zauna a kofar masallacin Asibitin. Tace Me ya faru kuma naga ka fito. Yace "Anty dan Allah ki ce ta tafi ko kuma ni in tafi." Wani takaici ya zo wa Anty wuya, tana bakin cikin yadda Halifa ke kara fito da wannan shegen ra ayi na shi. Tace Yanzu Halifa ni ban isa ba sam bani da wata daraja a idon ka. Sai yadda ka ke so? Kala baice ba ya nufi hanyar fita. Da gudu ta nufi Dadi ta kira shi tace yabi Halifa. Ko kafin su fito har ya dauki Keke napep tunda bakin titi Asibitin yake. Dady yace "Wai me kika fada masa ne haka gaba daya Yaron nan a rikice yake fa tun da ya samu matsala da yarinyar nan wai ma me ya kawo ta ne.?" Cike da jin haushi Anty tace Kaga dan Allah ka sama min lafiya ina ce muna tare da Kai ta shigo sai kuma ta ja tsaki ta fice daga Asibitin domin bata bukatar Halifa ya shiga gida saboda binne binnen Sahiba. Asiya ta wayi gari kamar mara lafiya domin bata samu kiran Halifa ba, ga kuma batun waccan da ta kira ta duk da tana ta son ta nuna wai kamar abin bai dame ta ba. Gabanta yana tsananta faduwa idan ta tuno da wani mafarki da tayi wai wasu macizai suna ta kaiwa Halifa sara shi kuma yana ta fesa musu wuta da bakin shi. Ta shiga gidan su Sulaiman ta gaida mahaifiyar su sannan ta ce, ko Yaya Sulaiman ya na ciki? Ya fito ta gaida shi da girmamawa. Yace ya aka yi ne Asiya ta nufo waye sai ya biyo ta. Ta tsaya a soro ta dube shi cike da kunya tace Amma ka samu labarin Yaya Halifa kuwa? Yace "Me ya faru jiya dai kafin ya zo gurinki ya biyo shagona yace in amshi dinkunan ki na biki nace masa sai yau zan saka yarinyar shagona ta zo ta gwada ki ta amshi kayan nan da shabiyu ta ke zuwa." Asiya tace jiya ya bani wayarsa ka gan ta, kuma yace zai kira ni, sannan kuma bai kira ba. sai naji kuma kamar wani abu ne ya faru da shi. Sulaiman ya yi murmushi," Ki kirashi shi mana to da wannan Wayar." Ta girgiza kai bayan ma ban iya wayar ba kuma akwai lambobin sirri, banda hakan ma bai bani Umarnin in kira ba, yace shine zai kira. Sulaiman ya ce Ina zuwa. Ya dakko wayar shi ya danna kiran Halifa. Bayan sun gaisa yace kana ina ne haka.? Halifa yace "Yanzu na shigo gida Asibiti na kwana jiya bayan na bar unguwar ku sai a mai nake ta yi wai ance Ulcer ce." Sulaiman yace Subhanallah Allah ya baka lafiya. Shiyasa mutuniyar tazo min ka ga ta nan wai taji a jikinta kamar da wani abu kace zaka kirata baka kira ba. Halifa Yace" Allah sarki kace zan kirata. Bilkisu ta dauki abincin ta cikin kunan rai ta nufi gida ba a taba wulakanta ta kamar haka ba. Suka yi jugum ita da Uwar suna lissafin mafita. Ina zata sami malami me zafin hannu wanda aikin shi zai zama sha yanzu magani yanzu. Can ta mike tare da fadin duk wanda ya ci tuwa dani miyar ma baisha ba. Halifa zai gane shayi ruwa ne tashi mu tafi indai na haifu sai Halifa ya zama abin sarrafawar ki. Hafsi ta kawo masa wani makullin domin bai San yadda ya yi da na hannun shi ba jiya. Anty ta shigo ta kwada masa kira tun daga bakin gate ya tsaya bai bude dakin ba, tace Halifa ka fita waje gidannan an binne wasu asirai saboda kai bari a tone ko kaje gidan Bros tunda shi kadai ne na dan wani lokaci. Halifa ya yi murmushin takaici ya fara gajiya da wadannan zantukan, shi baima fahimci me take fada ba. Anty kije ciki kawai ki huta dan Allah bana gane me kike cewa. Tace Halifa kana cusa min bakin ciki da wannan gaddamar taka, dan Allah iya yau ka saurare ni in ceci rayuwar ka. an binne mugayan asirai dan a cutar da kai a gidan nan. Yace "Anty waye shi a gidan nan da zai min wannan mijinki ko yayanki haba Anty dan Allah karki ruda kanki mana." Hajiya Talatu ta kara so tana fadin sannu mai jiki, yanzu nake cewa Sahiba nace mata zani duba ka sai suka wuce bata tashe ni ba. Halifa yace na samu sauki sosai. Anty tace Halifa In mutum zai cuce ka ai ba sai na gida ba, amma tabbas gidannan anyi binne binne saboda kai, ta kalli Hajiya Talatu wadda ta zaro ido cikin faduwa gaba tana sake tambayar Anty waye kuma zai masa hakan.? Anty ta yi murmushin yake, Sahiba kenan ke dai ki ga mutum ni dai kawai ya fita. Halifa ya dafa kafadar Anty yace kiyi hakuri babu wani abu da zai same ni wanda Allah bai kaddara min ba, karyar mutum ko aljani. Ya jiya ya bude dakinsa ya shige. Shirin kasuwa ya yi yana fitowa falonsa Hafsi na kawo masa kunu yace a sa sugar a ciki? Tace "E" Yace je ki kawo min mara sugar. Tace "Sai dai a dama." Yace to ayi hakan bakina babu dandano. Kafin ta kawo sai ya yanke shawara kiran Asiya. Tana kwance kan yar yaloluwar tabar marta baza ta iya fassara halin da zuciyar ta ke ciki game da Halifa ba, amma dai da ace akwai dama to zata so ta ganshi ta ga jikin shi ta kuma bashi wata kulawa wadda zai samu sauki. Kamar daga sama wayar ta soma kida, ta dauka da rawar hannu sannan ta sa a ku ne bayan ta tashi zaune, sai kuma abin ya motsa wato jin kan. Tayi sallama a natse, ya amsa, ta gaida shi gami da tambayar jiki, yace da sauki. Tayi dan dim saboda yadda ta ke jin muryar shi tana ratsa dodon kunnen ta. Yace to ya shirye shirye nace Sulaiman ya zo ya amshi kayanki. Ta lumshe ido,. "Ya fada min dazu zan bashi." Yace kin gano nawa ne ake yin gyaran jikin? Tace a a ai ban ma san wa zan tambaya ba, domin Maman Annur a bikin ta ita ta yi a gida na kurkur. Yace to bari zan bincika sai in kai ki ko baza ki bini ba? Ta yi yar dariya. Bana tunani su Baba za su hanani zuwa tunda kai ne. Yayi murmushi salon maganar ta yana birge shi. Sai me ki ke bukata bayan wannan kamar paty ko Walima haka? Kamar munyi wannan maganar ranar da ka zo nace saboda jikin Baba baza yi komai ba, garama dai walimar tunda akwai lada a cikin ta." Halifa yace haka ne yarinya da hankalin manya. Yaci gaba da fadin ina fatan baki ji haushin abinda masu shagon nan suka fada Akan ki ba jiya? Ta yi yar dariya " Zan iya tambayar ka? " Yace Sosai ina sauraron ki. Tace," Abinda suka fada ya kankare wani abu na daga kima ta a gurinka?"