Sashe 45
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Take Halifa ya sa hannu aka soma yi mata shirin shiga tiyata. Ana yunkurin saka mata ledar fitsari sai wani nishi yazo mata kafin su yi wani yunkuri haihuwa ta zo. Halifa yana ta kai kawo yana ta addu'a Allah ya sa a yi aikin cikin nasara. Gashi ba bu dama ya kira kowa kar a san inda take. Aka fito masa da jariri nade cikin tawul ya sha kayan sanyi likitan da kanshi ya miko masa ɗan yaro namiji .kyakykyawa yana fadin na taya ka murna. Cike da farin ciki da kuma rawar jiki Halifa ya amshi gudan jininsa hannunsa na rawa dan shi ba ya iya daukar jarirai.
Yace "Yanzu wannan da na ne? To ita kuma Mamansa din fa tana ina ne?
Likitan yace tana cike da koshin lafiya ina yi maka albishir da cewa ta haihu ne da kanta. Yanzu nurse za su gyara ta. Halifa ya ce "Alhamdulillah " To bari mu zauna mu jirata,goron albishirin ka kuma sai mun samu nutsuwa. Likita yace sai a kira wayar a sanar da yan uwa da abokan arziki. Halifa yace zan sanar da su.
Bayan likitan ya koma ciki Halifa ya shiga tunanin yanzu shikuwa ya zai yi gurin kula da ita da kuma jariri ita kanta bata san ma ya zata kula da kanta ba bare Yaron.
Ko ya kira Inna? Kai Inna zata raba su ne.Anty kuma bai gama binciken da yake yi ba,Allah ya rufa asirin su kuma har yanzun ba a san suna tare ba.
Ya tashi da sauri ya nufi office din likitan yana rungume da dan a kirjin sa. Likitan ya taso yana cewa a kwai wani abu ne? Halifa yace a a, Ina son ka ba ni wata nurse da zata kulamin da su a gida kamar yadda zata kula da jikinta da kuma shi yaron nata. Likitan ya dan yi mamaki har ya kasa shiru, yace amma wannan mai sauki ne da ka sanar da dangin ka,ko nata.
Halifa yace "Ka san kowa da irin nasa tsarin ni kuma dai haka nawa ya ke. Likitan yace To wannan ba zai zama matsala ba, za a duba nurse guda daya da kuma dattijuwa ko a cikin masu kula da tsaftar mu ne sai mu baka suna zuwa suna duba su.
Asiya kamar ba ita ce ta haihu ba, tana zaune a mota rungume da danta ta kafa mishi ido tana jin wata kaunar sa, suka nufi gida. Halifa yana tuki a hankali kamar ya dakko kwai.
Asiya ta kalle shi cike da murmushi tace yana kama da ni fa. Halifa yace "Ko dai da ni, ki kalli fuskar shi sosai ki kalli hancin. "Asiya tace da kuwa anyi kyakykyawan yaro Allah dai ya yi masa albarka. Halifa ya sa hannu ya shafi kuma tunta Ameen Babyna.
Kwanciya ta yi dama likita yace ta ci abinci ta sha magani ta kwanta ta huta tunda Halifa ya matsa kan cewa su tafi gida..Halifan ne ya hado mata shayi zafin ruwa baya baya ta sha ta kwanta. Shi kuma dama Halifa ya kwana gadin su sai bayan ya yi sallar asuba sanna ya kwanta.
Kuka Yaron ya tada Asiya bata san ya zata masa ba.gashi tana tausayin Halifa ya samu bacci.
Ta dauki wayar sa ta fita falo ta duba lambar likitan ta kira shi,bayan sun gaisa ta ke sanar da shi yaron ya ta shi yana kuka. Yace ina baban tace yana bacci, Likitan yace yunwa ce kawai ke damun baby zan masa text na madara sai ya siyo yanzu kafin ruwan nono ya zo,ki ci abinci ki sha shayi sosai da kunun kanwa dan ki samu ruwan nono da wuri, kar yaron ki ya rame. Asiya tace to tayi godiya.
Kukan yaron ya farkar da Halifa,ya ce "Ya baki tashe ni ba?" Ta fada masa yadda suka yi da likitan yace To bari in je neman madarar ya dauki makullin mota da sauri ya fita yana kiran wayar likitan yana fada masa abinda zai siyo wanda maijego da jariri ke bukata a yanzu.
Ya dawo ya samu yaron yayi bacci. Ba jimawa Nurse Anty Amina da gyatuma Wadda tace Hajjo ake ce mata, suka iso. Anty Amina tana tsaye Hajjo ta wanke yaro tas sannan ta yi wa Asiya wanka ta gasa mata jiki. Ta ci abinci ta fito fes.
Anty Amina ce ta nuna wa Asiya yadda zata hada mishi madara da kuma yadda zata bashi, sannan ta gargadeta akan cewa da tasamu ruwan nono to fa ta aje madarar nan nonon Uwa shine abu mafi amfani a gurin jariri. Ta dubi Halifa tace Ranka ya dade ai ni ba sai nazo kullum ba jifa jifa zan ke zuwa, amma ita Hajjo sai ta zo kullum sai dai ku samu mai aikin gida kuma kafin matar gidan ta yi kwari. Halifa ya yi godiya tare da bata kyautar kudi.
Hajjo tace akwai wata jikarta ta zo daga maiduguri in suna so sai take zuwa tana ta ya Asiya girki da kuma shara. Halifa ya ce ba damuwa su rinƙa zuwa.
Kwana biyu Halifa ya kwashe bai leka kasuwa ba, ga abin fadi babu dama shi ya yi wa dan sa huduba da sunan mahaifinsa wanda shima shine sunan sa wato Umar.
Halifa ya samu Sulaiman ya ce, Dan Allah zan baka wani aiki ne, na fara shi ni kadai amma naga bazai yiwu ni kadai ba.
Tun lokacin da aka yi posting din video wanda ya shiga dakin mata ta, na ke bi comments na mutane duk posting din da na gani lokacin na dauki lambar wani wanda yace shege Mansur kayi nayi yau Kaine kuma da kwartanci. Na bibiyi wanda ya yi wannan rubutun ta hanyar number sa da ke a kan shafin sa, na ga cewa tela ne shi,dan haka na bukaci zan kai masa Dinkin mata ta. To abinda nake son ka min guda daya ne,zan baka kaya ka kai masa a kofar ruwa yake,sai ka ce masa kai ne kuka yi chatin da shi,ka kira shi da lambar ka,kace masa shine daya layin ka.
Sannan ina son ka tambaye shi Mansur kayi nayi,cikin hikima na san dai ka san me zaka yi,sai muji ta inda zamu same shi.
Sulaiman yace "Ka yi dabara,amma kuma ba abin ya wuce ba?"
Zai dai wuce insha Allahu iya shi in na kama zuciyata zata samu saukin domin zai fito min da duk wanda ke da hannu akan komai.
"Haka ne Sulaiman ya fada cike da kwarin gwiwa. "Zan kokarta in ga na yi maka wannan insha Allahu za mu samu nasara.
Bros bayan amarya ta tare ba yabo ba fallasa tana ta kokarin farantawa ango dan haka ya zubar da komai ya kula ta aka sha amarci, sai dai tun safe yake barin gida sai kuma dare, can yake tafiya gurin maman Nihal ya yi wanka ya yi shirin kasuwa, da ya ke su maza yayan Baban su ne,sai yake nuna mata bai yi komai da amaryar ba,ita kuma tana ta lallashi wai ya kula ta saboda hakkinta da Allah ya dora masa.
Zuwan Anty uku gidan bata samun shi amarya kuma ta tabbatar wa da Anty cewar gida yake kwana sai dai yana fita da wuri dan wani lokacin ma a gidan wanka na kasuwar ya ke yin wanka ya canza kaya. Anty tace "gi
Gidan wanka kuma duk bandakunan da ke gidan nan amma ace sai ya yi wanka a kasuwa? " To rigima kuke yi tace a a lafiya lau muke.To yana cin abinci ko baki soma girkin ba?" Amarya tace Gaskiyar magana bai tabacin abinci na ba. Fitar wuri yake yi, in ya dawo kuma sai ya zo da nama ko kaza. Anty tace "Kuma ke hakan ya miki?Amarya ta fara jin haushin tambayoyin Anty dan haka tace Umm.Anty ta fahimta yarinyar bata son maganar tace Nifa kamar Uwarki ce shiyasa ki ka ga ina tambayar ki domin in ya miki ba daidai ba in taka masa birki,amma tunda ke kin ce ba matsala shike nan .
Ta mike tana fadin ni zan tafi. To ki gaida gida. Har ta kai bakin kofa ta tsaya, ke kuma haka ki ke yi wa bakin duk wanda ya zo ba dan cincin ba lemo ko tayi ruwa zuwana uku fa. Amarya tace "Na ga ai an kai muku na ku ne cincin din da sauran kayan gara,nawa na baki ne,ke kuma Anty ai ba bakuwa bace. To ruwan kuma fa shima bazaki iya bani ba. " Dan ruwa sai in baki mana ruwa dai Allah na tuba dawo ki sha."Amarya ta fada tana yatsina baki. Anty tace Allah ya amfana,na yi miki magana ne kar wani ya zo bare a yi masa haka ni ai ta gida ce. Amarya ta yi yar dariya. Anty dama ai dan ke ce shiyasa nima na yi haka.
Maganar ta doki Anty ta dawo ta tsaya, kina nufin idan Uwarki ta zo gidan nan itama haka zaki yi mata?
Amarya tace "Anty ina tabbatar miki daga nan har in shekara ba lalai uwata ta zo gidan nan ba matsawar lafiya lau,ita kuma haka Allah ya yi ta da kamun kai zan ce ko kawaici,bare har ta doko sammako,to kin san Allah Anty gidan Yayanmu shekara biyu matarsa ta haihu sai lokacin ta taka gidan ta yi musu barka,in anyi maganar bata je ba sai ta ce me zakaje gidan yaro ka yo masa, indai suna lafiya haka ake so,ni bana wannan gayyar sa idon da kwakwafi, da kalan nema raini gurin yara. Anty ta gama gane yarinyar nan ta fake da Guzuma ne take harbin Karsana. "Wato ni ki ke yada wa magana baki san ni ba ko? Kiyi a hankali kar ki dakko irin wannan ta kun tsakanin mu, an bini ma ya aka cika bare kuma Anja da ni. Amarya ta ce kiyi hakuri Anty yadda ki ke zato ba haka nake nifi ba.Anty taa wuce fuuu a fusace. Amarya ta raka ta da harara tana fadin nima din ba sani na ki ka yi ba.