Sashe 29
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A tsakar gida kuwa kwarto ya gudu Halifa yaji takaicin haka domin ya so yasa a daure masa shi. Ya shiga dakin a fusace Asiya wadda ta gama sarewa ta dube shi. Yace "Wai Asiya in tambaye ki, dame na rage ki har ki ke kula wannan kazamin daga gani ko sana'a bashi da ita. Ko bana iya gamsar da ke a shimfida ne? Asiya sai Kallon shi take ba shakka ya gama yarda cewa ta aikata laifin.
Ta mike ta shiga daki ta gama amincewa auren su ya kare ta sauke akwati tana duba kayan da zata dauka a kayanta na gida dai kala daya ne wata doguwar rigar atamfa Dan haka ta ciro ta da wani hijabbinta na idin da akayi kafin auren su. Ya shigo dakin lokacin ta gama sakawa ta duba jakar ta ta dauki dan kudin ta wanda yakan bata. Ya ce ina zaki ko binshi za kiyi? Ta dube shi cikin wani yanayi wanda bazata iya fassara shi ba. Duk abinda aka yi ba sukai wannan kalmar da ya fada mata yin daci a zuciyar ta ba. Hawaye suka kwaranyo daga Idanuwanta. Cikin rawar murya tace "Ka yi duk zargin da zaka yi bazan hana ka ba. Gaskiyar ita ce, ban aikata komai ba, banda masaniya akan komai, sannan yanzu kuma gidan mu zanje. Zaki je ki tona wannan maganar ta yi ta yawo cikin mutane? Abinda ya sa ban samu ba koda wancan yaron ya gudu bana son in kai shi gaba maganar ta zama abin tattaunawa a satin nan, can kuma abin ya koma Soshiyal midiya. Asiya tace ni ba zan damu ba ko waye ma zaiji ya ji kuma ba zan hana shi yarda ba tunda kaima ka yarda. Kuskuren da nayi na dauka cewa zaka bani kariya a matsayin ka na mijina ashe nayi kuskure. Ta fito fallo ya biyota ban fa baki izinin fita ba. " Halifa bana bukatar izini domin aure da zargi basa haduwa." To kin fi son kije ki tada hankalin Inna gata da hawan jini? Asiya tace bari kaji Inna tafi kowa sani na, ko a mafarki bazata taba yarda da wannan wasan kwaikwayon ba.
Ta kama kofa ta bude yace Cikina kar kije min dashi ko ina. Anty dake bakin kofa ta a she. Ta ce ta ina ya zama cikin ka, kana jin me cikin ya fada? Ka barta taje gida tunda tana gaddama cewar bata aikata ba sai ka bincika ka samu Tabbaci. Halifa bai ce kala ba har Asiya ta fice.
Shima ya rufe dakin ya fice. A baya yake bin Napep din da ta hau har Unguwar su.
Asiya ta shiga gida Inna tana kwance Abba yana girki Maman Annur taje gidan aiki. Inna ta tashi zaune tana fadin Asiya ce yau da wuri haka? Asiya tace inna ai ba zuwan dadi bane. Nan ta kwashe komai ta sanar da ita. Inna ta shiga salati da sallallami tace yau kuma da haka na wayi gari. Allah ka fidda wannan yarinyar sai kuma ta shiga lallashin Asiya tare da bata magana. Inna dai ta boye wa Asiya damuwar ta ne kawai amma fa ta shiga tashin hankali domin duk yadda Asiya take Kallon abin ya fi haka, ga shi su ba karfi ba ta yi imani Asiya bazata taba aikata abinda aka danganta ta dashi ba.
Da dare Halifa yana ta kai kawo daga falo zuwa daki yana auna abin da ya faru wata zuciyar tace kai. me yasa baka zo ka shigo dakin ba a lokacin? Ya tuna yadda Anty ta rike shi tana karkaje kar ayi mugun abu, zaka yi mugun gani. To amma gashi yana kokwanto kodai sharri ne aka yi mata masu bata guba din nan. Ya kamata ya fahimci cewa lallai akwai wani abu. Ya fita zuwa sasan Anty tana waya da ƙawarta Wai ta kira tana cewa ta ga abinda ya faru a gidan an dora a tiktok. Anty tana cewa wallahi kuwa nima dazu Hafsa ke nuna min ko suwaye suka dauka suka dora ga shinan shi kwarton an masa duka ita kuma Asiya tana ta kuka, aiko ta sha zagi. Halifa yace Anty me aka dora a Tiktok? Matar tawa aka dora? Waye yake da tabbci ko shedar cewa zina ake aikatawa adakin? Waye ya yi musu kamu irin Na shari 'a?
Anty ta juyo da sauri cike da mamaki ta kalli Halifa tana murna ta zare masa yarinyar daga zuciya yanzu Sai batun zubda ciki amma shine zai mata tsalle? Ta mike a fusace " Halifa idan har na isa da kai wallahi sai ka bar yarinyar nan. Wane irin asiri ta yi maka haka wallahi ko waye ya tsaya maka sai ka barta ba dai a zuri a taba. Halifa yace Anty gaskiyar magana ina son mata ta kuma zuciyata ta ki amincewa da cewar Asiya ta aikata wannan abin in halinta ne da ta yi kafin ta zo gidana amma yarinyar nan a budurwa na same ta, ni ne mutum na farko da na fara kusantar ta. Bazan manta hakan ba. Dan haka saina bincika sosai kuma duk wanda na gano da hannun shi a dauka ta a Video ya yada sai na yi shara a da shi.
Ya Juya a fusace. Baki Anty ta saki ta bishi da kallo lallai wannan sai ta yi da gaske.
Yana shiga daki ya dauki waya Sam bai damu da hawa Internet ba, amma sai ya kunna data da nufin duba Tiktok. Kiran Bros ne ya katse shi ya daga cikin sauri domin yana bukatar jin ta bakin wani. Cike da tashin hankali yace Uncle me yake faruwa ne dazu maman Nihal take nuna min Matar ka a Tiktok. " Ina zan same ka yanzu? Halifa ya tambaye shi cike da damuwa. Bros yace ina gida kuma kaga muna da tazara Amma mu hadu a zoo road yanzu." To Halifa ya furta ba tare da ya tsaya tunani ba.
Jikin motar Halifa suka jingina inda Halifa ya zayyano wa Bros komai. Ya kara da cewa kasan menene Bros sam zuciyata ta ki aminta cewa yarinyar nan zata aikata abinda ya faru. Tana ta kawo min hujjoji masu karfi, Bros yace "To ina yarinyar yanzu? Tana gidan su. Halifa ya amsa tare da girgiza kai, ya furzar da huci, ya ci gaba da fadin ban so ta tafi ba, abinda ya bashi haushi ke nan na kyaleta ya kamata ta min uzri a lokacin domin abinda na gani ya isa hujja ko a gaban Alkali cewa ta yi laifin. Bros yace Uncle Baka da wata hujja da ka ke fadin ko a gaban Alkali ka yi mata kamun shara a ne. Ina son ka nutsu ka saurari zuciyar ka wadda ta ki amincewa da zargin da ake yi wa matar ka, kuma dorashi da akayi a Soshiyal midiya ya kamata kasan cewa akwai masu yakar ka da nufi aka yi Allah kuma shine ya san masu yin da kuma dalilin su na yi din.
Halifa ya sauke ajiyar zuciya yace yanzu ka bani shawara menene abinda zanyi? Bros yace ka fara kare matar ka daga sharrin yan Soshiyal midiya dinnan Sannan ka sameta ka bata hakuri kuma ka tashi daga gidan nan ka koma gidan ka. Halifa yace tafiyar da ta yi bayan na hanata ya bata min rai sosai har yanzu ina jin haushin abin. Bros yace ka bari nan da sati daya kowa ya huce kai da ita sai kaje ka same ta ku sasanta.
Da safe ya gama shirin fita ya dauki kayan sawar Asiya da wayarta ya je har kofar gidan ya ba wani yaro yace ya kai yace gashi a bawa Asiya. Tana kwance ta kasa karin kummalo ta rasa yadda zata yi tare damuwar ta. Bata San tana mugun son Halifa ba sai yanzu da auren su ke gargarar mutuwa. Ta tabbatar in har auren nan ya mutu ita ma mutuwa zata yi.
Sai ga yaro da kaya niki niki wai inji Halifa. Ta kalli Inna hawaye suka zubo mata tace ya tabbata Haliifa ya gama yarda cewa na ci amanar sa. Inna cike da tausayawa yar ta cikin lallashi tace. "Bana zaton hakan yana nufin ya yarda muci gaba da addu’ar neman mafita ga Allah.
Sallamar Sulaiman ce ta dakatar dani take na fara rokon Allah ya sa tare suka zo da Halifa.
Na fito daga daki ina fadin sannu da zuwa yaya Sulaiman. Ko amsawa bai yi ba ya shiga tambayar Asiya wai kuwa me kika aikata na ganki a Tiktok? Gaban Asiya ya yanke ya yi wata muguwar faduwa, Wani sabon Sharrin ya sauka kenan, ta furta tana Kallon idon Sulaiman. Ya ce kalli kiga ni yadda abin ya yadu mutane sai sharhi suke yi suna kara yada abin. Asiya ta gama kallo gaba daya zuciyar ta tana bugawa da sauri, ta mika mishi Wayar ta koma ta zauna Sulaiman ya ci gaba da fadin wallahi nasan sharri ne sai dai na yi mamaki yadda Halifa ya yarda. Asiya tace dole ya yarda ta fada masa duk yadda abin ya faru da kuma yadda ta sani.
Sulaiman ya yi ta mamaki tare da yi mata addu"a Allah ya fidda ita, sannan yace yanzu ya za ayi da mutanen Soshiyal midiya din nan? Yan jarida ma nasan in suka ji labari sai sun zo gidan nan yadda abin nan ya yadu kyau ki bar garin nan zuwa nan da kura ta lafa. Inna ta fito cikin mamaki tace "Abin har ya kai Haka? Gaskiya dai ina ganin ba sai taje wani guri ba, kawai dai baza ta fita ko ina ba." Sulaiman yace to shike nan Amma ina mai tabbatar miki cewar yanda kowa ya zama dan jarida yanzu ba sai ta fita ba, har gida zaki ga ana zuwa domin gani da kuma jin ta bakinta. Asiya tace inaga zan zauna a daki kawai. Sulaiman ya ce Allah ya kyauta ya fita.