← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 62

Sashe 33

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anty tace Allah na tuba tunda ba wasu masu hali bane Uwar ma kamar wata sakarya a gaban ta ma sai mu bata. Haka dai suka gama kulle kullen su suka tashi.
Inna tana wanki na wankau da aka kawo mata, sai taji an doko sallama. a murya bibbiyu ta amsa tare da daga kai ta kalli su Anty duk da gabnata ya fadi amma sai ta dukar da kai ta ci gaba da wankinta bayan ta amsa sallamar a zuciyatar ta ci gaba da adduo'in neman tsarin Allah daga sharri su.
Anty tace Ko da kika kallemu kika watsar muma ba zama muka zo ba, ina yar iskar yarki mai bin maza gurinta muka zo za ayi gwajin kwayar halitta dan musani ko cikin ba jinin mu bane.

Inna bata tanka ba Hajiya Talatu ta fusata, tace "Ke baiwar Allah dake muke magana, kamar ke matsiyaciya har kin isa muna magana ki yi mana banza?
Inna ta sake dago kai ta dube su tace, Wai me yasa Mutane suke hana kansu sukuni saboda son zuciya kuma su hana wani? Anty ta ce ba gurin ki muka zo ba, mun zo ne gurin yar iskar yar ki ta zo muje a yi gwaji dan mu rarrabe domin bazamu dauki dan wani a matsayin dan mu ba, yawwa. Inna tace ikon Allah to bari in fada muku babu inda Asiya zata kuma ciki dole ku karba duk sharri da tuggu da kike shirya wa yarinyar nan da wani kaita gidan boka ko ki bata guba duk na banza ne domin zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho sai ya yi ina son ki sani tsakanin dan Asiya da Halifa sai yazo Duniya kuma sai ya gaji abinda ki ke kwadayin mallakewa.!!! Kuma kina raye zaki ga haka!!!

Ke!!! Anty ta daka mata tsawa. Taci gaba da fadin Ina son ki iya bakin ki ki kama kanki banda dalili ke kin isa ki fada min magana? Yar wanke wanke na tafi ki komai banza talaka matsiyaciya.

Ga ki matsiyaciya kina gorin arziki jahila baki san cewa wanda yake rabon arzikin shine Ubangijin talaka ba, kuma hakan ba yana nufin ya manta dashi bane. Kije ki nemi ilmi. kuma ku fitar min a gida ta dauki ruwan dauda na wa kin data tsoma tsumman share ruwa ta nufi kansu da shi tana fadin babu wanda bai iya tijara ba sai in bai so ba!!! Ta sheka musu a jiki ta nufi ruwan zafi dake kan wuta tana dumamen tuwo,. Tace sai in kona ku ku kukazo har gida. Da sauri suka yi baya sai dai tuni Inna ta wanke su da ruwan datti kuma tana fadin Auzu billahi minnashaidanirrajim.

Hajiya Talatu mamakin Inna ya cika ta, wai dama tana magana? Gashi ta wanke su da ruwan dattin ta kuma wawuro na kan murhu da gudu suka fita Anty tana sai na sa yan sanda sun rufe min ke.!! Inna tace na isa dauri muguwar mace wadda ke zalintar Dan Uwan ta to haka bakin ciki zai kashe ki insha Allah mutu ka raba Halifa da Asiya.

Lamarin nan ya bataran Anty sosai ba a taba ci mata zarafi kamar haka ba tunda Uwar ta ta haife ta. Har suka kai gida bata ce komai ba tana saka abinda zata sa a yi wa Innar su Asiya ne kawai dan ta gane tazarar da ke tsakanin mai arziki da matsiyaci.

Hajiya Talatu tace Ga abinda nake fada miki, yanzu in kina da yan sanda saidai ki bada Adireshi aje kawai a aje miki ita sai jibi zakije sai a lokacin zaki fadi abinda kike son a yi miki da ita. Idan nice fa wallahi matar nan sai taje gidan yari ko na kwana daya ne.

Anty tace ko yanzu bazan barta haka ba. Bari mu canza kaya muje ofishin yan sanda. Suna zuwa Anty zata soma bayani ga dansanda dake kan teburin Hajiya Talatu ta jata gefe tace ke in kika biyo ta haka fa mune bamu da gaskiya tunda mu muka je gidan ta. Harkar girma kawai za ayi kinzo da kudi dai ko? Anty tace "A a sai dai ki Ara min." Hajiya Talatu taje muje ki ciro baza a rasa gurin POS a nan kusa ba, bani da kudin da zan aramiki ba biyana kike yi ba.

Anty tace Au harda gori kuma har nawa zan ciro? Hajiya Talatu tace dubu Hamshin shima maleji za ayi dan na sanki da shegen son kudi bazaki iya fidda dari ba. Anty ta danyi shiru can tace "Ko dai share matar nan zanyi kawai in samu mu gama da yar tata? " Hajiya Talatu tace ai kinji matsalar ki duk da munyi wanka har yanzu ina jin tashin warin ruwan dattin talaucin da matar nan ta watsa mana kuma daga yau raini ya shiga tsakanin ku. Dan taci bulus Anty ta fusata ta fita zuwa zuwa POS. Tun a can Hajiya Talatu ta amshe kudin tare da fadin kawo ki gani ba a shiga irin gurin nan da kudi ttsirara.

Suna komawa Hajiya Talatu tace D. P. O. yana ciki? Suka ce bai shigo ba,. Tace D. C. O fa suka ce yana hanya. Tace to ina son a dakko min wata ne a Fage ta ci mana zarafi daga kawai kaninmu yana auren Yarta, sai aka kama ta da wani shine mukaje gidan dan taje ayi gwajin Kwan halitta tunda tana dauke da ciki shima ta watsa mana ruwan dauda tare da zazzagi mu.

Ta sa hannu a jaka ta tsakuro kudin ta mika shi gashi ku sha mai ku kawo mana ita nan sai gobe zamu dawo.

Jiki na bari Shugaban su na gurin yace maza a dakko mota ta sake kawo dubu daidai ta ba yan gurin Shugaban kuma dubu biyar tace ku sha ruwa a hanya. Nan fa suka dauki mata biyu da maza da direban suka ce muje ina kuka aje motar ku? Hajiya Talatu da Anty suka kalli juna. Hajiya Talatu tace ai bamu zo da mota ba, me adaidaita ne gashi can motarmu mun aiki direba bai dawo ba. Dansandan yace Ku shige gaba muje ku nuna mana gidan sai ku tafi abinku.

A cikin adaidaita Hajiya Talatu tace "Kawata wallahi yau naji kunya da Dansandan nan ya yi maganar mota ya kamata ace kina da mota taki ba wai ta Dady ko ta Halifa ko Adamu ba, sai zaki Je Unguwar sirri kina hawa adaidata sahu. Kin girmi haka wallahi ke ba tsohuwa ba amma baki jan mota da kanki. Yanda mata suke baza kafasitin nan da hawa manyan motoci suje Dubai da Umara akai akai, gaskiya Sahiba akwai bukatar yiwa rayuwar ki gyaranbawul. Anty ta sauke ajiyar zuciya tace kibari dai komai ya daidaita zaki sha mamaki yanzu ina sauran kudin ko duka kika ba su?

Hajiya Talatu ta zage jakar ta tura sauran kudin a karamin zif sannan tace, "Har dubu ta da dari biyar ta shiga, kece bakuwar ba Yansanda kudi....

.
[8/20, 22:26] Ummi Tandama😇: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6H4trFsn0pEII5by1w

Suka aje mota a kofar gidan Inna suka tsai tsaya tare da tura matan ciki dan su kamo matar gidan. Sulaiman sun fito gidan su shi da Abban su zai tafi shago Abba za shi Unguwa sai kawai suka ga Yansanda a kofar gidan su Asiya. Abba da Sulaiman suka kalli juna dan neman karin bayani, amma kuma babu wanda ya san komai.
Abba ya taka kofar gidan cike da al ajabi dan jin karin bayani daidai lokacin da Matan yansanda suka fito suna cewa matar gidan tana salla sai sun jira kadan.

Sulaiman ya tako zuwa gurin wani matashi kamar sa a cikin yansanda yana tambayar sa ko lafiya?
Ya kalli Sulaiman "Kai dan gidan ne? Kafin ya bashi amsa ya ji wanda Abban su ya tambaya yana cewa " Matar gidan zamu tafi da ita. Da sauri Sulaiman ya matsa kusa da su daidai lokacin da Abba yake cewa ina zaton dai kunyi kuskure ba matar gidan nan bace, domin babu wata matsala da zata saka har a dakko mata ku. Dansanda ya fusata bangane me kake nufi ba, kana son kace bamu San aikin mu ba? To tare da masu korafin muka zo suka nuna mana gidan suka wuce ka ga kuwa babu maganar kuskure. "
Ina suke masu korafi? Abba ya katse shi. Malam Dan Allah ka tafi abinka ko ka jira in anje can ka bi kaji komai. Sulaiman ya tsoma baki da cewa babu inda zaku tafi da ita domin dai babu wani laifi da Inna zata yi wa wani. Sai ka hana inji wani ɗan sandan dake gefen sa dan baki kerere lebensa ya farfashe saboda shan taba.
Ina takardar shedar kamun ta domin dai ku ba yansandan nan Unguwar bane. Abba ya furta yana Kallon babban su wanda ya ke kada kai cikin isa.

Malam a Najeriya fa muke inba manyan mutane ba waye ake zuwa kamashi da waranti? Matar nan sai taje tunda ta ci zarafin Hajiya kawai dan tazo akan maganar auren kaninta bayan yarinyar ma an kamata da wani!! Abba ya ja tsaki tare da fadin Koma menene dai sai naga takardar shedar kamunta sannan zaku kamata. Wanda baisan kanshi ba shine ake zuwa a diba kara zube,ko da muke a Najeriya ba kowa bane lalatacce wanda bai san doka ba.
Chapter 33 · 0% Book details