Sashe 34
Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sulaiman wanda ya gano daga inda maganar ta taso ya shiga kiran layin Halifa yau dai kam ko shiga bata yi, ba kamar kwanaki ba da tana shiga amma ya ki dauka, har Sulaiman ya fusata ya daina kira, Kenan ma ya yi Blocking dina Sulaiman ya raya a ransa
Takaici ya kama Sulaiman ya sa kai ya shiga gidan daidai da komawar matan yan sanda viki. . Suka ce mama munzo zamu tafi da ke office din mu. Sulaiman yace babu inda Inna zata je. Abba ya kira makotan su a waya ya sanar da su, wadanda ke kusa duk suka zo harda me Unguwar su. Take ya kira D. P. O na nan Unguwar ya tambaye shi cewa yarana ne suka zo kama matar marigayi makocin su. Take ya bincika ya Tabbatar cewa ba daga gurin su bane. Nan fa aka ce babu inda Inna zata dan ba su da hurumin kamata daga wata Unguwa ko daga sama ne sai an biyo ta kan yansanda Unguwa.
Mutane suka cika matasa suka soma hayaniya tsageru suka soma jifan yansanda wanda haka ya tilasta musu fesa tiyagas sannan suka dauki motar su suka tafi.
Inna wadda har ta saka hijabi tana cewa aje duk inda za a ta zauna tana kuka tana baiwa Babar su Sulaiman labarin abinda ya faru. Makota suka yi ta shigowa suna jajantawa Inna. Abban Su Sulaiman ya gama sauraron Inna yace ko sun dawo kar kije zalunci ne kawai irin na masu kudi, zan kira kawun shi wanda shine waliyinsa tunda abokina ne dan inji duk da sanin su ake ta wannan bada kalar, ke baki sanar dani me ake ciki ba, yanzu haka ma shi din bai san komai akai ba.
Inna tace " Ba mamaki in bai sani din ba, amma abin ya bi gari ana ta cecekuce jiya zuwa yaune abin ya lafa." Yace Allah ya kyauta. Tayi masa godiya suka yi sallama.
Anty ta zata Inna na kulle dan haka washe garin ma sai yamma sukaje ofishin yansanda sai dai wadanda suka samu jiya ba su ne yau a gurin ba, Hajiya Talatu tace ai ba matsala tunda dai mun san tana tsare bari mu nemi ganin D. P..O.
Bayan sun gaisa suka sanar masa cewa sune mutanen da suka yi rigima da wata mata ta kwana a nan. D. P. O yace bai San zan can ba, daga ina ne aka kawo ta? Suka ce daga Fagge Yace " Gaskiya bamu da hurumin yi muku case a nan kuje can Fagen ku yi case din a can. Daya sa aka bincika sai ya gano yan Unguwar sun hana a kamo matar. Yace to dama dai ba hurumin mu bane kuje Fagen.
Anty Wadda takaici ya hana magana har sai da suka zauna a Kekenapep ta ja tsaki ta ce Gaba daya kinsa na yi asarar dubu hamshin dina gashi babu wata nasara da aka samu shikenan matar nan ta ci galaba a kaina!
Hajiya Talatu cikin sigar wanke kanta daga zargin Anty tace "Ko kadan kar kiga laifina. Ke kika kaimu na Unguwar ku kuma ko yanzu din na can Unguwar ta su Fagen zamuje ai ba barin case din zamuyi ba." Bazanje ba"! Anty ta katse ta, " Kin ga Talatu na sako ki cikin sabgar nan ne dan ki sama mun mafita badan ki kara min damuwa da takaici ba. dan haka in baza ki iya ba, ina rokon ki da ki hada komatsanki ki koma garin ku. Hajiya Hajiya Talatu ta saka dariya tare da fadin Dadina da ke sahibata, idan kika fusata sai ki rasa abin fada, shiyasa ko me zakice baya damuna.
Anty ta ja tsaki Sannan tace sai ki fada min mafita dan wannan dai babu nasara. Hajiya Talatu tace mafita fa na fada miki kiyi duk abinda zaki yi amma ina son ki sani zakiyi komai ne kafin Halifa ya dawo domin ko yanzu bana tunanin zai ji dadin kiran yansanda da kika yi wa Inna. "
Anty tace Hakane yanzu dai menene mafita? Hajiya Talatu tace dole fa mu fara ta kan cikin a zubda shi sannan abubuwa su biyo baya.
Abban su Sulaiman ya kira Baffan Halifa a waya bayan sun gaisa sai yake tambayar Baffa da cewa Yaya anyi abu cikin mutunci da girmamawa yanzu kuma abu ya zo da cin zarafin Uwar yarinyar nan su Halifa za su kirawa yansanda. Baffa ya kasa gane kan zance kuma ya kasa hasko ma wace yarinya ake nufi. Sai da Abban su Sulaiman ya fayyace masa zance kamar dai yadda Inna ta sanar da shi. Baffa ya cika da mamaki yana shakku akan wai Aunty Halifa ce za ace duk ta kitsa wannan lamarin ko dai su binciki yarinyar nan yaran yanzu ka iya kulla abinda ba shi bane. Yace Kuma kuna da tabbaci akan abinda yarinyar nan ta fada? Saboda ni dai iya sanin na nayi wa Habiba mutuniyar kirki sbedar cewa ta na son Halifa kuma mu dangin Halifa na waje Uba, ta dauke mu kamar dangin ta, kuma ta bawa Halifa tarbiyya daidai gwargwado bana shakka akan haka. Sai dai kuma bari zan yi magana da Halifa idan ya dawo domin gaskiya baya nan ya yi tafiya, kuma dai ni bai sanar da ni komai ba. Abban su Sulaiman yace To Wallahi kamar yadda ka bada shedar matar nan haka zan baka shedar yarinyar nan da uwarta. Kusan sai ince maka kaf Unguwar nan tamu da kyar a samu mai hakuri da kirki Uwar yarinyar nan. Shi yasa muka hana yansanda su tafi da ita. amma ka bincika dai insha Allahu ai gaskiya zata yi halinta ko ba dade ko ba jima. Haka suka yi sallama kowa yana cike da yakinin shike da gaskiya.
Anty ta tura Adamu Bros gidan wata kawarta wadda suka yanke shawarar hada yaran bayan fahimtar da ta yi cewa Mijin kawar ta ta ya samu kudi harma ya tsaya takardar dan majalisar jiha. Da ta share Hajiya Mairo bata ko daga kiranta bayan mijina ya samu karayar arziki, sai gashi harda kai mata ziyara daga jin labarin abin Duniya ya kara dawo musu. A nan ne tace "Kai najima banzo ba haka Huda ta girma gaskiya baki kyauta ba ko ita ai da kin turo min ta dan yi min kwana biyu anyi hutu Hafsa fa tana nan kinga ai da sun saba. Ta fadi hakane bayan Huda tazo ta gaida ita.
Hajiya Mauro tace Kaji ki da kare kai keda kika watsar da mutane yaushe har zan turo miki ita? Anty tace hummm ni da zaku ba wannan yaron ita wallahi da nayi murna ga hankali masha Allah. Hajiya Mairo tace Da dai kafin ya yi aure ne gaskiya ba zata gidan Mijin wata ba. Adamu ai yaron kirki ne kawai dai bazan kai yarana gidan kishiya bane. Anty ta amshe da fadin "Wace kishiya kike ta fadine Adamu yanzu bashi da mata sun rabu, yarinyar da harni ta zazzaage a gaban sa nan take ya dan kara mata saki uku ya aunata gidan su." Hajiya Mairo tace Ko dai ke ce kika shiga shirgin su shiyasa har ta yi miki rashin kunya. "Haba Hajiya Mairo ashe baki ma san ni ba ko ince kin manta ni. Anty ta cafke maganar, taci gaba da fadin zan turo shi in har ya yi mata shikenan muyi tuwon mu manmu.
Sun shirya cewa yaje a ranar Lahadi Dan haka ta kira Bros ya zo har gida ta kwatanta masa gidan Hajiya Mairo tare da bashi Umarnin lallai ya shiyar a ranar Lahadi ya tafi su hadu da Huda.
Maman Nihal ce ta karfafa masa tare da tilasta masa cewar yaje din domin bashi da wata mafita dole ya yi biyayya ga mahaifiyarsa. Huda tana da kyau dukda ya kula tana da jin kanta sannan kuma ta aminta da shi. Ta gefensa dai kawai yace mata su yi tunani zuwa sati mai zuwa zai dawo in har sun ga ya dace su yi aure. Saidai kafin satin Huda ta fada da Bros ta matsa masa da kira da sako. A gurin Hajiya Mairo Anty ta ke samun labarin zuwa Bros da yadda Huda ta amince da shi.
Anty ta kira Adamu ta yi masa tatas sakamakon baizo ya sanar da ita yadda suka yi da Huda ba. Kuma tace lallai da kanshi take son ya kawo kudin da za akai yaba Dadin su hannu da hannu, wanda za a kai gidan su Huda tace kuma ya bada kudi masu kauri domin tuwo girma dai miyarsa nama
.
Kafin zagayowar satin da yace su yi tunani Anty ta tilasta aka kai kudin auren har aka saka rana wata biyu.
Halifa ji yake kamar karya dawo Nigeria domin ya samu nutsuwa zuciyar shi abu daya zai dawo danshi Asiya. Ya kasa samun ta balle labarin ta. Ya yanke shawarar yana dawowa zaije ya dakkota su koma sabon gidansu Koda Anty bata amince da hakan ba.
Asiya kuwa tana shirin dawowa domin soyayya da kewar mijita sun hana ta kwanciyar hankali. Saiga Inna cike da tashin hankali take sanar da su Abinda Anty ta yi mata. Sannan ta kara da fadin cewa tana zargin cewar Halifa ya san komai tunda har baizo ba ko hakuri ya bata. Asiya ta sha kuka dan takaici gaskiya Halifa ya sani domin tana da Tabbaci Sulaiman ya kira shi ya fada masa ya kamata ya zo ya wanke kansa a gurin Inna. Dan haka ta kudure a ranta cewa duk wanda ya taba mutuncin Innarta zata iya hakura da shi da soyayyarsa. Saidai wani sashe na zuciyata ya ki yarda da cewa Halifa yana da masaniya. Ta dai yanke shawarar ci gaba da zama a Malumfashi har sai ta haifi dan cikin ta.