← Book details Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 62

Sashe 37

Hasashe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asiya tace Inna gaskiya Na hakura da yin awon nan ina yawan mafarki da Asibiti wai kuma ga Anty abin dai na kasa fassara shi. Inna tace" Khairan insha Allah babu abinda zai samu ke da abinda ke cikin ki, Kiyi ta adduo'in neman tsarin nima kuma ina yi, kinsan dai Allah baya wofintar da adduo'in mahaifa akan yaransu. Insha Allah zaki sauka lafiya.

Sadiya da ke gefe tace Ameen insha Allah. Ni Mijin nata ne ma ko da dai ance ya yi tafiya amma ya kamata ko a waya ya nemeki in dai ba wai yana zargin ki a gaske ba. Asiya tace Babu mamaki ya neme ni ai nâ kashe wayata. Inna tace shi dai ya sani nikam gara ma ya baki takardar ki in kin haihu lafiya kya samu wani mijin daidai ke. "Asiya tabi Inna da ido tana Kallon ta domin kalaman Inna sun soki zuciyar ta har ma ta rasa kalmar fadi. Sadiya tace muna daya Inna gara su rabu da a kashe ta a banza, dan matar nan ta shirya wa haka. Suka ci gaba da tattauna zancan a tsakanin Inna da Sadiya. Asiya dai bakinta dai ya yi nauyi zuciyar ta kuwa ta shiga zogi gaskiya bata jin zata iya rayuwa ba tare da Halifa ba, gaskiya tana son shi zata iya jure komai saboda shi, sai yanzu ta yi data sanin dawowarta gida da ta tsaya kamar yadda ya bukata. Inna tana da sauki amma in ta cije bata canzuwa ga ciwon ta ba sa son abinda zai bata mata rai. Ta share zufar da ta keto mata ta kuma sauke ajiyar zuciya lokaci guda.
Inna ta kalleta lafiya ko dan ance bazaki koma gidansa ba? Asiya tace Ba haka bane kawai dai bari ya dawo muji ta bakinsa. Inna tace Ai ko ya dawo bazan iya gayyar rashin mutuncin ba abida kawai zaifi shine a rabu. Yansanda kamar anzo kama yan fashi banda Allah yasa muna zaune da yan Unguwa lafiya ba, ai da tuni sun tafi dani, Kasar nan ba a jin kunya a juya takarda a rubuta abinda ake so a kaiwa alkali ya jefa ka gidan Yari..Sadiya Tace nifa Har shi Halifa haushin sa nake ji, da ka yake zaune ace duk abubuwan da ta miki wai yace bai sani ba kuma bai fahimci komai akai ba?!! Asiya tace kar kice haka maman Annur kar ki ga laifin sa dan bai sani ba, Na farko baya yini a gidan sannan ya yarda da ita bata taba yi masa wata mugunta ba bare ya zarge ta. Kuma yadda naga yana shiga tashin hankali idan zuciyarsa ta hasaso ko ta zarge ta shine yasa ban fada masa komai ba. Kinga kuwa dole a yi masa uzri. Inna tace "Dama fa ba sanin su mukayi ba, dare daya yazo rabon dai wannan ciki. Ni mutum ko dan karuna ne ya zo dan kudi wallahi bazan dauki wulakanci ba. Asiya ta sunkuyar da kai. Lallai abin ya wuce yadda take tunani.

Halifa ya shiga ciki falon Anty Hafsi tana waya yace ina Anty? Tace tana ciki ba ta da lafiya. Yace Allah ya sau wake, ki ce mata nazo zan dauki kaya. Hafsi ta ce To ka shiga mana Uncle ita da Hajiyan Zariya ne. Yace Shiyasa bazan shiga ba domin bana son ganin matar nan a gidan nan duk lokacin da ta zo abubuwa sai sun yi ta faruwa babu dadi.

Hafsi ta taba baki "Ai kwadayi ke kawo ta dan ma Anty tana taka mata burki. Ya ja tsaki Sannan ya bi bayan Hafsi.
Anty tana kwance ta rufa cikin bargo tana ta rawar sanyi Hajiya Talatu tana yi mata sannu. Ya kalli sashin akwatuna suna jere kamar yadda suke hatta rinbom din dake jikin akwatunan suna jiki. Ya dan taba baki shikam ya tabbatar wadannan din dai ya gani dazu. Ya dan matsa kusa da Anty yace Sannu Anty zazzabi ne. Hajiya Talatu ta ce Hawan jinin ta ne ya tashi ta samu kanta a bacin rai gidan su wannan matar taka da muka je neman sasanci Uwar ta ta zage mu tas ta zuba mana ruwan wanki har ta yi ikirarin kisan Antyn ka. "Shine dalilin kira mata ya sanda da kukayi? Halifa ya katse Hajiya Talatu. Tace Eh to ai dole dannan kaji yadda ta tara mutane tana shan alwashin kashe Antyn ka kuwa!!? Cike da tsana Halifa ya sake Kallon ta." Nasan ke zaki zuga ta kuje gidan ku yi mata rashin mutuncin kuma ko me ya faru dai ku kuka sameta har gidan ta. Anty wadda ke kwance tana makyarkyata ta tashi da sauri zaune cike da mamaki tana Kallon Halifa cike da Al ajabi yaron da in bata da lafiya ya fi kowa daga hankali yaron da in wani ya tabota sai inda karfin sa ya kare idan da ne ya samu bata da lafiya ba zai bari ta kara minti goma a gidan ba, zai tabbatar tana gadon Asibiti.

Ta soma magana cikin kuka Halifa ni ka ke fadawa magana akan surukan ka shine har kake wadannan zantuka ko? Halifa Ya ce. "Menene karya ko laifi a magana ta Anty? Nace kuje neman sasanci ne da wa muka yi fada ni da mata ta ba fada muka yi ba, anyi mata sharri ne kuma ta yi fushi in kuma ta huce zata dawo to menene naku da zuwa gidan?Wallahi Anty kin bani mamaki kuma kin nuna min cewa lallai mahaifiyata ta mutu domin da tana raye wallahi baza ta dakkowa surukai na mutane muskunai masu rauni kamar su Inna yansanda ba. Kamar yadda ke ma nasan bazaki dakkowa iyayen matar Bros ba tunda danki ne.

Yanzu kam Anty kukan gaske take rerawa ba kamar dazu ba da take kukan kissa da makirci ba. Hajiya Talatu wadda ta hangame baki ta kasa magana har sai da ya kai aya ta sauke ajiyar zuciya tace Amma dai dannan baka kyauta ba, Antyn ka bata cancanci irin wadannan kalamai daga bakin ka ba domin..... Ke da Allah yimin shiru ina wuya dake wallahi in kika kara magana sai nasa an rufe min ke, kuma ki tashi ki fita ki bar gidan nan yanzun.!! Anty mai rashin lafiya ta diro daga kan gado Tazo gaban Halifa ta sa hannu ta dauke shi da wani wawan mari, Ka fara shaye shaye ne a tafiyar da ka yi ko? Ta daga murya ni zaka ciwa zarafi wannan ne sakamako na ko Halifa!! Ta fashe da sabon kuka mai karfi wanda ya janyo hankali kowa na gidan inda suka nufo dakin. Halifa ya dafe kuncin sa ya cike da bacin rai a kofar fita suka ci karo da Dady zai shiga falon. Ganin yadda Halifa ya wuce ba tare da ya Kalle shi ba bare ya yi masa magana ba ya gane akwai matsala dan haka ya nufi ciki da sauri, kukan Anty da zantuka da take maimaitawa ne suka dira a kunnen shi. Tana fadin ni Halifa zai ciwa zarafi akan surukansa wallahi daga shi har su basu isa ba inna haihu cikin iyayena ko asiri suka yi masa sai na karya shi.

Bai shiga dakin ba ya wuce nashi dakin sai da ya cire kayan jikinsa ya saka jallabiyya sannan ya fito ya nufi dakin Halifa dan jin ba"asi.
Yana fitowa tsakar gida Halifa ya fita a motarsa da gudu daga gidan ya danyi shiru yana tunanin abinda zai yi, yana tsoron masifar Anty ne shiyasa bai ma shiga dakin ta ba. Ya yi ta maza ya tunkari dakin danjin meke faruwa.

Ya kalli yaran da suka tasa su gaba suna kallo yace kai duk ku fice. Ya dubi Anty wadda ke ta kuka tana sharbe sam bataji dadin abinda Halifa ya fada mata ba har zuciyar ta. Hajiya Talatu tana fadin daga gani zugashi suka yi. Dady yace Wai me yake faruwa ne? Sabon kuka Anty ta dora tana rattafo mishi abinda Halifa ya fada mata. Dady yace Gaskiya fa ya fada miki kuma ya kamata ki zauna ki yi wa kanki tunani sosai domin kina shiga hurumin yaran nan, menene naki na kirawo musu yansanda kuma?
"Dan Allah ka rufe min baki!! Anty ta katse shi, ai kai dama kullum nice mai lefi akan komai. To Bari kaji Halifa dai dan Uwa na ne in ka so kayi masa fada ya bini ko kuma ka sa mana ido. Cikin mamaki taji ya daka mata tsawa." Ke Habiba saurara kiji, na gaji da abinda ki ke yi a gidan nan ina kauda kai. Ina yi ne fa dan a zauna lafiya ba wai dan tsoron ki ko wani abu ba, ina son ki sani bazan iya ci gaba da wadannan munanan dabi un naki ba, dan haka ina son ki sani komai zai iya faruwa ya sa kai ya fice daga dakin. Sai lokacin ta samu damar magana ta kalli Talatu Ki dubi wannan mutumin fa, har yana da izzar yi min magana kenan? Ta mike rai bace ta nufi kofar dakin shi tace ka fito ka fada min abinda zai faru karkari dai ka ce ka sake ni ko? Kaga sai ka hada yan kayan ka ka yi gaba banda haka me zai faru!! A doke dai ba zan doku ba haka ma zage bazan zagu ba.. Ya fito da karamar waya a hannunsa yana sauraron labarai ya kalleta ya ja tsaki ya wuce..

Anty fa abin ya zame mata goma da I shirin tana mamakin Inda mijinta ya samo kwarin gwiwa. Hajiya Talatu ta ce, Alamu suna nuna ayyuka duk sun karye wadan da kika yi masa, dan haka gobe akwai sammakon gidan malamai sai kuma kin kwance bakin aljihu. Anty tace Kai Na shiga uku yanzu me yafi mahimmanci a guri na aikin Halifa ko na Asiya ko na Dady......
Chapter 37 · 0% Book details